Ka Saurari Lamirinka
“Al’ummai, waɗanda ba su da shari’a [na Allah], kadan bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a.”—ROMAWA 2:14.
1, 2. (a) Ta yaya mutane da yawa suka aikata domin sun tausaya wa wasu? (b) Waɗanne misalai na Nassi ne suka kwatanta son taimaka wa wasu?
CIWON farfaɗiya ta kama wani matashi mai shekara 20 da ke tsaye a gefen hanyar jirgin ƙasa kuma ya faɗa kan hanyar jirgin. Da ganin haka, wani mutum da ke wurin ya saki hannu ’ya’yansa mata biyu kuma ya yi tsalle ya faɗa inda matashin yake kwance. Ya ja matashin cikin ramin da ke tsakanin hanyar jirgin, ya kwanta a kansa don ya kāre shi daga jirgin da ya taka birki kuma ya tsaya a gabansu. Wasu za su iya cewa mutumin jarumi ne, amma ya ce: “Ya kamata mutum ya yi abin da ya dace. Na yi hakan ne don na ji tausayin matashin, ba don na yi suna ba ne ko don a yabe ni.”
2 Mai yiwuwa ka san wani da ya yi kasada don ya taimaki wasu. Mutane da yawa sun ɓoye baƙin da ba ’yan ƙasarsu ba ne a lokacin Yaƙin Duniya ta biyu. Ka tuna da abin da ya faru da manzo Bulus da mutane 275 da jirginsu ya ragargaje a garin Malita, kusa da Sicily. Mutanen garin suka fito suka taimaki waɗannan baƙin, kuma suka nuna musu “alheri irin da ba a kan saba yi ba.” (Ayukan Manzanni 27:27–28:2) Muna da misalin yarinya Baisra’ila wadda ko da yake ba ta kasadar da ranta ba, ta tausaya wa ɗaya cikin ’yan Suriya da suka kama ta. (2 Sarakuna 5:1-4) Ka tuna sanannen almarar Yesu na Basamariye mai halin karɓan maƙwabta. Wani firist da Balawi sun ƙyale ɗan’uwansu Bayahudi da aka yi wa mugun duka, aka bar shi rai ga Allah, duk da haka wani Basamariye ya taimake shi sosai. Har yanzu wannan almarar tana motsa zuciyar mutane daga al’adu da yawa.—Luka 10:29-37.
3, 4. Da yake mutane da yawa suna rashin son kai duk da kasadar da suke yi, menene wannan yake nuna mana game da koyarwar rai na bayyanau?
3 Hakika, muna zama “cikin kwanaki na ƙarshe,” domin mutane da yawa “masu-zafin hali” ne kuma “marasa-son nagarta.” (2 Timothawus 3:1-3) Duk da haka, mun ga inda aka nuna ayyukan alheri, wataƙila mun amfana daga irin waɗannan ayyukan. Mutane da yawa suna da halin son taimakon wasu, har su sadaukar da kansu, shi ya sa wasu suka kira hakan “halin jin tausayi.”
4 Ana ganin irin wannan son taimaka wa mutane a dukan ƙabilu da al’adu, kuma hakan ya ƙaryata ƙa’idar nan cewa mutane sun fito ne daga dabobbi.” Francis S. Collins, mai ilimin kwayoyin hali wanda ya ja-goranci gwamnatin Amirka a ƙoƙarinta na sanin adadin kwayoyin halitta a jikin mutum, ya ce: “Rashin son kai ya zama matsala ga masu rai na bayyanau. . . . Ko da yake ƙwayoyin halitta sun ci gaba da rayuwa, ba za a iya ba da bayanin rashin son kai ba. Ya kuma faɗi cewa: “Wasu mutane suna taimakon waɗanda ba su fito daga wuri ɗaya ba [wato iyali ɗaya, ƙabila ɗaya, al’ada, da addini ɗaya] da kuma waɗanda ba abin da ya haɗa su. Koyarwar Darwin ba za ta iya ba da bayanin wannan ba.”
“Lamiri”
5. Menene ake yawan gani a mutane?
5 Dokta Collins ya nuna fanni guda na rashin son kai: “Lamiri yana gaya mana mu taimaki wasu ko da ba za su iya biyan mu ba.”a Da yake ya ambata “lamiri,” yana iya tuna mana abin da manzo Bulus ya nanata: “Al’ummai, waɗanda ba su da shari’a, kadan bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a, waɗannan, domin ba su da shari’a sun zama shari’a ga kansu; da shi ke suna bayana aikin shari’a a rubuce cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaida tare, tunaninsu kuma yasu yasu suna kai ƙara ko kuwa suna kawo hujja.”—Romawa 2:14, 15.
6. Me ya sa dukan mutane za su ba da lissafi ga Mahaliccinsu?
6 A cikin wasiƙar da ya rubuta wa Romawa, Bulus ya nuna cewa ’yan adam za su ba da lissafi ga Allah domin ana ganin wanzuwarsa da halayensa a abubuwan da ya halitta. Wannan ya kasance haka “tun halittar duniya.” (Romawa 1:18-20; Zabura 19:1-4) Hakika, mutane da yawa sun yi banza da Mahaliccinsu kuma suna biɗan salon rayuwa na lalata. Duk da haka, nufin Allah shi ne ’yan adam su amince da adalcinsa kuma su tuba daga mugun ayyukansu. (Romawa 1:22–2:6) Yahudawa suna da ƙaƙƙarfan dalili na yin hakan, domin an ba su Dokar Allah ta wurin Musa. Amma, ya kamata har mutane da ba su da “zantuttukan Allah” su fahimci cewa Allah yana wanzuwa.—Romawa 2:8-13; 3:2.
7, 8. Menene ya nuna cewa mutane da yawa sun san abin da ya kamata, kuma menene ya tabbatar da hakan?
7 Ƙaƙƙarfan dalilin da ya sa ya kamata dukanmu mu amince da Allah kuma mu aikata yadda ya dace shi ne azancin sanin nagarta da mugunta. Da yake mun san abin da ya kamata, hakan ya nuna cewa muna da lamiri. Ka yi tunanin wannan: Wasu yara ƙanana suna jira a layi su yi lilo. Sai wani yaro ya zo ya sha gabansu, bai damu da waɗanda suke jira ba. Sauran suka ce, ‘Hakan ba shi da kyau!’ Ka tambayi kanka, ‘Me ya sa har yara da yawa a take sun nuna sun san abin da bai dace ba? Da yake sun yi haka ya nuna cewa sun san abin da bai dace ba. Bulus ya rubuta: “[Duk lokacin da] Al’ummai, waɗanda ba su da shari’a, kadan bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a.” Bai ce ba “Idan,” kamar abin da ƙyar ne yake faruwa. Da yake ya ce “duk lokacin da,” ko kuma “sa’ad da,” yana nuna cewa abin da yake faruwa ne a kai a kai. Saboda haka, furcin nan cewa mutane “bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a” yana nufin cewa azancin sanin abin da ya kamata ya motsa su su aikata cikin jituwa da abin da muka karanta a cikin rubutacciyar dokar Allah.
8 Ana ganin wannan halin a cikin ƙasashe da yawa. Wani farfesar jami’ar Cambridge ya rubuta cewa mizanan ’yan Babila, Masarawa, da Helenawa da kuma mutanen dā da suke zama a Australiya da kuma ’Yan Amirka na dā sun ƙunshi “ƙin zalunci, kisan kai, cin amana da yin ƙarya, yin alheri ga tsofaffi, matasa, da kuma raunannu.” Dokta Collins ya rubuta: “Mutane a dukan duniya sun san game da ra’ayin nagarta da mugunta.” Hakan bai tuna maka abin da ke rubuce a Romawa 2:14 ba?
Ta Yaya Lamirinka Yake Aiki?
9. Menene lamiri, ta yaya zai taimake ka kafin ka yi wani abu?
9 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa lamiri ne yake lura da ayyukanka kuma ya auna su. Kamar dai wata murya a cikinka tana gaya maka ko matakin da kake son ka ɗauka ya yi daidai ko bai yi ba. Bulus ya ambata wannan muryar da ke cikinsa: “Lamirina yana shaida tare da ni cikin Ruhu Mai-tsarki.” (Romawa 9:1) Alal misali, wannan muryar tana iya gaya maka tun da wuri kafin ka ɗauki mataki da ya ƙunshi yin abin da ke nagari da mugunta. Lamirinka zai iya taimaka maka ka yi tunanin abin da kake son ka yi a nan gaba kuma ya nuna maka yadda za ka ji idan ka yi abin.
10. Ta yaya sau da yawa lamiri yake aiki?
10 Sau da yawa lamirinka yana aikatawa bayan ka yi wani abu. Sa’ad da yake gudun hijira daga Sarki Saul, Dauda ya yi wa sarkin da Allah ya naɗa rashin hankali. Bayan haka, “zuciyar Dauda ta buga shi.” (1 Samuila 24:1-5; Zabura 32:3, 5) Ba a yi amfani da kalmar nan “lamiri” a wannan labarin ba, amma lamirin Dauda ne ya dame shi. Mu ma akwai lokacin da lamirinmu ya taɓa damunmu. Mun yi wani abu, kuma muka damu game da yadda muka aikata. Lamirin wasu mutane da ba su biya kuɗin harajinsu ba ya dame su kuma daga baya suka biya bashinsu. Wasu sun yi ikirarin zunubin zina da suka yi ga abokin aurensu. (Ibraniyawa 13:4) Duk da haka, sa’ad da mutum ya aikata daidai da lamirinsa, zai samu gamsuwa da kwanciyar hankali.
11. Me ya sa zai kasance da lahani ka ‘bar lamirinka ya yi maka ja-gora’? Ka ba da misali.
11 Za mu iya ‘barin lamirinmu kawai ya yi mana ja-gora’? Yana da kyau mu saurari lamirinmu, amma yana iya yaudarar mu sosai. Hakika, “mutumi namu na ciki” na iya ruɗinmu. (2 Korinthiyawa 4:16) Ga misali. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da Istifanas mai bin Kristi sosai wanda yake “cike da alheri da iko.” Wasu Yahudawa sun fitar da Istifanas bayan birnin Urushalima kuma suka yi ta jifansa da dutse har ya mutu. Shawulu (wanda daga baya ya zama manzo Bulus) ya tsaya kusa kuma ya “yarda da kisan” Istifanas. Kamar dai waɗannan Yahudawan sun tabbata cewa sun aikata yadda ya kamata kuma hakan bai dami lamirinsu ba. Haka yake da Shawulu, domin bayan haka “yana kan yin numfashi da kashedi da kisa tukuna bisa masu-bin Ubangiji.” Hakika, a lokacin lamirinsa bai gaya masa cewa abin da ya yi ba daidai ba ne.—Ayukan Manzanni 6:8; 7:57–8:1; 9:1.
12. A wace hanya ɗaya ce za a iya shafan lamirinmu?
12 Menene mai yiwuwa ya shafi lamirin Shawulu? Dalili ɗaya na iya zama tarayya na kud da kud da wasu mutane. Yawancinmu mun yi magana ta waya da mutum da muryarsa ta yi kama da ta babansa. Mai yiwuwa ɗan ya gaji muryar, amma wataƙila ya kwaikwayi yadda babansa yake magana ne. Hakanan ma, yin tarayya na kud da kud da Yahudawan da suka tsane Yesu kuma suke hamayya da koyarwarsa ya shafi Shawulu. (Yohanna 11:47-50; 18:14; Ayukan Manzanni 5:27, 28, 33) Hakika, wataƙila abokan Shawulu ne suka shafi lamirinsa.
13. Ta yaya inda mutum yake da zama zai iya shafan lamirinsa?
13 Al’ada ko kuma inda mutum yake da zama za su iya shafan lamirinsa, kamar yadda inda mutum yake da zama zai iya sa shi ya yi magana yadda mutanen wurin suke yi. (Matta 26:73) Abin da ya faru da mutanen Assuriya na dā ke nan. An san su da mugunta kuma sassaƙarsu ya nuna cewa suna azabtar da ’yan bauta. (Nahum 2:11, 12; 3:1) An kwatanta mutanen Nineveh na zamanin Yunana cewa ba su “iya rarrabe hannun damansu da hagu ba.” Wato, ba su da mizani mai kyau na sanin abin da ya dace da abin da bai dace ba a ra’ayin Allah. Lallai wannan yanayin zai iya shafan lamirin wanda ya yi girma a Nineveh! (Yunana 3:4, 5; 4:11) Hakanan ma a yau, halin waɗanda suke kusa da shi zai iya shafan lamirin mutum.
Yadda Za Mu Kyautata Lamirinmu
14. Ta yaya lamirinmu yake nuna abin da Farawa 1:27 ta ce?
14 Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u kyautar lamiri, kuma mun gaji lamirinmu daga wajensu. Farawa 1:27 ta gaya mana cewa an halicce ’yan adam cikin surar Allah. Wannan ba ya nufin siffar Allah na zahiri, domin shi ruhu ne amma mu kuma mutane ne masu tsoka . An halicce mu cikin surar Allah domin muna da halayensa, mun san abin da ya kamata kuma ta hakan lamirinmu yana aiki. Wannan ya nuna hanya ɗaya da za mu ƙarfafa lamirinmu, mu sa ya zama tabbatacce. Wato, mu ƙara koya game da Mahaliccin, kuma mu kusance shi.
15. A wace hanya ɗaya ce za mu amfana ta wajen sanin Ubanmu?
15 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ne ya ba mu rai, da haka yana kama da Uba ga dukanmu. (Ishaya 64:8) Kiristocin da suke da begen zuwa sama ko kuma zama a aljanna a duniya, suna iya kiran Allah Uba. (Matta 6:9) Ya kamata mu yi sha’awar kusantar Ubanmu kuma mu koyi ra’ayinsa da mizanansa. (Yaƙub 4:8) Mutane da yawa ba sa son yin hakan. Sun yi kama da Yahudawan da Yesu ya gaya wa cewa: “Ba ku taɓa jin muryatasa ba daɗai, ba ku taɓa ganin kamatasa kuma. Ba ku da maganatasa cinikinku zaune ba.” (Yohanna 5:37, 38) Ba mu taɓa jin ainihin muryar Allah ba, duk da haka za mu san yadda yake tunani ta wajen karanta kalmarsa kuma mu zama kamarsa kuma mu ji yadda yake ji.
16. Labarin Yusufu ya kwatanta menene game da koyarwa da kuma bin abin da lamirinmu ya ce?
16 Labarin Yusufu a gidan Fotifa ya nuna hakan. Matar Fotifa ta yi ƙoƙari ta rinjayi Yusufu. Ko da yake ya yi rayuwa lokacin da ba a rubuta wani littafi na Littafi Mai Tsarki ba kuma ba a ba da Dokoki Goma ba, Yusufu ya aikata ta wajen cewa: “Ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah kuma?” (Farawa 39:9) Iyalinsa suna zama da nisa, saboda haka bai yi hakan ba don ya faranta musu rai. Yana son ya faranta wa Allah rai. Yusufu ya san mizanan Allah game da aure, cewa namiji zai auri mace guda, su biyu su zama “nama ɗaya.” Wataƙila ya ji labarin yadda Abimelech ya ji sa’ad da ya san cewa Rifkatu tana da aure, wato, ba zai yi kyau ba idan ya aure ta kuma hakan zai jawo wa mutanensa alhaki. Hakika, Jehobah ya albarkaci sakamakon wannan batun, kuma hakan ya nuna ra’ayinsa game da zina. Da yake Yusufu ya san dukan waɗannan labaran, wannan ya ƙarfafa lamirinsa kuma ya sa ya ƙi lalata.—Farawa 2:24; 12:17-19; 20:1-18; 26:7-14.
17. Idan ya zo ga batun zama kamar Ubanmu, me ya sa yanayinmu ya fi na Yusufu kyau?
17 Hakika, yanayinmu yanzu ya fi kyau. Muna da dukan Littafi Mai Tsarki inda muke koya game da ra’ayin Ubanmu da yadda yake ji, har da abin da ya amince da shi da abin da ya hana. Idan mun ƙara sanin Nassosi da kyau, za mu matsa kusa da Allah kuma mu zama kamarsa. Yayin da muka yi hakan, lamirinmu zai aikata cikin jituwa da tunanin Ubanmu. A alamance, zai daɗa jituwa da nufinsa.—Afisawa 5:1-5.
18. Duk da yadda rayuwarmu ta dā ta shafe mu, menene za mu yi don mu kyautata tabbacin lamirinmu?
18 Ta yaya za a ce inda muke da zama zai shafi lamirinmu? Mai yiwuwa ra’ayi da ayyukan danginmu da kuma inda muka yi girma ya shafe mu. Da haka, wataƙila lamirinmu ya zama matacce ko kuma gurɓatacce. Yana magana da ‘harshen’ mutane da ke kusa da mu. Hakika, ba za mu iya canja rayuwarmu ta dā ba, amma muna iya ƙuduri aniya mu zaɓi abokane da wurin zama da za su shafi lamirinmu a hanya mai kyau. Mataki mai muhimmanci shi ne mu riƙa kasancewa koyaushe da Kiristoci waɗanda da daɗewa sun yi ƙoƙari su zama kamar Ubansu. Taron ikilisiya, har da yin cuɗanya kafin taro da kuma bayan taro zai ba mu zarafi mafi kyau na yin hakan. Muna iya lura da ra’ayi da ke bisa Littafi Mai Tsarki na ’yan’uwa masu bi da yadda suke aikatawa, har da yadda suke a shirye su saurari yadda lamirinsu yake gaya musu ra’ayin Allah da hanyoyinsa. Daga baya, wannan zai taimake mu mu daidaita lamirinmu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, kuma mu nuna halayen Allah sosai. Sa’ad da muka daidaita lamirinmu da ƙa’idodin Ubanmu kuma muka bi tasiri mai kyau na Kiristoci masu bi, za mu fi tabbata da lamirinmu kuma za mu fi so mu saurari abin da ya ce.—Ishaya 30:21.
19. Waɗanne fannoni na lamiri ya kamata mu mai da wa hankali?
19 Har ila, wasu suna fama su bi abin da lamirinsu ya ce a kowace rana. Talifi na gaba zai tattauna wasu yanayi da Kiristoci suka fuskanta. Ta wurin bincika irin wannan yanayin, za mu ga aikin lamiri sarai, da abin da ya sa lamirin mutane ya bambanta, da kuma yadda za mu ƙara saurarar abin da ya ce.—Ibraniyawa 6:11, 12.
[Hasiya]
a Hakanan ma, Owen Gingerich wani farfesa na yanayin sammai a Jami’ar Harvard, ya rubuta: “Wannan rashin son kai ya ta da wata tambaya da amsar ba ta cikin binciken da ’yan kimiyya suka yi game da dabbobin da ke cikin daji. Amma amsar ta gaskiya tana cikin halayen da Allah ya ba mu na jin tausayi wanda ya haɗa da lamiri.”
Menene Ka Koya?
• Me ya sa za a ce dukan mutane sun san abin da yake da kyau da marar kyau?
• Me ya sa ya kamata mu mai da hankali game da barin lamirinmu ya yi mana ja-gora?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu kyautata lamirinmu?
[Hotuna a shafi na 11]
Lamirin Dauda ya dame shi . . .
amma lamirin Shawulu na garin Tarsus bai dame shi ba
[Hoto a shafi na 12]
Za mu iya koyar da lamirinmu