Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 10/1 pp. 13-15
  • Darussa Daga Littafin Hosea

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Hosea
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “KA ƊAUKO MATA TA FASIKANCI”
  • (Hosea 1:1–3:5)
  • “Ubangiji Yana da Mahawara”
  • (Hosea 4:1–13:16)
  • “HANYOYIN UBANGIJI MADAIDAITA NE”
  • (Hosea 14:1-9)
  • Annabcin Yusha’u Yana Taimakonmu Mu Bi Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Bi Allah, Ka Sami Alheri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Hosiya
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • “Hanyoyin Ubangiji Masu Gaskiya Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 10/1 pp. 13-15

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Hosea

AN KUSAN daina bauta ta gaskiya a masarautar ƙabilu goma na arewacin Isra’ila. A lokacin sarautar Jeroboam na Biyu, an yi wadata a Isra’ila, amma hakan ya ragu ba da daɗewa ba bayan mutuwarsa. Hargitsi da zirga-zirga ta siyasa ne suka biyo bayan hakan. An kashe huɗu daga cikin sarakuna shida da suka bi bayansa. (2 Sarakuna 14:29; 15:8-30; 17:1-6) Aikin annabci da Hosea ya yi na shekara 59, wanda ya soma a shekara ta 804 K.Z., ya kai wannan lokacin hargitsi.

An nuna sarai yadda Jehobah ya ji game da al’ummar Isra’ila daga abin da ya faru a auren Hosea. Jigon saƙon Hosea shi ne fallasa laifin Isra’ila da annabcin hukunci a kanta da kuma masarautar Yahuda. Hosea ya rubuta dukan waɗannan saƙon a cikin littafi mai ɗauke da sunansa ta wajen yin amfani da kalmomi masu sauƙi da kuma iko cikin alama. Tun da yake littafin yana cikin hurarriyar Kalmar Allah, saƙonsa mai rai ce kuma mai aikatawa.—Ibraniyawa 4:12.

“KA ƊAUKO MATA TA FASIKANCI”

(Hosea 1:1–3:5)

Jehobah ya gaya wa Hosea: “Je ka, ka ɗauko mata ta fasikanci.” (Hosea 1:2) Hosea ya yi biyayya kuma Gomer ta haifa masa ɗa. Bayan haka, a bayyane yake cewa yara biyu da ta haifa shegu ne. Ma’anar sunayensu, wato, Lo-ruhamah da Lo-ammi, suna nuni ga yadda Jehobah ya ƙi nuna wa Isra’ila jin ƙai da kuma yadda ya yi watsi da mutanensa marasa aminci.

Yaya Jehobah yake ji game da mutanensa masu tawaye? Ya gaya wa Hosea: “Je ka, har wa yau, ka ƙaunaci mace ƙaunataciyar mijinta amma mazinaciya, kamar yadda Ubangiji ya ke ƙaunar ’ya’yan Isra’ila, ko da sun juya ga bin waɗansu allohi.”—Hosea 3:1.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:1—Me ya sa Hosea ya ambata sunayen dukan sarakuna huɗu da suka yi sarauta a Yahuda a lokacin hidimarsa amma sunan sarkin Isra’ila guda ne kawai ya ambata? Ya yi hakan ne domin zuriyar Dauda kaɗai ce take da ikon yin sarautar mutanen Allah. Sarakunan Yahuda sun fito daga zuriyar Dauda ne amma sarakunan masarautar arewa ba su fito daga zuriyarsa ba.

1:2-9—Da Gaske ne Hosea ya auri mata da ta zama fasiƙa? Hakika, Hosea ya auri matar da ta zama kwartuwa. Annabin bai faɗi kome ba da ya nuna cewa abin da ya faɗa game da rayuwar iyalinsa mafarki ne ko kuma wahayi.

1:7—Yaushe ne aka nuna wa gidan Yahuda jin ƙai kuma aka cece su? Wannan ya faru a shekara ta 732 K.Z., a zamanin Sarki Hezekiya. A lokacin, Jehobah ya sa ’yan Assuriya suka daina kai wa Urushalima hari, sa’ad da ya sa mala’ika guda ya kashe sojojin magabta guda 185,000 a cikin dare ɗaya. (2 Sarakuna 19:34, 35) Ta hakan ne Jehobah ya ceci Yahuda, ba “da baka, ko da takobi, ko da yaƙi, ko da dawakai, ko da mahaya” ba, amma ta mala’ika guda.

1:10, 11—Tun da masarautar arewa ta Isra’ila ta faɗi a shekara ta 740 K.Z., ta yaya ’ya’yan Isra’ila za su “taru” su haɗa kai da ’ya’yan Yahuda? Yawanci daga masarauta na arewa sun tafi Yahuda kafin a kai mazaunan ƙasar Yahuda bauta a Babila a shekara ta 607 K.Z. (2 Labarbaru 11:13-17; 30:6-12, 18-20, 25) Sa’ad da Yahudawa da suke zaman bauta suka koma ƙasarsu a shekara ta 537 K.Z., zuriyar waɗanda suke masarauta ta arewa suna cikin waɗanda suka koma.—Ezra 2:70.

2:21-23—Menene waɗannan kalmomin da Jehobah ya annabta suke nufi: “Zan shibka ta [Jezreel] gareni cikin ƙasan; ita wadda ba ta sami jinƙai ba zan nuna mata jinƙai”? Jezreel ne sunan ɗan fari da Gomer ta haifa wa Hosea. (Hosea 1:2-4) Wannan sunan da ke nufin “Allah Zai Shuka Iri,” furci ne na annabci da ke nuna cewa Jehobah zai tara mutane masu aminci da suka rage a shekara ta 537 K.Z., kuma ya shuka su kamar iri a Yahuda. Ƙasar da ta zama kango shekaru 70 za ta ba da amfanin hatsi, inabi mai zaƙi, da mai. Annabcin ya nuna cewa ƙasar za ta ba da albarka kuma Allah zai kawo ruwan sama. Dukan waɗannan za su faru domin a biya bukatun raguwar mutane da suke dawowa ne. Manzanni Bulus da Bitrus sun yi amfani da Hosea 2:23 wajen tattara raguwar Isra’ila ta ruhaniya.—Romawa 9:25, 26; 1 Bitrus 2:10.

Darussa Dominmu:

1:2-9; 3:1, 2. Hosea ya yi sadaukarwa ta wajen kasancewa cikin auren don yana son ya yi biyayya da nufin Allah! Muna shirye ne mu bar abubuwa da muke so don mu yi nufin Allah?

1:6-9. Kamar yadda Jehobah ya tsane zina ta zahiri haka ya tsane zina ta ruhaniya.

1:7, 10, 11; 2:14-23. Abin da Jehobah ya annabta game da Isra’ila da Yahuda ya faru. Kalmomin Jehobah a koyaushe suna cikawa.

2:16, 19, 21-23; 3:1-4. Jehobah yana shirye ya gafarta wa waɗanda suka tuba da dukan zuciyarsu. (Nehemiah 9:17) Kamar Jehobah, ya kamata mu zama masu juyayi da jin ƙai sa’ad da muke sha’ani da mutane.

“Ubangiji Yana da Mahawara”

(Hosea 4:1–13:16)

“Ubangiji yana da mahawara da mazaunan ƙasan.” Me ya sa? Domin “babu gaskiya, ko jinƙai, ko sanin Allah a ƙasan.” (Hosea 4:1) Mutanen Isra’ila masu taurin kai sun yi zamba da zubar da jini kuma sun yi fasikanci na zahiri da na ruhaniya. Maimakon su nemi taimakon Allah, suka “kira zuwa ga Masar, su kan tafi wurin Assyria.”—Hosea 7:11.

Jehobah ya yi shelar hukuncinsa, yana cewa: “An haɗiye Isra’ila.” (Hosea 8:8) Masarautar Yahuda tana da laifi. “Ubangiji yana da mahawara da Yahuda” in ji Hosea 12:2, “za ya yi ma Yaƙub hukumci bisa ga al’amuransa; bisa ga ayukansa za ya yi masa sakamako.” Allah ya yi tabbataccen alkawarin maidowa: “Zan panshe su daga ikon kabari; zan panshe su daga mutuwa.”—Hosea 13:14.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

6:1-3—Wanene yake cewa: “Mu zo, mu koma wurin Ubangiji”? Wataƙila Isra’ilawa marasa aminci ne suke ƙarfafa juna su koma wurin Jehobah. Idan haka ne, suna nuna kamar sun tuba ne. Ƙaunarsu ta alheri na ɗan lokaci ne kuma tana saurin wucewa kamar “jibo na safiya, kamar raɓa da ta kan watse tun da wuri.” (Hosea 6:4) A wani ɓangare kuma, mai yiwuwa Hosea ne yake magana yana roƙon mutane su koma wurin Jehobah. Ko yaya dai, mazauna masarautar ƙabilu goma na Isra’ila masu taurin kai suna bukatar su tuba da gaske kuma su koma ga Jehobah.

7:4—Ta yaya ne Isra’ilawa mazinata suke kamar “tanderu”? Wannan kwatanci ya nuna yawan mugun sha’awoyin da ke zuciyarsu.

Darussa Dominmu:

4:1, 6. Idan muna son mu ci gaba da samun alherin Jehobah, dole ne mu ci gaba da koya game da shi kuma mu yi rayuwar da ta jitu da abin da muka koya.

4:9-13. Jehobah zai hukunta waɗanda suke yin lalata kuma suke saka hannu a bauta marar tsarki.—Hosea 1:4.

5:1. Ya kamata waɗanda suke shugabanci tsakanin mutanen Allah su ƙi ridda gabaki ɗaya. Idan ba haka ba, za su rinjayi wasu su soma bautar ƙarya, da haka su zama “tarko” a gare su.

6:1-4; 7:14,16. Tuban baki kawai munafunci ne kuma ba shi da amfani. Don ya samu jinƙan Allah, dole ne wanda ya yi laifi ya nuna ya tuba da dukan zuciyarsa kuma ya dawo ga wani abu “maɗaukaki,” wato, bauta mai ɗaukaka. Ya kamata ayyukansa su jitu da mizanan Allah masu girma.—Hosea 7:16.

6:6. Yin zunubi yana nuna rashin ƙauna ta aminci ga Allah. Ba yawan hadayu na ruhaniya da zai daidaita wannan kasawar.

8:7, 13; 10:13. Ƙa’idar cewa “iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe” ta zama gaskiya a batun Isra’ilawa masu bautar gunki.—Galatiyawa 6:7.

8:8; 9:17; 13:16. Annabce-annabce game da masarauta na arewa sun cika sa’ad da ’yan Assuriya suka ci babban birninta, Samariya. (2 Sarakuna 17:3-6) Muna da tabbaci cewa Allah zai yi abin da ya faɗa.—Litafin Lissafi 23:19.

8:14. Jehobah ya aika “da wuta a bisa biranen [Yahuda],” a shekara ta 607 K.Z., ta hannun Babiloniyawa, kuma hakan ya jawo halakar da aka annabta a kan Urushalima da kuma ƙasar Yahuda. (2 Labarbaru 36:19) Dole ne abin da Allah ya faɗa ya faru.—Joshua 23:14.

9:10. Ko da yake sun keɓe kansu ga Allah na gaskiya, Isra’ilawa sun “zo Baal-peor, suka keɓe kansu ga abin nan mai-ban ƙyama.” Za mu zama masu hikima ne idan ba mu bi mummunan misalinsu ba kuma muka guji ƙin cika keɓe kanmu da muka yi ga Jehobah.—1 Korinthiyawa 10:11.

10:1, 2, 12. Ya kamata mu bauta wa Allah ba tare da riya ba. Idan ‘muka shibka cikin adalci, za mu yi girbi bisa ga jinƙai na Allah.’

10:5. Beth-aven (da ke nufin “Gidan ban Ciwo”) sunan reni ne da aka ba Bethel (da ke nufin “Gidan Allah”). Sa’ad da aka kai gunkin maraƙi na Beth-aven zuwa bauta, mazaunan Samariya sun yi makokin rasa gunkin da suke bautawa. Wauta ce mutum ya dogara ga gunkin da ba shi da rai da ba zai ma iya kāre kansa ba!—Zabura 135:15-18; Irmiya 10:3-5.

11:1-4. Jehobah koyaushe yana bi da mutanensa cikin ƙauna. Ba da kai ga Allah ba zalunci ba ne.

11:8-11; 13:14. Abin da Jehobah ya faɗa game da maidowar mutanensa zuwa bauta ta gaskiya ‘ba za ta koma wurinsa wofi ba.’ (Ishaya 55:11) A shekara ta 537 K.Z., zaman bauta a Babila ya ƙare kuma waɗanda suka rage suka koma Urushalima. (Ezra 2:1; 3:1-3) Dukan abin da Jehobah ya faɗa ta wurin annabawansa zai cika.

12:6. Ya kamata mu ƙuduri aniya mu nuna ƙauna ta alheri, mu yi adalci, kuma mu kasance da bege ga Jehobah koyaushe.

13:6. Isra’ilawa sun “ƙoshi, zuciyassu kuwa ta ɗaukaka; domin wannan sun manta da [Jehobah].” Muna bukatar mu mai da hankali da halin girman kai.

“HANYOYIN UBANGIJI MADAIDAITA NE”

(Hosea 14:1-9)

Hosea ya yi roƙo: “Ka komo wurin Ubangiji Allahnka; gama ka fāɗi ta wurin saɓonka.” Ya aririce mutane su gaya wa Jehobah: “Ka kawasda dukan saɓo, ka karɓi abin da ke nagari; da hakanan za mu kawo hadayun leɓunanmu misalin bajimai.”—Hosea 14:1, 2.

Ya kamata mai zunubi da ya tuba ya je wurin Jehobah, ya amince da hanyoyinsa, kuma ya miƙa masa hadayu na yabo. Me ya sa? Domin “hanyoyin Ubangiji madaidaita ne, masu-adilci kuwa za su riƙa tafiya a cikinsu.” (Hosea 14:9) Muna farin cikin cewa mutane da yawa “za su zo wurin Ubangiji da wurin alherinsa kuma cikin kwanakin ƙarshe.”—Hosea 3:5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba