Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 11/1 pp. 11-15
  • Ka Nuna Bangaskiya Ta Yadda Kake Rayuwarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Nuna Bangaskiya Ta Yadda Kake Rayuwarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙaramar Liyafa
  • Wace Irin Liyafa ce Za a Yi?
  • Ɗaurin Aure da Kuma Liyafa
  • “Uban Biki”
  • Kyautar da Ake Bayarwa a Ranar Aure
  • Yadda Za Ku Shirya Bikin Auren da Zai Ɗaukaka Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Me Ake Yi a Bikin Daurin Auren Shaidun Jehobah?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Aure Mai Daraja A Gaban Allah Da Mutum
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ku Guji Shirya Bikin Aure Irin Na Mutanen Duniya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 11/1 pp. 11-15

Ka Nuna Bangaskiya Ta Yadda Kake Rayuwarka

“Hakanan kuwa bangaskiya, in ba ta da ayuka ba, mataciya ce cikin kanta.”—YAƘUB 2:17.

1. Me ya sa Kiristoci na farko suka mai da hankali ga bangaskiya da ayyuka?

GABAKI ɗayansu, Kiristoci na farko sun nuna bangaskiyarsu ta irin rayuwar da suka yi. Almajiri Yaƙub ya umurci duka Kiristoci: “Ku zama masu-aika magana, ba masu-ji kaɗai ba.” Ya daɗa: “Kamar yadda jiki ba tare da ruhu matace ne, hakanan kuma bangaskiya ba tare da ayyuka mataciya ce.” (Yaƙub 1:22; 2:26) Bayan shekara 35 da rubuta waɗannan kalmomin, yawancin Kiristoci sun ci gaba da nuna bangaskiyarsu da ayyukan da suka dace. Amma abin baƙin ciki shi ne, wasu sun ƙi yin haka. Yesu ya yaba wa ikilisiyar da ke Samiruna; amma ga yawanci da ke ikilisiyar Sardisu, ya ce: “Na san ayukanka, kana da suna mai-rai ne, amma matace ne.”—Ru’ya ta Yohanna 2:8-11; 3:1.

2. Menene ya kamata Kiristoci su tambayi kansu game da bangaskiyarsu?

2 Yesu ya ƙarfafa waɗanda suke Sardisu, da kuma waɗanda za su karanta kalmominsa a nan gaba, su tabbatar da ƙaunarsu ta farko ga gaskiya ta Kirista kuma su kasance a faɗake a ruhaniya. (Ru’ya ta Yohanna 3:2, 3) Ya kamata kowanenmu ya tambayi kansa: ‘Ayyuka na fa? Ayyuka na suna tabbatar da cewa ina da bangaskiya kuma ina iya ƙoƙari na don in nuna bangaskiyata a duka abubuwan da nike yi, har ma a ɓangarorin da ba su shafi aikin wa’azi da taro na ikilisiya kai tsaye ba?’ (Luka 16:10) Za mu iya tattauna fasalolin rayuwa masu yawa, amma yanzu za mu tattauna guda ne kawai: liyafa, har da wanda ake yi bayan ɗaurin aure na Kirista.

Ƙaramar Liyafa

3. Menene ra’ayin Littafi Mai Tsarki game da yin liyafa?

3 Yawancinmu na farin ciki idan aka gayyace mu zuwa liyafa na Kiristoci masu farin ciki. Jehobah “Allah ne mai farin ciki,” wanda yake son bayinsa su kasance masu farin ciki. (1 Timothawus 1:11; NW) Jehobah ya sa Sulemanu ya rubuta wannan gaskiyar a cikin Littafi Mai Tsarki: “Sa’annan na yabi wasa da dariya; gama babu abin da ya fi ma mutum a duniya kamar ya ci, ya sha, ya ji daɗi; shi riƙa yin wannan cikin aikinsa dukan kwanakin ransa.” (Mai-Wa’azi 3:1, 4, 13; 8:15) Irin wannan farin cikin na iya kasancewa a inda iyali take cin abinci ko kuwa a wata ƙaramar liyafa na masu bauta ta gaskiya.—Ayuba 1:4, 5, 18; Luka 10:38-42; 14:12-14.

4. A kan me ya kamata mutumin da ke shirya liyafa ya mai da hankali?

4 Idan kana shirin yin irin wannan liyafar, wanda kai ne ke ɗauke da nauyinsa, ya kamata ka yi tunani sosai game da shirin da kake yi, ko da masu bi kaɗan ne kawai za ka gayyata don ku ci abinci kuma ku yi hira tare. (Romawa 12:13) Za ka so ka ga cewa an yi “abu duka da hankali” bisa “hikima mai-fitowa daga bisa.” (1 Korinthiyawa 14:40; Yaƙub 3:17) Manzo Bulus ya rubuta: “Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah. Kada ku bada sanadin tuntuɓe.” (1 Korinthiyawa 10:31, 32) Waɗanne fasaloli ne suke bukatar a mai da musu hankali sosai? Yin tunani sosai a kan wannan, zai sa ka tabbata cewa abin da kai da baƙinka kuka yi zai bayyana cewa kuna aikata abin da kuka gaskata.—Romawa 12:2.

Wace Irin Liyafa ce Za a Yi?

5. Me ya sa ya kamata mai masaukin baƙi ya yi tunani sosai a kan ko ya kamata ya ba da barasa da kuma sauti?

5 Yawancin masu masaukin baƙi sukan yi tunani ko ya kamata su ba da barasa. Ba dole ba ne a ba da barasa don taron ya zama mai ban ƙarfafa. Ka tuna cewa Yesu ya yi tanadin abinci ga wasu rukunin mutanen da suka zo wurinsa, ya ba su burodi da kifi. Labarin bai ce ya yi tanadin barasa ba, ko da yake mun san cewa zai iya yin haka. (Matta 14:14-21) Idan kana son ka ba da barasa a wurin liyafa, ka yi haka daidai kima, kuma ka tabbata cewa akwai wasu kayan sha domin waɗanda ba sa shan giya. (1 Timothawus 3:2, 3, 8; 5:23; 1 Bitrus 4:3) Kada ka sa wani ya ji cewa an tilasta masa ya sha abin da zai sare shi “kamar maciji.” (Misalai 23:29-32) Sauti ko yin waƙa fa? Idan liyafar za ta haɗa da sauti, babu shakka za ka zaɓi waƙoƙi, kuma za ka mai da hankali ga launi da kuma kalmomin waƙar. (Kolossiyawa 3:8; Yaƙub 1:21) Yawancin Kiristoci sun ga cewa saka Waƙoƙin Mulki ko kuwa yin irin waɗannan waƙoƙin tare na daɗaɗawa. (Afisawa 5:19, 20) Kuma ka dinga duba ƙarfin muryar a kai a kai domin kada waƙar ta hana hira mai daɗi da ake yi, kuma kada ta dami maƙwabta.—Matta 7:12.

6. Ta yaya ne mai masaukin zai iya nuna cewa bangaskiyarsa rayayya ce, game da hira ko kuwa wasu ayyuka?

6 A wurin liyafa, Kiristoci na iya tattauna abubuwa dabam dabam, su karanta wasu littattafai, ko kuwa su ba da labarai masu daɗi. Idan hirar ta kauce daga mizanai na Kirista, mai masaukin baƙin na iya mayar da su kan hanya cikin dabara. Kuma ya lura sosai don kada mutum ɗaya ya sha kan hirar da ake yi. Idan ya lura cewa hakan na faruwa, yana iya yin magana don ya jawo wasu cikin hirar, wataƙila yana iya jawo matasan don su ma su yi magana, ko kuwa yana iya gabatar da wani batu da zai sa mutane su yi kalamai dabam dabam. Matasa da tsofaffi za su ji daɗin irin wannan liyafar. Idan a matsayinka na wanda ya tsara liyafar, ka bi da abubuwa yadda ya kamata kuma cikin dabara, ‘jimirinka zai sanu’ ga waɗanda suka hallara. (Filibbiyawa 4:5) Za su fahimci cewa bangaskiyarka rayayya ce, wadda ta shafi dukan fasalolin rayuwarka.

Ɗaurin Aure da Kuma Liyafa

7. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali ga shirin ɗaurin aure da kuma liyafa?

7 Wani lokaci na musamman na farin ciki shi ne ɗaurin aure na Kirista. Bayin Allah na dā, tare da Yesu da almajiransa sun halarci irin wannan bikin da kuma liyafar. (Farawa 29:21, 22; Yohanna 2:1, 2) A baya bayan nan, labarin da ake ji ya nuna cewa shirya liyafar ɗaurin aure na bukatar ƙoƙari sosai idan ana son ya yi kyau, kuma ya kasance da daidaituwa na Kirista. Duk da haka, waɗannan fasaloli ne na rayuwa, da suke ba Kirista damar nuna bangaskiyarsa.

8, 9. Ta yaya ne abubuwan da ake yi a yawancin aure suke nuna abin da muka karanta a 1 Yohanna 2:16, 17?

8 Yawancin mutanen da ba su san mizanan Allah, ko kuwa ba su damu da shi ba, sun ɗauki ɗaurin aure inda ake wuce gona da iri. A wata jarida ta ƙasar Turai, wata amarya ta faɗi waɗannan kalaman game da “babban bikin” auren da ta yi: ‘Mun shiga wata ƙaramar motar katako da dawakai huɗu suke ja, a bayanmu kuma akwai wata motar da dawakai sha biyu suke ja, wadda take ɗauke da mawaƙa. Bayan haka, mun ci haɗaɗɗen abinci ga kuma waƙa mai daɗi, kai abin da ban sha’awa. A ranar ni sarauniya ce.’

9 Ko da yake al’adu sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, waɗannan kalaman sun nuna abin da manzo Yohanna ya rubuta: “Dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.” Ka yi tunanin ƙwararrun ma’aurata Kiristoci da suke son su yi “babban” ɗaurin aure tare da liyafa mai girma. Maimakon haka, ya kamata tsarinsu ya nuna cewa sun bi shawarar da ta ce “wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 Yohanna 2:16, 17.

10. (a) Me ya sa shiri ke da muhimmanci idan ana son ɗaurin aure ya yi kyau? (b) Ta yaya za a yanke shawara game da waɗanda za a gayyata?

10 Ya kamata Kiristoci ma’aurata su kasance da daidaituwa, kuma Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka musu. Ko da yake ranar ɗaurin aure na da muhimmanci, sun san cewa wannan soma taɓi ne na rayuwar aure na Kiristoci biyu da suke da begen rai madawwami. Ba sa bukatar su yi babban bikin aure. Idan suka zaɓi su yi liyafa, ya kamata su lissafa kuɗin da za su kashe da kuma irin liyafar da za su yi. (Luka 14:28) A rayuwarsu ta Kirista, mijin ne shugaba bisa ga Nassi. (1 Korinthiyawa 11:3; Afisawa 5:22, 23) Saboda haka, angon ne ke da hakkin liyafar auren. Ya kamata angon ya tattauna da matar da zai aura batutuwa kamar wanda suke so ko kuwa waɗanda za su iya gayyata zuwa bikin auren. Ba zai yiwu ba su gayyaci duka abokansu ko ’yan’uwa; saboda haka, za su yanke shawarar da ya kamata. Ya kamata ma’auratan su tabbata cewa idan ba su gayyaci wasu ’yan’uwa Kiristoci ba, hakan ba zai ba ’yan’uwan haushi ba.—Mai-Wa’azi 7:9.

“Uban Biki”

11. Menene matsayin “uban biki” a wurin ɗaurin aure?

11 Idan ma’auratan suka zaɓi su yi liyafa don ɗaurin aurensu, ta yaya za su tabbata cewa wannan taron ya kasance da daraja? Tun shekaru da yawa, Shaidun Jehobah sun fahimci muhimmancin sanya sashen nan da aka ambata a liyafar da Yesu ya halarta a Kana. Akwai “uban biki,” wanda mai bi ne da ya san abin da ya dace. (Yohanna 2:9, 10) Hakazalika, ango mai hikima zai zaɓi ɗan’uwa Kirista wanda ya ƙware a ruhaniya don wannan aiki mai muhimmanci. Da yake angon ya gaya masa abin da yake so, uban bikin zai iya bin umurnin da aka ba shi kafin da kuma lokacin bikin.

12. Menene angon ya kamata ya yi la’akari da shi game da yin amfani da barasa?

12 Daidai da abin da aka tattauna a sakin layi na 5, wasu ma’aurata ba sa ba da barasa a wajen liyafar aurensu domin kada a sha a yi maye kuma a ɓata farin ciki da nasarar bikin. (Romawa 13:13; 1 Korinthiyawa 5:11) Duk da haka, idan za su ba da barasa, ya kamata angon ya tabbatar da cewa an yi haka daidai kima. Akwai barasa a ɗaurin auren da Yesu ya halarta a Kana, kuma ya yi tanadin barasa mai kyaun gaske. Abin sha’awa shi ne furcin da uban bikin ya yi: “Kowane mutum ya kan fara sanya ruwan anab mai-kyau; sa’anda mutane sun sha dayawa, daga baya abin da ba ya yi ya shi kyau ba: amma kai ka ajiye ruwan mai-kyau har yanzu.” (Yohanna 2:10) Hakika, Yesu bai ƙarfafa yin maye ba, domin hakan ba shi da kyau. (Luka 12:45, 46) Sa’ad da yake bayyana mamakinsa domin kyaun barasar, uban bikin ya bayyana sarai cewa, ya lura akwai waɗanda aka gayyata zuwa wurin bikin aure da suka yi maye. (Ayukan Manzanni 2:15; 1 Tassalunikawa 5:7) Saboda haka, ya kamata angon da kuma tabbataccen Kirista da ya zaɓa ya zama uban biki su tabbatar da cewa duka waɗanda suka hallara sun bi wannan umurnin: “Kada ku yi maye da ruwan anab kuma-cikinsa da hauka.”—Afisawa 5:18; Misalai 20:1; Hosea 4:11.

13. Menene ya kamata ma’aurata su yi la’akari da shi idan suna son a saka sauti a liyafar aurensu, kuma don me?

13 Kamar sauran liyafar da ake yi, idan akwai sauti, ya kamata a mai da hankali sosai ga muryar saboda mutane su ji hirar da suke yi. Wani Kirista dattijo ya ce: “Yayin da yamma ta yi, sa’ad da ake jin daɗin hira ko sa’ad da aka soma rawa, muryar sautin na ƙaruwa. Muryar da aka rage a dā na iya ƙaruwa kuma za ta iya hana hirar da ake yi. Liyafar aure na ba da dama na yin tarayya mai kyau. Zai zama abin baƙin ciki idan sauti mai ƙara ya ɓata wannan dama!” A nan ma, angon da uban bikin na bukatar su aikata yadda ya kamata, kada su ƙyale hakkin lura da irin waƙa da kuma muryar sautin ga masu kula da sautin har da mawaƙan da suka ɗauko. Bulus ya rubuta: “Iyakar abin da ku ke yi kuma, cikin magana da aiki, ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu.” (Kolossiyawa 3:17) Sa’ad da baƙin suka koma gida bayan liyafar auren, za su tuna cewa waƙar na nuna cewa ma’auratan suna yin komi a cikin sunan Yesu? Ya kamata ya zama haka.

14. Menene ya kamata Kiristoci su tuna game da aure?

14 Hakika, mutane za su yi farin cikin tunawa da ɗaurin auren da aka tsara sosai. Adam da Edyta da suka yi aure shekara 30 da ta shige, sun yi kalami a kan wani ɗaurin aure: “Za ka san cewa Kiristoci ne ke wurin. Akwai waƙoƙin yabo ga Jehobah da kuma nishaɗi mai daɗi. Rawa da waƙa ba su ne suka fi muhimmanci ba. Liyafar tana da daɗi da kuma ban ƙarfafa, kuma an yi komi cikin jituwa da mizanan Littafi Mai Tsarki.” Babu shakka, akwai abubuwa masu yawa waɗanda amarya da ango za su yi da zai nuna cewa suna da bangaskiya.

Kyautar da Ake Bayarwa a Ranar Aure

15. Wace shawara ce na Littafi Mai Tsarki za a iya amfani da ita game da kyautar da ake bayarwa a wurin aure?

15 A yawancin kasashe, abokai da ’yan’uwa suna ba da kyauta ga waɗanda suke aure. Idan kana son ka yi haka, menene ya kamata ka sa a zuciya? Ka tuna abin da manzo Yohanna ya ce game da “darajar rai ta wofi.” Ya haɗa irin wannan wofin da ‘duniyar da ke wucewa,’ ba da Kiristocin da suke nuna bangaskiyarsu ta ayyuka ba. (1 Yohanna 2:16, 17) Bisa ga hurarren bayanin Yohanna, ya kamata amarya da angon su ambata sunan mutanen da suka ba su kyauta? Kiristocin da suke Makidoniya da Akaya sun ba da kyauta ga Kiristocin da suke Urushalima, amma babu alamar da ta nuna cewa an ambata sunayensu. (Romawa 15:26) Yawancin Kiristocin da suke ba da kyauta a wurin ɗaurin aure ba za su so a ambata sunansu ba don kada su jawo hankali ga kansu. Game da wannan, ka duba shawarar Yesu da ke Matta 6:1-4.

16. Ta yaya ne sababbin ma’aurata za su kauce wa kunyatar da wasu game da kyauta na aure?

16 Faɗin sunayen waɗanda suka ba da kyauta na iya jawo “cakuna” game da wanda ya fi kyau ko kuwa wanda ya fi tsada. Da haka, Kiristoci amarya da ango masu hikima za su guje wa faɗin sunayen waɗanda suka ba da kyauta. Faɗin sunayen waɗanda suka ba da kyauta a fili na iya kunyatar da waɗanda suka kasa ba da kyauta. (Galatiyawa 5:26; 6:10) Ba laifi ba ne amarya da ango su san sunayen waɗanda suka ba su kyauta. Suna iya yin haka daga takardar da aka liƙa a jikin kyautar, amma ba wai a karanta shi a fili ba. Sa’ad da muke saye, da bayar, da kuma karɓar kyautar aure, dukanmu na da damar nuna cewa, har ma a batu na sirri, bangaskiyarmu na shafar ayyukanmu.

17. Wane makasudi ne ya kamata Kiristoci su kasance da shi game da bangaskiyarsu da ayyukansu?

17 Nuna bangaskiyarmu ya ƙunshi fiye da kasancewa da ɗabi’a mai kyau, zuwa taron Kirista, da kuma saka hannu a aikin wa’azi. Bari dukanmu mu kasance da rayayyiyar bangaskiya da za ta shafi dukan abin da muke yi. Hakika, za mu iya nuna bangaskiyarmu ta wurin ‘cikakken’ ayyuka, tare da waɗanda aka ambata a baya.—Ru’ya ta Yohanna 3:2.

18. Ta yaya ne kalmomin da ke Yohanna 13:17 za su iya zama gaskiya game da auren Kirista da kuma liyafa?

18 Bayan Yesu ya kafa misali mai kyau ga manzanninsa masu aminci ta wajen wanke ƙafafuwansu cikin tawali’u, ya ce: “Idan kun san waɗannan abu, masu-albarka ne idan kun yi su.” (Yohanna 13:4-17) A wuraren da muke da zama, wataƙila ba zai yiwu ko kuwa ba a wanke ƙafar wani, kamar baƙon da muka yi. Amma, kamar yadda muka tattauna a cikin wannan talifin, akwai wasu fasaloli na rayuwa da za mu iya nuna bangaskiyarmu ta wajen ƙauna, yin la’akari, har da waɗanda suka haɗa da liyafa da kuma auren Kirista. Haka yake ko da mu ne ke aure ko an gayyace mu, ko kuwa a wata liyafa na Kiristocin da suke son su nuna bangaskiyarsu ta wajen ayyuka.

Yaya Za Ka Amsa?

Ta yaya za ka iya nuna bangaskiyarka

• sa’ad da kake shirya liyafa?

• sa’ad da kake shirin ɗaurin aure ko kuwa liyafar aure?

• sa’ad da kake bayar ko karɓar kyautar aure?

[Hoto a shafi na 12]

Ko da mutane kaɗan ne kawai ka gayyata, bari “hikima mai-fitowa daga bisa” ta yi maka ja-gora

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba