Biɗar Rayuwa Mai Ma’ana
“Abin da yake da numfashi duka shi yi yabon Ubangiji.”—ZABURA 150:6.
1. Ka kwatanta yadda wani matashi ya biɗi rayuwa mai ma’ana.
“NA KARANTA aikin likita domin ina son in taimaka wa mutane a rayuwata. Na yi tunanin cewa yin suna da kuma kuɗin da zan samu a aikin likita za su sa ni farin ciki,” in ji Seung Jin, wanda ya girma a ƙasar Koriya.a “Sa’ad da na fahimci cewa likita ba zai iya taimaka wa mutane yadda ya kamata ba, abin ya ɓata mini rai. Sai na soma koyan zane, amma zanen da nake yi bai taimaka wa mutane yadda nake tsammani ba, kuma hakan ya sa na ji cewa na nuna son kai. Sai na koma koyarwa a makaranta kuma ba da daɗewa ba na fahimci cewa zan iya gaya wa mutane gaskiya ne kawai amma ba zan iya yi masu ja-gorar da za ta sa su sami farin ciki na ainihi ba.” Kamar yawancin mutane, Seung Jin yana biɗar rayuwa mai ma’ana.
2. (a) Mecece ma’anar kasancewa da manufa a rayuwa? (b) Ta yaya ne muka sani cewa akwai dalilin da ya sa Mahalicci ya saka mu a duniya?
2 Kasancewa da manufa ta gaske a rayuwa yana nufin mutum ya kasance yana da dalilin ci gaba da rayuwa, manufa da ta fita sarai a rayuwarsa, da kuma abin da yake so ya cim ma a dukan ƙoƙarce-ƙoƙarcensa. Mutane za su iya kasancewa da irin wannan manufar kuwa? Ƙwarai kuwa! Domin Allah ya ba mu hankali, lamiri, da kuma iya yin tunani, hakan ya nuna cewa Mahalicci yana da manufa mai kyau na ajiye mu a duniya. Babu shakka, idan muka yi rayuwar da ta jitu da nufin Mahalicci ne kawai za mu iya kasancewa da manufa mai kyau kuma mu cim ma manufarmu.
3. Menene nufin Allah ga mutane ya ƙunsa?
3 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa nufin Allah a gare mu ya ƙunshi abubuwa masu yawa. Alal misali, hanya mai ban al’ajabi da aka halicce mu ya bayyana ƙauna marar son kai da Allah ya nuna. (Zabura 40:5; 139:14) Saboda haka, yin rayuwar da ta jitu da nufin Allah yana nufin nuna ƙauna ga mutane ba tare da son kai ba kamar yadda Allah ya yi. (1 Yohanna 4:7-11) Kuma hakan yana nufin yin biyayya ga umurnin Allah da ke taimaka mana mu yi rayuwar da ta jitu da manufarsa mai kyau.—Mai-Wa’azi 12:13; 1 Yohanna 5:3.
4. (a) Menene ake bukata don a kasance da manufa mai ma’ana a rayuwa? (b) Mecece manufa mafi ma’ana da mutum zai iya biɗa?
4 Nufin Allah ne cewa mutane su yi rayuwa cikin farin ciki kuma salama ta kasance a tsakaninsu da kuma sauran halittu. (Farawa 1:26; 2:15) Amma menene muke bukatar mu yi don mu kasance da farin ciki, mu sami kāriya, da kuma kwanciyar hankali? Kamar yaron da ke bukatar ya ga iyayensa a kusa da shi don ya yi farin ciki ya kuma sami kāriya, muna bukatar mu kasance da dangantaka mai kyau da Ubanmu na samaniya don rayuwarmu ta kasance da ma’ana da kuma manufa. (Ibraniyawa 12:9) Allah ya buɗe mana hanyar samun irin wannan dangantakar da shi ta wajen barin mu mu kusance shi da kuma addu’armu da yake ji. (Yaƙub 4:8; 1 Yohanna 5:14, 15) Idan muka yi “tafiya tare da Allah” cikin bangaskiya kuma muka zama abokansa, za mu iya jawo farin ciki da ɗaukaka ga Ubanmu na samaniya. (Farawa 6:9; Misalai 23:15, 16; Yaƙub 2:23) Wannan ita ce manufa mafi girma da mutum zai iya biɗa. Mai zabura ya rubuta: “Abin da yake da numfashi duka shi yi yabon Ubangiji.”—Zabura 150:6.
Mecece Manufarka a Rayuwa?
5. Me ya sa mai da abin duniya abu na farko a rayuwa wauta ce?
5 Ɗaya daga cikin nufin Allah shi ne mu kula da kanmu sosai da kuma iyalinmu. Wannan ya haɗa da kula da bukatunmu na zahiri da na ruhaniya. Amma muna bukatar daidaita a waɗannan batutuwan, saboda kada abubuwa na zahiri da kuma damuwarmu su sha kan abubuwa mafi muhimmanci na ruhaniya. (Matta 4:4; 6:33) Amma abin baƙin ciki shi ne, yawancin mutane sun mai da hankalinsu ne kawai a kan tara abin duniya. Wauta ce neman biyan bukatunmu da abin duniya kawai. Wani bincike da aka yi na masu kuɗi sosai a Asiya ya nuna cewa yawancinsu “suna jin cewa ba su da kāriya da kwanciyar hankali, duk da cewa suna more sunan da suka yi da kuma abubuwan da suka tara.”—Mai-Wa’azi 5:11.
6. Wace shawara ce Yesu ya ba da game da neman arziki?
6 Yesu ya ambata “ruɗin dukiya.” (Markus 4:19) Ta yaya ne dukiyoyi suke iya ruɗar mutum? Sukan bayyana kamar suna kawo farin ciki, amma ba sa kawowa. “Mutumin da ke son kuɗi ba zai taɓa isar sa ba,” in ji Sulemanu Sarki mai hikima. (Mai-Wa’azi 5:10, The New English Bible) Amma zai yiwu mutum ya biɗi makasudin tara abin duniya kuma ya bauta wa Allah da dukan zuciyarsa? A’a, ba zai yiwu ba. Yesu ya ce: “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.” Yesu ya aririci mabiyansa su tara wa kansu dukiya ba a duniya ba amma “a Sama,” wato, su yi suna mai kyau a wurin Allah, wanda “ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.”—Matta 6:8, 19-25; LMT.
7. Ta yaya ne za mu iya “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai”?
7 Sa’ad da yake rubuta wasiƙa ga abokin aikinsa Timoti, manzo Bulus ya yi gargaɗi sosai game da wannan batun. Ya gaya wa Timoti: “Ka dokace waɗanda ke mawadata . . . kada su ratayi begensu bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah, wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu; . . . su kasance da niyyar babbayarwa, masu-son zumunta; suna ajiye wa kansu tushe mai-kyau domin wokaci mai-zuwa, da za su ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.”—1 Timothawus 6:17-19.
Menene “Hakikanin Rai”?
8. (a) Me ya sa yawancin mutane suke neman kuɗi da yin suna? (b) Menene suka ƙi fahimta?
8 Ga yawancin mutane, furcin nan “hakikanin rai” yana nufin tara kayan alatu da kuma jin daɗi. Wata jarida ta Asiya ta ce: “Waɗanda suke kallon fim ko talabijin suna yin muradin abin da suka gani, da kuma yin mafarkin abin da ba su samu ba.” Yawancin mutane sun mai da neman kuɗi da yin suna manufarsu a rayuwa. Yawancin mutane suna saɗaukar da kuzarinsu, lafiyarsu, rayuwar iyali, da abubuwa masu muhimmanci na ruhaniya domin neman waɗannan abubuwan. Mutane kaɗan ne kawai suke tsayawa su yi tunani cewa waɗannan kayan alatu da rayuwar jin daɗi da ake nunawa a kan talabijin suna nuna “ruhun duniya” ne, wato, irin tunanin da ke rinjayar biliyoyin mutane a duniya kuma yake motsa su su juya baya ga nufin Allah a gare mu. (1 Korinthiyawa 2:12; Afisawa 2:2) Babu shakka, shi ya sa mutane da yawa ba sa farin ciki a yau!—Misalai 18:11; 23:4, 5.
9. Menene mutane ba za su iya taɓa cim ma ba, kuma me ya sa?
9 Waɗanda suke aiki tuƙuru domin su kula da wasu, su kawar da yunwa, rashin lafiya da kuma rashin adalci fa? Aiki mai kyau da kuma sadaukar da kai da suke yi yana taimakawa sosai a yawancin lokaci. Amma, duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcen da suke yi, ba za su iya canja wannan duniyar zuwa mai kyau ba. Me ya sa? Domin a gaskiya “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan,” kuma ba ya son a canja ta.—1 Yohanna 5:19.
10. A wane lokaci ne masu aminci za su mori “hakikanin rai”?
10 Zai zama abin baƙin ciki sosai idan mutum ba shi da bege fiye da na yin rayuwa a wannan duniyar ta yanzu! Bulus ya rubuta cewa: “Idan cikin wannan rai kaɗai mun yi bege ga Kristi, mun fi dukan mutane ban tausai.” “Bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu,” shi ne halin waɗanda suka gaskata cewa wannan rayuwar ita ke nan kawai. (1 Korinthiyawa 15:19, 32) Amma muna da bege, “bisa ga alkawarinsa [Allah], muna sauraron sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.” (2 Bitrus 3:13) A wannan lokacin, Kiristoci za su iya morar “hakikanin rai,” wato, “rai na har abada” a cikin kamilta, a sama ko a ƙarƙashin sarauta ta ƙauna a Mulkin Allah.—1 Timothawus 6:12.
11. Me ya sa faɗaɗa aikin Mulkin Allah yake da ma’ana sosai?
11 Mulkin Allah ne kawai zai iya magance matsalolin mutane gaba ɗaya. Yin aiki tuƙuru wajen faɗaɗa al’amuran Mulkin Allah shi ne abu mafi ma’ana da mutum zai iya biɗa. (Yohanna 4:34) Yayin da muke aikin nan, muna morar dangantaka mai kyau da Ubanmu na sama. Kuma muna farin cikin yin hidima tare da miliyoyin ’yan’uwa na ruhaniya da suke biɗar irin wannan manufar a rayuwa.
Yin Sadaukarwa da ta Dace
12. Ka bambanta rayuwa a wannan duniyar da “hakikanin rai.”
12 Wannan duniyar “tana wucewa, duk da sha’awatata,” in ji Littafi Mai Tsarki. Babu wani sashen duniyar Shaiɗan, har da yin suna da arziki da ba za a halaka ba, “amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:15-17) Akasin arziki marar tabbaci, da ɗaukaka na ɗan lokaci, da kuma jin daɗi na gajeren lokaci a wannan duniyar, “hakikanin rai,” wato, rai na har abada a ƙarƙashin Mulkin Allah, zai kasance ne har abada kuma ya cancanci mu yi sadaukarwa, amma sadaukarwar da ta dace.
13. Ta yaya ne wasu ma’aurata suka yi sadaukarwar da ta dace?
13 Yi la’akari da Henry da Suzanne. Sun yi imani sosai da alkawarin da Allah ya yi cewa duka waɗanda suka mai da Mulkin abin farko a rayuwarsu za su sami taimakon Allah. (Matta 6:33) Saboda haka, maimakon su biyun su ɗinga aiki don su biya kuɗin gidan haya mai tsada, sun zaɓi su zauna a gidan haya marar tsada domin su ba da ƙarin lokaci wajen biɗar abubuwa na ruhaniya su da yaransu mata biyu. (Ibraniyawa 13:15, 16) Wata ƙawarsu da take da manufa mai kyau ba ta fahimci irin wannan zaɓin da suka yi ba. Sai ta ce wa Suzanne: “Ƙawata, idan fa kina son ki zauna a wurin da ya fi wannan kyau, kina bukatar ki sadaukar da wani abu.” Amma, Henry da Suzanne sun san cewa saka Jehobah farko yana “da alkawari ga rai na yanzu, da na mai-zuwa.” (1 Timothawus 4:8; Titus 2:12) Yaransu mata sun girma sun zama masu wa’azi da kuzari na cikakken lokaci. A matsayin iyali, sun ga cewa ba su rasa komi ba, maimakon haka, sun amfana sosai ta wajen mai da biɗar “hakikanin rai” manufarsu.—Filibbiyawa 3:8; 1 Timothawus 6:6-8.
Kada Ka ‘Cika Moriyar’ Duniya
14. Waɗanne haɗarurruka ne za mu fuskanta idan muka mance ainihin manufarmu?
14 Akwai haɗari sosai idan muka mance ainihin manufarmu kuma muka yi watsi da “hakikanin rai.” Muna iya “shaƙe da sha’ani, da wadata, da annashuwa ta wannan rai.” (Luka 8:14) Sha’awar da ta wuce kima da kuma yawan damuwa a kan abubuwan biyan bukata suna iya sa mutum ya nitse sosai a wannan duniyar. (Luka 21:34) Abin baƙin ciki, wasu sun saka hannu cikin mugun son kuɗi kuma sun “ratse daga imani, sun huda kansu da baƙinciki mai-yawa,” har ma sun rasa dangantakarsu mai tamani da Jehobah. Wannan sakamako ne marar kyau na ƙin riƙe “rai wanda shi ne hakikanin rai”!—1 Timothawus 6:9, 10, 12; Misalai 28:20.
15. Ta yaya ne wata iyali ta amfana daga ƙin ‘moriyar duniya’ sosai?
15 Bulus ya shawarci “waɗanda su ke moron duniya, [su yi] kamar ba su cika moriyatata ba.” (1 Korinthiyawa 7:31) Keith da Bonnie sun bi wannan shawarar. “Na zama Mashaidin Jehobah a lokacin da na kammala makarantar likitan haƙori,” in ji Keith. “Ina da zaɓi. Ina iya kula da masu ciwon haƙori masu yawa kuma in samu kuɗi sosai, amma hakan zai shafi bautarmu ga Allah. Na rage adadin marasa lafiya da nike gani domin na sami ƙarin lokaci na kula da bukatu na ruhaniya da na motsin rai na iyalinmu, wanda ya haɗa da yara mata guda biyar. Ko da yake ba mu da ajiyayyun kuɗi a yawancin lokaci, mun koyi mu yi maneji, kuma muna samun abin da muke bukata a kowane lokaci. Iyalinmu ta ƙara kusantar juna, kuma muna cike da farin ciki. Daga baya, mu duka mun soma hidima na cikakken lokaci. Yanzu yaranmu mata sun yi aure, kuma uku daga cikinsu sun riga sun haifi na su yaran. Iyalinsu tana cike da farin ciki, domin sun ci gaba da sa nufin Jehobah abin farko a rayuwarsu.”
Ka Mai da Nufin Allah Abin Farko a Rayuwarka
16, 17. Waɗanne misalai na mutane ƙwararru ne Littafi Mai Tsarki ya ambata, kuma ta yaya ake tunawa da su?
16 Littafi Mai Tsarki ya ba da misalan waɗanda suka yi nufin Allah da kuma waɗanda suka ƙi yin nufinsa. Darussan da ke cikin waɗannan misalan sun shafi kowa da kowa, a duk inda mutum yake zaune, da kuma yanayinsa. (Romawa 15:4; 1 Korinthiyawa 10:6, 11) Nimrod ya gina manyan birane, amma ya yi hakan ne don hamayya da Jehobah. (Farawa 10:8, 9) Yawanci kuma misalai ne masu kyau. Alal misali, Musa bai mai da sunansa mai martaba a ƙasar Masar ya zama manufarsa a rayuwa ba. Maimakon haka, ya ɗaukaka gatarsa ta ruhaniya a matsayin “wadata . . . mafi girma bisa ga dukiyar Masar.” (Ibraniyawa 11:26) Luka wanda likita ne wataƙila ya taimaka wa Bulus da wasu a lokacin da suka yi rashin lafiya. Amma Luka ya ba da taimako mafi girma a matsayin mai wa’azi da kuma marubucin Littafi Mai Tsarki. Shi kuma Bulus, sananne ne ba a matsayin Lauya ba, amma a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje, wato, “manzon Al’ummai.”—Romawa 11:13.
17 Ana tuna Dauda ne ba a matsayin shugaban sojoji ba ko marubuci da kuma mawaƙi, amma a matsayin ‘wanda Ubangiji yake so.’ (1 Samuila 13:14; LMT) Mun san Daniel ne ba don matsayinsa ba a fadar Babila, amma don hidimarsa ga Jehobah a matsayin annabi mai aminci; ba a san Esther a matsayin sarauniyar Farisa ba, amma domin gaba gaɗinta da kuma bangaskiyarta; Bitrus, Andarawus, Yakubu, da Yohanna, ba don nasarar da suka yi wajen kamun kifi ba, amma a matsayin manzannin Yesu. Mafi girma, a wurin mu Yesu ba ‘masassaƙi’ ba ne, amma “Kristi ne.” (Markus 6:3; Matta 16:16) Duka waɗannan mutanen sun fahimci cewa duk wata iyawa, dukiya, ko suna da suka mora, ainihin abin da za su mai da wa hankali a rayuwarsu ita ce hidimar Allah, ba aikin da suke yi ba. Sun san cewa manufa mafi amfani kuma wadda za ta kawo sakamako mai kyau ita ce mutum ya kasance mai jin tsoron Allah.
18. Ta yaya ne wani Kirista matashi ya yanke shawarar yin amfani da rayuwarsa, kuma menene ya fahimta?
18 Seung Jin, da aka ambata ɗazu ya fahimci wannan batun. “Maimakon in yi amfani da duka kuzari na a wajen aikin likita, zane, ko koyarwa a makaranta, na yanke shawarar yin amfani da rayuwata cikin jituwa da keɓe kaina da na yi ga Allah,” in ji shi. “A yanzu ina yin hidima a inda ake da bukata mai girma na masu koyar da Littafi Mai Tsarki, kuma ina taimaka wa mutane su gane hanyar rai madawwami. A dā ina tunanin cewa kasancewa mai hidima na cikakken lokaci ba zai ɗauki lokaci na ba. Amma a yanzu na ga cewa ba haka rayuwa take ba yayin da nike ƙoƙartawa wajen ƙara kyautata halaye na da kuma iya yin aiki tare da mutanen da suka fito daga wurare dabam dabam. Na ga cewa mai da nufin Jehobah manufarmu ita ce hanyar rayuwa mafi ma’ana.”
19. Ta yaya za mu iya samun manufa mafi ma’ana a rayuwa?
19 Mu Kiristoci, muna da sani na ceton rai da kuma begen samun ceto. (Yohanna 17:3) Saboda haka, “kada [mu] karɓi alherin Allah banza.” (2 Korinthiyawa 6:1) Maimakon haka, bari mu yi amfani da ranakunmu da kuma shekarunmu masu tamani wajen yabon Jehobah. Bari mu sanar da sani da ke kawo farin ciki a yanzu kuma wanda zai kai ga rai na har abada. Idan muka yi haka, za mu shaida kalaman Yesu: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayukan Manzanni 20:35) Kuma za mu sami manufa mafi ma’ana a rayuwa.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Mecece manufa mafi ma’ana da za mu iya samu a rayuwa?
• Me ya sa biɗar abubuwan duniya wauta ce?
• Menene “hakikanin rai” da Allah ya yi alkawarinsa?
• Ta yaya ne za mu iya yin amfani da rayuwarmu a yin nufin Allah?
[Hotuna a shafi na 18]
Kiristoci suna bukatar su yi sadaukarwar da ta dace