Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 10/1 pp. 21-25
  • Biɗar Nufin Allah A Yau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Biɗar Nufin Allah A Yau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ɗaukan Matakan da za su Kawo Ci Gaba da Kuma Amfani
  • Ka Kasance da Daidaita
  • Biɗar Nufin Allah a Rayuwa
  • Rayuwa Mai Amfani Sosai
  • Biɗar Rayuwa Mai Ma’ana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku?
    Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku?
  • Ka Tuna da Masu Hidima ta Cikakken Lokaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Yadda Za Mu Yi Farin Ciki Sa’ad da Muka Soma Sabuwar Hidima
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 10/1 pp. 21-25

Biɗar Nufin Allah A Yau

“[Kristi] ya mutu sabili da duka, domin waɗanda ke rayuwa kada su ƙara rayuwa da kansu.”—2 KORINTHIYAWA 5:15.

1. Ka ambata abin da wani mai wa’azi a ƙasashen waje ya shaida a inda yake hidimarsa.

“MOTARMU ita ce motar farar hula ta farko da ta fara shiga wani ƙauye a Afirka bayan an kammala yaƙin basasa,” in ji wani mai wa’azi a ƙasashen waje mai suna Aaron.a “Mun kasa aika saƙo ga ƙaramar ikilisiyar da ke ƙauyen, kuma muna bukatar mu kula da bukatun ’yan’uwan. Ban da abinci, sitira, da kuma littattafan da za su taimaka a fahimci Littafi Mai Tsarki, mun zo da kaset ɗin bidiyon nan Jehovah’s Witnesses—The Organization Behind the Name.b Mutane masu yawa da suke son gaskiya sun yi jerin gwano zuwa ‘gidan kallo’ na ƙauyen don su kalli fim ɗin, wato a ƙarƙashin rumfar da aka yi da ciyawa inda aka ajiye bidiyo da talabijin, hakan ya sa muka nuna shi sau biyu. Mun sami mutane masu yawa da suke son nazarin Littafi Mai Tsarki a waɗannan lokatai da muka nuna fim ɗin. Babu shakka, kwalliya ta biya kuɗin sabulu.”

2. (a) Me ya sa Kiristoci suka yanke shawarar yin amfani da ransu a hidimar Allah? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika yanzu?

2 Me ya sa Aaron da abokansa suka fita yin wannan aiki mai wuya? Domin suna godiya ga hadayar fansa ta Yesu Kristi, sun keɓe rayuwarsu ga Allah kuma suna son yin amfani da rayuwarsu cikin jituwa da nufin Allah. Kamar su, duka Kiristocin da suka keɓe kansu sun ƙudurta cewa ba za su yi “rayuwa . . . [don] kansu” ba, amma za su yi iya ƙoƙarinsu “sabili da bishara.” (2 Korinthiyawa 5:15; 1 Korinthiyawa 9:23) Sun san cewa a lokacin da aka halaka wannan duniyar, duka kuɗi da kuma suna da aka yi a wannan duniyar za su zama marar amfani. Domin suna raye da kuma koshin lafiya, suna son su yi amfani da ransu da kuma lafiyarsu cikin jituwa da nufin Allah. (Mai-Wa’azi 12:1) Ta yaya za mu iya yin haka? A ina ne za mu iya samun gaba gaɗi da kuma ƙarfin da muke bukata don mu yi haka? Kuma waɗanne zarafin hidima ne muke da shi?

Ɗaukan Matakan da za su Kawo Ci Gaba da Kuma Amfani

3. Waɗanne muhimman matakai ne yin nufin Allah ya ƙunsa?

3 Ga Kiristoci na gaskiya, yin nufin Allah abu ne na har abada. Ana somawa ne da matakai masu muhimmanci kamar su shiga Makarantar Hidima ta Allah, karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana, zuwa wa’azi, har a kai ga yin baftisma. Yayin da ake samun ci gaba, muna bukatar mu tuna kalaman manzo Bulus: “Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin cigabanka ya bayyanu ga kowa.” (1 Timothawus 4:15) Irin wannan ci gaban ba na ɗaukaka kai ba ne, amma yana nuna ƙudurinmu ne na yin nufin Allah babu son kai. Bin irin wannan tafarkin ya nuna cewa mun yarda Allah ya yi mana ja-gora a dukan al’amura na rayuwa, kuma yana yin haka sosai fiye da mu.—Zabura 32:8.

4. Ta yaya za mu iya kawar da damuwa marar amfani?

4 Ja da baya ko kuwa yawan damuwa da kanmu yana iya hana mu samun cin gaba a hidimarmu ga Allah. (Mai-Wa’azi 11:4) Saboda haka, wataƙila muna bukatar mu sha kan damuwarmu tukun kafin mu samu farin ciki na gaske wajen yi wa Allah hidima da wasu. Alal misali, Erik yana tunanin yin hidima a wata ikilisiya da ake yin yaren wata ƙasa. Amma damuwarsa ita ce: ‘Zan dace da su kuwa? Zan so ’yan’uwan? Za su so ni?’ Ya ce: “Daga baya na fahimci cewa ina bukatar in damu da ’yan’uwan sosai fiye da kaina. Na yanke shawarar daina damuwa da waɗannan abubuwan amma in yi iya ƙoƙarina babu son kai. Na yi addu’a don samun taimako kuma na tafi wurin. A yanzu, ina jin daɗin hidimata a wurin sosai.” (Romawa 4:20) Hakika, idan muka yi wa Allah hidima da kuma mutane babu son kai, za mu sami farin ciki da gamsuwa.

5. Me ya sa muke bukatar shiri mai kyau a biɗar nufin Allah? Ka ba da misali.

5 Biɗar nufin Allah yadda ya kamata ya ƙunshi shirya al’amuranmu sosai. Zai dace mu guje wa cin basussukan da za su sa mu zama bayin wannan duniyar kuma su rage damar da muke da ita na yin aikin Allah. Littafi Mai Tsarki ya tuna mana: “Mai-cin bashi kuma bawa ne ga mai-bada bashi.” (Misalai 22:7) Idan muka dogara ga Jehobah kuma muka mai da abubuwa na ruhaniya farko hakan zai taimaka mana mu daidaita al’amura yadda ya kamata. Alal misali, Guoming da ’yan’uwansa mata biyu suna zaune da mamarsu a wani wuri da gidan haya ke da tsada kuma aiki na da wuyan samu. Ta wajen kashe kuɗi yadda ya kamata da kuma rarraba kuɗin da suke kashewa a tsakaninsu, sun ci gaba da samun ainihin abin da suke bukata duk da cewa ba dukansu ke aiki ba. “A wasu lokatai, mu duka ba mu da kuɗin kashewa,” in ji Guoming. “Duk da haka, mun ci gaba da hidimarmu na majagaba kuma muna kula da mamarmu sosai. Muna farin ciki sosai domin mamarmu ba ta son mu bar biɗar abubuwa na ruhaniya domin mu yi mata tanadin abubuwan jin daɗin rayuwa.”—2 Korinthiyawa 12:14; Ibraniyawa 13:5.

6. Wane misali ne ya nuna yadda za mu iya sa rayuwarmu ta jitu da nufin Allah?

6 Idan kana biɗar wani abin duniya sosai, kamar kuɗi ko wani abu dabam, mai da nufin Allah abin farko zai bukaci ka yi canje-canje masu yawa. Ba za a iya yin waɗannan canje-canjen cikin dare ɗaya ba, kuma idan ka yi kuskure wajen yin canjin da farko, hakan ba ya nufin kasawa. Yi la’akari da Koichi, wanda yake ɓata lokaci mai yawa wajen yin nishaɗi. Koichi ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da yake matashi, amma shekaru da yawa, wasan bidiyo ya ɗauke masa hankali. Wata rana Koichi ya tambayi kansa: ‘Wai me nike yi ne? Na riga na wuce ɗan shekara 30, kuma babu wani abu mai ma’ana da nike yi da rayuwata!’ Koichi ya sake soma nazarin da yake yi na Littafi Mai Tsarki kuma ya sami taimako daga ikilisiya. Ko da yake canjin ya zo ne a hankali, bai ja da baya ba. Ta wajen addu’a da kuma ƙarfafa daga wasu, ya sha kan wannan muguwar jaraba. (Luka 11:9) Yanzu Koichi bawa mai hidima ne kuma yana cike da farin ciki.

Ka Kasance da Daidaita

7. Me ya sa muke bukatar mu kasance da daidaita a wajen yin aikin Allah?

7 Biɗar nufin Allah yana bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu. Kada mu keɓe kanmu ko mu nuna ragwanci wajen yin hakan. (Ibraniyawa 6:11, 12) Duk haka, Jehobah ba ya son mu gajiyar da kanmu a zahiri, a tunaninmu, ko kuwa a motsin ranmu. Idan muka yarda cewa ba za mu iya yin aikinsa da na mu ƙarfin ba, hakan zai nuna cewa muna ɗaukaka Allah kuma muna da daidaita. (1 Bitrus 4:11) Jehobah ya yi alkawarin cewa zai ba mu ƙarfin da muke bukata don yin nufinsa, amma bai kamata mu wuce gona da iri ba, ta wajen yin abin da bai ce mu yi ba. (2 Korinthiyawa 4:7) Don ci gaba da bauta wa Allah ba tare da gajiyar da kanmu ba, muna bukatar mu yi amfani da ƙarfinmu a hanya mai kyau.

8. Menene ya faru sa’ad da wata Kirista matashiya ta yi ƙoƙarin ta bauta wa Jehobah yadda ya kamata kuma ta mai da hankali ga neman abin duniya, kuma wane gyara ne ta yi?

8 Alal misali, Ji Hye wadda take zaune a Asiya ta Gabas, ta yi wani aiki mai wuya har tsawon shekara biyu kuma tana majagaba. “Na yi ƙoƙarin na bauta wa Jehobah yadda ya kamata kuma na mai da hankali ga aikina,” in ji ta, “amma barcin awa biyar kawai nike yi daddare. Daga baya, sai na ji cewa ba na jin daɗin abubuwa na ruhaniya.” Domin ta bauta wa Jehobah da ‘dukan zuciyarta, ranta, da dukan azancinta,’ Ji Hye ta nemi aikin da ba zai cinye lokacinta ba. (Markus 12:30) “Duk da matsin da na fuskanta daga iyalina na neman kuɗi, na yi ƙoƙarin mai da nufin Allah abin farko,” in ji ta. “A yanzu ina samun isashen kuɗi na biyan bukatata, kamar su sayen sutura mai kyau. Kuma ina farin ciki domin ina samun isashen barci! Ina jin daɗin hidimata, kuma ruhaniyata ta yi ƙarfi. Hakan ya yiwu ne domin ba ni da lokaci na abubuwan duniya masu jawo hankali da masu ɗauke hankali.”—Mai-Wa’azi 4:6; Matta 6:24, 28-30.

9. Ta yaya ne ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu za su iya shafan mutane a hidima?

9 Ba kowa ba ne zai iya bauta wa Allah a matsayin mai wa’azi na cikakken lokaci ba. Idan kana fama da tsufa, rashin lafiya, da kowace irin kasawa, ka san cewa Jehobah yana farin ciki domin amincinka da kuma hidimar da ka yi da dukan zuciyarka. (Luka 21:2, 3) Saboda haka, kada wani a cikinmu ya raina yadda ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu za su iya shafan wasu ko da kaɗan ne. Alal misali, a ce mun je yin wa’azi a wasu gidaje kuma babu wanda ya saurare mu. Bayan mun tafi, masu gidan suna iya ɗaukan dogon lokaci ko kwanaki suna maganar ziyarar da muka kai, har ma a inda aka ƙi buɗe mana kofa! Mun san cewa ba dukan mutanen da suka saurari bishara ba ne za su zama masu bi, amma wasu za su zama. (Matta 13:19-23) Wasu suna iya sauraronmu sa’ad da yanayi a duniya ko rayuwarsu ya canja. Ko yaya, ta wajen yin iya ƙoƙarinmu a hidimar fage, muna yin aikin Allah. Mu “abokan aiki na Allah ne.”—1 Korinthiyawa 3:9.

10. Waɗanne zarafi ne waɗanda suke cikin ikilisiya suke da shi?

10 Bugu da ƙari, mu duka muna iya taimaka wa iyalanmu da kuma ’yan’uwanmu na ruhaniya maza da mata. (Galatiyawa 6:10) Tasiri mai kyau da muka yi a kan wasu yana iya shafan su sosai kuma har abada. (Mai-Wa’azi 11:1, 6) Sa’ad da dattawa da bayi masu hidima suka yi ayyukansu yadda ya kamata, za su taimaka wa waɗanda suke cikin ikilisiya su kasance da ruhaniya, kuma aikin Kirista zai ƙaru. Muna da tabbaci cewa idan muna da “yawaita cikin aikin Ubangiji,” wahalarmu “ba banza ta ke ba.”—1 Korinthiyawa 15:58.

Biɗar Nufin Allah a Rayuwa

11. Ban da yin aiki tare da ikilisiya, waɗanne zarafi ne kuma za mu iya samu?

11 Mu Kiristoci muna son mu ci gaba da rayuwa, kuma muna son mu ɗaukaka Allah a dukan abubuwan da muke yi. (1 Korinthiyawa 10:31) Idan muka ba da kanmu yadda ya kamata wajen wa’azin bisharar Mulki da kuma koyar da mutane su yi biyayya ga dukan abubuwan da Yesu ya umurta, za mu sami hanyoyi masu yawa na bauta wa Allah da za su sa mu farin ciki. (Matta 24:14; 28:19, 20) Ban da yin aiki tare da ikilisiya, muna iya samun damar yin hidima a inda ake bukatar masu wa’azi, wataƙila a wani yanki, inda ake yin wani harshe, ko a wata ƙasa. Ana iya gayyatar dattawa da bayi masu hidima da suka ƙware waɗanda ba su yi aure ba su halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima, bayan haka su je su yi hidima a ikilisiyoyin da ake bukatar Kiristocin da suka ƙware, wataƙila a ƙasarsu ko a wata ƙasa. Ma’aurata waɗanda suke yin hidima na cikakken lokaci suna iya cancanta su sami koyarwa a makarantar Gilead kuma su yi hidima a ƙasar waje. Kuma ana bukatar waɗanda za su ba da kansu da son rai su yi ayyuka dabam dabam a Bethel da kuma gina da kula da wuraren taro da ofisoshin hidima.

12, 13. (a) Ta yaya za ka iya yanke shawarar irin hidimar da za ka biɗa? (b) Ka kwatanta yadda za a iya yin amfani da aikin da aka riga aka koya a wani wuri.

12 Wace irin hidima ce za ka biɗa? A matsayinka na keɓaɓɓen bawan Jehobah, ka dogara ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa a kowane lokaci don ja-gora. ‘Managarcin ruhunsa’ zai taimaka maka ka yanke shawarar da ta dace. (Nehemiah 9:20) Wani aikin shi ke kai ga wani, kuma abubuwan da aka koya a wani ɓangaren hidima, a yawancin lokaci ana yin amfani da su a wata hidimar.

13 Alal misali, Dennis da matarsa, Jenny, suna taimakawa a kowane lokaci wajen gina Majami’ar Mulki. Bayan ambaliyar Hurricane da aka yi a kudancin Amirka, sun ba da kansu da son rai wajen taimaka wa mabukata. Dennis ya ba da rahato: “Yin amfani da ayyukan da muka koya wajen gina Majami’un Mulki don taimaka wa ’yan’uwanmu ya faranta mana rai sosai. Godiyar da waɗanda muka taimaka ma suka nuna ya sa mu farin ciki sosai. Yawancin sauran rukunonin kai agaji ba su yi nasara ba sosai wajen sake gini. Shaidun Jehobah sun riga sun gyara ko gina fiye da gidaje 5,300 da kuma Majami’un Mulki masu yawa. Mutane sun ga hakan kuma a yanzu suna sha’awar saƙonmu.”

14. Menene za ka iya yi idan kana son ka biɗi hidima na cikakken lokaci?

14 Za ka iya biɗar nufin Allah ta wajen zaɓan aikin hidima na cikakken lokaci? Idan haka ne, za ka sami albarka. Idan yanayinka a yanzu ba zai ƙyale ka ka yi haka ba, wataƙila kana bukatar ka yi wasu canje-canje. Ka yi addu’a kamar yadda Nehemiah ya yi sa’ad da yake son ya je ya yi wani aiki mai muhimmanci: “Ya Ubangiji, ina roƙonka, . . . ka arzutadda bawanka yau, ka yarda kuma ka ba shi jinƙai a wurin mutumin nan.” (Nehemiah 1:11) Bayan ka yi addu’a ga “mai-jin addu’a,” ka aikata daidai da addu’arka. (Zabura 65:2) Kana bukatar ka ɗauki waɗannan matakan idan kana son Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenka na bauta masa sosai. Idan ka yanke shawarar soma hidima na cikakken lokaci, ka manne wa shawararka. Yayin da lokaci ke wucewa, saninka zai ci gaba da ƙaruwa, kuma farin cikinka zai ƙaru.

Rayuwa Mai Amfani Sosai

15. (a) Ta yaya za mu amfana idan muka yi hira da tsofaffin bayin Allah kuma muka karanta labaransu? (b) Ka ambata labari na rayuwa wanda ya ƙarfafa ka?

15 Waɗanne sakamako ne za ka iya samu idan ka biɗi nufin Allah? Ka yi hira da tsofaffin bayin Jehobah, musamman waɗanda suka daɗe sosai a cikin hidima na cikakken lokaci. Suna yin rayuwa mai ma’ana! (Misalai 10:22) Za su gaya maka cewa Jehobah bai taɓa yin watsi da su ba kuma suna samun ainihin abin da suke bukata har ma fiye da haka a lokacin wahala. (Filibbiyawa 4:11-13) Tun daga shekara ta 1955 zuwa 1961, Hasumiyar Tsaro na Turanci ta wallafa labaran rayuwa masu yawa na waɗanda suke da aminci a ƙarƙashin kan bayanin nan “Pursuing My Purpose in Life.” Tun daga wannan lokacin, an wallafa ɗarurruwan labaran rayuwa. Irin waɗannan labaran suna nuna himma da kuma farin ciki irin waɗanda ke cikin Littafi Mai Tsarki a littafin Ayukan Manzanni. Karanta irin waɗannan labaran zai motsa ka ka ce, ‘Wannan ita ce irin rayuwar da nake son na yi!’

16. Me ke sa rayuwar Kirista ta kasance da ma’ana da kuma farin ciki?

16 Aaron, da aka ambata ɗazu ya ce: “A Afirka, ina yawan haɗuwa da matasan da suke tafiya wata ƙasa don biɗar abin duniya. Yawancinsu ba sa samu. Amma, muna yin nufin Allah ta wajen ɗaukaka bisharar Mulki, kuma muna morar rayuwa mai ma’ana da kuma ƙalubale. Mun gani da idanun mu cewa “bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayukan Manzanni 20:35.

17. Me ya sa ya kamata mu ci gaba da biɗar nufin Allah a yanzu?

17 Kai kuma fa? Wace manufa ce kake biɗa? Idan ba ka da makasudin da zai taimaka maka ka biɗi nufin Allah, wasu abubuwan dabam za su cike wannan gurbin. Me zai sa ka ɓata rayuwarka mai ma’ana wajen biɗar abubuwan jin daɗi na wannan duniyar Shaiɗan? Nan ba da daɗewa ba, a lokacin ‘babban tsanani,’ kuɗi da kuma matsayi a wannan duniyar za su zama abin banza. Abin da zai fi muhimmanci a lokacin shi ne dangantakarmu da Jehobah. Za mu yi farin ciki sosai cewa mun yi wa Allah hidima da kuma wasu kuma mun biɗi nufin Allah sosai a rayuwarmu!—Matta 24:21; Ru’ya ta Yohanna 7:14, 15.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

b Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Yaya Jehobah yake ji game da hidimar da muke yi masa?

• Ta yaya ne kasancewa da daidaita da kuma amfani za su taimaka mana mu yi wa Allah da wasu hidima?

• Waɗanne zarafi ne na yin hidima za mu samu?

• Ta yaya za mu iya yin rayuwa mai ma’ana a yanzu?

[Hotuna a shafi na 23]

Muna bukatar daidaita idan muna son mu ci gaba da bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya

[Hotuna a shafi na 24]

Akwai hanyoyi masu yawa da za a iya bauta wa Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba