Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 11/1 p. 3
  • Ƙalubalen Kasancewa da Tawali’u

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙalubalen Kasancewa da Tawali’u
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Koyi Tawali’u Na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Jehovah Ya Bayyana Ɗaukakarsa Ga Masu Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • ‘Ku Yafa Zuciya ta Tawali’u’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 11/1 p. 3

Ƙalubalen Kasancewa da Tawali’u

MUTANE da yawa suna ganin cewa tawali’u ba shi da muhimmanci a duniya a yau. Mutane da suke shugabantar wasu kuma suke samun nasara su ne masu ɗaukaka kansu, masu fahariya, kuma su ne masu nace wa samun abin da suke so. Mutane da yawa suna sha’awar rayuwar da masu arziki da sanannu suke yi, amma ba sa sha’awar masu tawali’u. Waɗanda suka yi nasara suna fahariya cewa sun yi nasara ne saboda ƙoƙarinsu. Maimakon su kasance da tawali’u, suna yaba wa kansu don nasarar da suka samu.

Wani mai bincike daga Kanada ya yi magana game da halin son kai da girman kai da ake nunawa a ƙasarsu. Waɗansu suna ganin cewa muna zaune ne a zamanin da jin daɗi ya fi rayuwa mai kyau muhimmancikuma lura cewa mutane a yau sun damu ne kawai da kansu. A irin wannan duniyar, mutane ba za su ɗauki tawali’u da muhimmanci ba.

Hakika, yawancin mutane sun yarda cewa tawali’u ya dace da waɗansu ne kawai, tun da ana jin daɗin yin sha’ani da mutane masu tawali’u. Amma, a wannan duniyarmu da take cike da gasa, wasu mutane suna tunanin cewa idan suka zama masu tawali’u, za a mai da su wawaye.

Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki ta annabta cewa a zamaninmu mutane za su zama “masu-ruba, masu-girman kai.” (2 Timothawus 3:1, 2) Ka yarda cewa wannan annabcin yana cika? Kana ganin ya dace mutum ya kasance mai tawali’u? Ko kuma kana tunanin cewa wanda yake da tawali’u wawa ne, wanda ake saurin cutarsa?

Hakika, Littafi Mai Tsarki ya nuna mana dalilin da ya sa tawali’u yake da muhimmanci da kuma abin da ya sa ya kamata mu kasance da shi. Ya faɗi daidaitacen ra’ayi mai kyau game da tawali’u kuma ya nuna cewa tawali’u na gaske alama ce ta ƙarfi ba wawanci ba. Talifi na gaba zai faɗi dalilin hakan.

[Hoto a shafi na 3]

Yaya ya kamata mu ji game da nasarorinmu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba