Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 11/1 pp. 4-7
  • ‘Ku Yafa Zuciya ta Tawali’u’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ku Yafa Zuciya ta Tawali’u’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mahalicci Maɗaukaki Mai Tawali’u Ne?
  • Abin da Tawali’u ba ya Nufi
  • Alamar Ƙarfi
  • Amfanin Tawali’u
  • Ka Koyi Tawali’u Na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Jehovah Ya Bayyana Ɗaukakarsa Ga Masu Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Yesu Ya Kafa Misali Na Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 11/1 pp. 4-7

‘Ku Yafa Zuciya ta Tawali’u’

MUTUMIN ya fito ne daga wani sanannen birni. Yana jin daɗin matsayinsa na ɗan ƙasar Roma kuma wataƙila ya fito ne daga wata iyali mai arziki. Wannan mutumin mai suna Shawulu, ya sami ilimi mai kyau a ƙarni na farko A.Z., Ya iya yare aƙalla guda biyu, kuma yana ɗaya daga cikin wani sanannen rukunin addinin Yahudawa, wato, Farisawa.

Shawulu yana raina talakawa kuma yana fahariya saboda yana ganin cewa shi adali ne. (Luka 18:11, 12; Ayukan Manzanni 26:5) Farisawa ’yan’uwan Shawulu suna ganin cewa sun fi wasu, suna son a girmama su kuma suna son manyan suna. (Matta 23:6, 7; Luka 11:43) Wataƙila yin tarayya da irin waɗannan mutanen ne ya sa Shawulu ya zama mai fahariya. Mun san cewa shi mai hamayya da Kiristoci ne sosai a dā. Daga baya, sa’ad da ya zama manzo Bulus, ya ce wai shi “mai-saɓo ne dā, mai-tsanani, mai-ɓatanci.”—1 Timothawus 1:13.

Hakika, sa’ad da Shawulu ya zama Kirista, wato manzo Bulus, halayensa sun canja gaba ɗaya. Da yake shi Kirista ne kuma manzo, ya nuna tawali’u sa’ad da ya ce shi “mafi ƙanƙantar tsarkaka duka” ne. (Afisawa 3:8; LMT) Shi mai wa’azi ne sosai, amma bai yaba wa kansa ba. Maimakon haka, ya yaba wa Allah. (1 Korinthiyawa 3:5-9; 2 Korinthiyawa 11:7) Bulus ne ya shawarci ’yan’uwansa Kiristoci: ‘Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa.’—Kolossiyawa 3:12.

Irin wannan shawarar ta shafi wannan zamaninmu kuwa? Kasancewa da tawali’u yana da amfani kuwa? Da gaske ne tawali’u alama ce mai nuna ƙarfi?

Mahalicci Maɗaukaki Mai Tawali’u Ne?

Ya kamata a yi la’akari da ra’ayin Allah idan ana tattaunawa game da tawali’u. Me ya sa? Domin shi ne Mamallaki kuma Mahaliccinmu. Da yake ya fi mu, ya kamata mu sani kuma mu amince da kasawarmu. Mun dogara da shi ne. “Ubangiji! ya fi ƙarfinmu mu gane shi; mafifici ne shi cikin iko,” in ji Elihu wani mutum mai hikima a zamanin dā. (Ayuba 37:23) Hakika, idan muka duba girman duniyarmu ya kamata hakan ya sa mu kasance da tawali’u! Annabi Ishaya ya ce: “Ku tada idanunku sama, ku duba ko wanene ya halicci waɗannan, wanda ya kawo rundunarsu bisa ga lissafinsu: yana kiransu duka da sunansu; bisa ga girman ikonsa, domin shi mai-ƙarfi ne cikin iko, ba wanda ba shi ko ɗaya.”—Ishaya 40:26.

Ban da cewa shi maɗaukaki ne, Jehobah Allah yana da tawali’u. Sarki Dauda ya yi addu’a ga Allah: “Ka kuma ba ni garkuwar cetonka: Nasiharka kuma ta maishe ni mai-girma.” (2 Samuila 22:36) Za a iya cewa Allah mai tawali’u ne saboda yana kula da talakawa waɗanda suke ƙoƙarin su bauta masa, kuma yana nuna masu jin ƙai. Daga sama Jehobah ya ƙasƙantar da kansa a alamance, domin ya kula da masu tsoronsa.—Zabura 113:5-7.

Bugu da ƙari, Jehobah yana ƙaunar bayinsa masu tawali’u. Manzo Bitrus ya rubuta: “Allah yana tsayayya da masu-girman kai, amma yana bada alheri ga masu-tawali’u.” (1 Bitrus 5:5) Game da yadda Allah yake ɗaukan masu fahariya, wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji yana ƙin kowane mai fahariya.” (Karin Magana 16:5; LMT) Ta yaya ne tawali’u zai kasance alamar ƙarfi?

Abin da Tawali’u ba ya Nufi

Tawali’u ya bambanta da ƙasƙantarwa. A wasu al’adu na dā, mutumin da ke da tawali’u bawa ne, almajiri, mai baƙin ciki kuma abin tausayi. Akasarin haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tawali’u yakan jawo girmamawa. Alal misali, wani mai hikima ya rubuta: “Ladar tawali’u da tsoron Ubangiji Dukiya ne, da girma, da rai.” (Misalai 22:4) Kuma Zabura 138:6 ta ce: “Ubangiji maɗaukaki ne, ya kan lura da masu tawali’u: Amma masu-girman kai daga nesa ya fishe su.”

Idan mutum yana da tawali’u hakan ba ya nufin bai iya kome ba ko kuma bai taɓa cim ma wani abu ba. Alal misali, Yesu Kristi bai taɓa da’awar cewa shi ba makaɗaicin Ɗan Jehobah ba ne, kuma bai taɓa nuna cewa hidimarsa a duniya ba ta da ma’ana ba. (Markus 14:61, 62; Yohanna 6:51) Duk da haka, Yesu ya nuna tawali’u ta wajen yaba wa Ubansa domin ayyukan da ya yi kuma ya yi amfani da ikonsa wajen taimaka wa mutane maimakon ya nuna musu iko da kuma zalunci.

Alamar Ƙarfi

Abokanan Yesu Kristi sun san shi ta wurin ayyuka masu ‘iko’ da ya yi. (Ayukan Manzanni 2:22) Hakika, ga waɗansu shi ‘ƙasƙantacce’ ne. (Daniel 4:17) Ya zama mai filako kuma ya koya wa mutane muhimmancin tawali’u. (Luka 9:48; Yohanna 13:2-16) Amma, tawali’un da yake da shi bai mai da shi wawa ba. Ya kasance da gaba gaɗi sa’ad da yake kāre sunan Ubansa da kuma lokacin da yake hidimarsa. (Filibbiyawa 2:6-8) A cikin Littafi Mai Tsarki, an kwatanta Yesu da zaki mai gaba gaɗi. (Ru’ya ta Yohanna 5:5) Misalin Yesu ya nuna cewa tawali’u ya jitu da ɗabi’a mai kyau.

Yayin da muke ƙoƙari mu kasance da tawali’u na gaske, mun fahimci cewa hakan ba ƙaramin aiki ba ne. Ya ƙunshi yin biyayya ga nufin Allah a kowane lokaci maimakon bin hanya mai sauƙi ko kuwa sha’awa ta jiki. Kasancewa da tawali’u yana bukatar ɗabi’a mai kyau, saboda haka, ya kamata mu sa bautar Jehobah da ƙaunar waɗansu su zama na farko maimakon abubuwan da muke so.

Amfanin Tawali’u

Tawali’u yana nufin ƙin fahariya ko kuma ɗaukaka kai. Za mu iya kasancewa da tawali’u da zai ja-goranci tunaninmu idan muka bincika kanmu, wato, ƙarfinmu, kasawarmu da kuma nasarorin da muka yi. Bulus ya ba da shawara mai kyau game da wannan sa’ad da ya ce: “Ni ke fāɗa ma kowane mutum wanda ke cikinku, kada shi aza kansa gaba da inda ya kamata; amma shi tuna yadda za shi aza da hankali.” (Romawa 12:3) Dukan waɗanda suka bi wannan shawarar suna nuna tawali’u.

Za mu nuna mu masu tawali’u ne idan muka sa bukatun wasu gaba da namu. An huri Bulus ya gargaɗi Kiristoci: ‘Kada ku yi kome domin tsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u ku maida wasu sun fi ku.’ (Filibbiyawa 2:3) Wannan ya jitu da umurnin da Yesu ya ba mabiyansa: “Wanda shi ke mafi girma a cikinku shi zama mai-hidimanku. Kuma dukan wanda za ya ɗaukaka kansa za ya ƙasƙanta; dukan wanda ya ƙasƙantadda kansa kuwa za ya ɗaukaka.”—Matta 23:11, 12.

Hakika, Allah yana ɗaukaka waɗanda suke da tawali’u. Almajiri Yaƙub ya nanata hakan sa’ad da ya rubuta: “Ku ƙasƙanta a gaban Ubangiji, shi kuwa za ya ɗaukaka ku.” (Yaƙub 4:10) Waye ne ba zai so Allah ya ɗaukaka shi ba?

Rashin tawali’u ya jawo rikici da kuma jayayya tsakanin mutane. A wani ɓangare kuma, tawali’u yana kawo albarka. Za mu sami amincewar Allah. (Mikah 6:8) Za mu sami kwanciyar rai saboda wanda yake da tawali’u zai sami farin ciki da gamsuwa fiye da wanda yake da girman kai. (Zabura 101:5) Dangantakarmu da iyalanmu, abokai, abokan aiki da kuma sauran mutane za ta yi kyau. Masu tawali’u suna guje wa tashin hankali da kuma nace wa halayen da za su iya ɓata wa wani rai, lalata dangantaka, baƙin ciki da kuma fushi.—Yaƙub 3:14-16.

Hakika, kasancewa da tawali’u kyakkyawar hanya ce na riƙe dangantaka mai kyau da mutane. Zai iya taimakonmu mu jimre ƙalubalen da ake fuskanta a wannan duniyar. Da taimakon Allah, manzo Bulus ya sha kan girman kai da yake da shi a dā. Hakazalika, mu yi ƙoƙari mu cire duk abin da zai sa mu girman kai ko kuma tunanin cewa mun fi wasu. Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “A bayan girman kai sai halaka, faɗuwa kuma tana biye da tada hanci.” (Misalai 16:18) Idan muka bi misalin Bulus da kuma shawararsa, za mu fahimci amfanin ‘yafa zuciya ta tawali’u.’—Kolossiyawa 3:12.

[Hoto a shafi na 4]

Bulus ya sha kan girman kai

[Hoto a shafi na 7]

Kasancewa da tawali’u zai taimake mu mu riƙe dangantaka mai kyau da mutane

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 5]

Anglo-Australian Observatory/David Malin Images

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba