Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 11/1 pp. 3-5
  • Tabbatacciyar Shawara Domin Renon Yara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tabbatacciyar Shawara Domin Renon Yara
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance Tare da Yaranka
  • Ka Koya Masu Halin Kirki
  • Ka Kasance da Daidaituwa
  • Albarka Daga Tabbatacciyar Shawara
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 11/1 pp. 3-5

Tabbatacciyar Shawara Domin Renon Yara

GAME da cikinta na fari, Ruth ta ce: “Sa’ad da nike ’yar shekara 19, ina zaune nesa da iyayena, kuma ban yi shirin ɗaukan ciki ba.” Da yake ita yarinya ce, ba ta yi tunanin zama uwa ba. Ina za ta sami tabbatacciyar shawara?

A wata sassa kuma, Jan mai yara biyu, ya ce: “Da farko ina da gaba gaɗi. Amma daga baya na fahimci cewa ba ni da ilimi a wannan fannin.” Da yake iyaye ba su san hanya mafi muhimmanci ta renon yara ba, a ina ne za su sami taimako na renon ’ya’yansu?

A yau, iyaye da yawa suna bincika Intane. Za ka iya yin tunani, wataƙila shawarar da suke samu tabbatacciya ce. Yana da kyau ka mai da hankali sosai. Ka san wanda yake ba ka shawara a cikin Intane ne? Sun ci nasara ne a renon ’ya’yansu? Babu shakka, kana mai da hankali game da al’amuran da suka shafi iyalinka. A wani lokaci, shawara daga gwanaye tana kashe gwiwa. Saboda haka, a ina za ka iya samun tabbatacciyar shawara?

Jehobah Allah, Wanda ya kafa iyali, shi ne Tushe mafi kyau na shawarar da ta dace ta renon yara. (Afisawa 3:15) Shi ne ainihin gwani. A cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ya ba da tabbatacciyar umurni mai amfani. (Zabura 32:8; Ishaya 48:17, 18) Hakkinmu ne mu yi amfani da shi.

An tambayi ma’aurata su faɗi abin da suka koya sa’ad da suka yi renon ’ya’yansu domin su zama daidaitattu da kuma masu tsoron Allah. Sun ce, ainihin abin da ya taimake su shi ne bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Sun fahimci cewa a yau shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki tabbatacciya ce, kamar yadda take sa’ad da aka rubuta Littafi Mai Tsarki.

Ka Kasance Tare da Yaranka

Sa’ad da aka tambayi Catherine mai yara biyu, shawarar da ta taimake ta, nan take ta ambaci Kubawar Shari’a 6:7. Ayar ta ce: “Za ka koya [mizanan Littafi Mai Tsarki] ma ’ya’yanka su da anniya, za ka riƙa faɗinsu sa’anda kana zaune cikin gidanka, da sa’anda ka ke tafiya a kan hanya, da sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi.” Catherine ta fahimci cewa idan tana son ta bi wannan umurnin, dole ne ta kasance tare da ’ya’yanta.

Wataƙila kana iya cewa, ‘yin haka ba shi da sauƙi.’ A lokacin da iyaye suke aiki domin su biya bukatun iyalinsu, ta yaya ne za su iya kasancewa tare da ’ya’yansu? Wani mutum mai suna Torlief wanda yanzu yaronsa yana da na sa iyalin, ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne a bi shawarar da ke cikin Kubawar Shari’a. Ka tafi da yaranka duk inda za ka, da haka, za ku sami zarafin tattaunawa tare. Torlief ya ce: “Ni da ɗana muna aikace-aikacen gida tare, ina yin tafiya tare da iyalina. Kuma muna cin abinci tare.” A sakamakon haka, ya ce, “koyaushe yaronmu yana son ya furta abin da ke zuciyarsa.”

Me zai faru idan akwai rashin sadarwa ko kuma ba a tattaunawa tare? Wannan zai iya faruwa sa’ad da yaran sun girma. Har ila, kasancewa tare da su sosai zai taimake su. Ken maigidan Catherine ya tuna cewa sa’ad da ɗiyarsu ta zama budurwa, ta yi kukan cewa ba ya sauraron ta. Wannan ba sabon abu ba ne daga matasa. Menene zai yi? Ken ya ce: “Sai na kasance tare da ita mu biyu kawai, muna tattauna abin da ke cikin zuciyarta da kuma abin da yake sa ta baƙin ciki. Wannan ya taimaka sosai.” (Misalai 20:5) Ken ya tabbata cewa dalilin da ya sa wannan ya taimaka shi ne, sun saba tattaunawa tare a gidansu. Ya ce: “Da ni da ɗiyata muna da dangantaka mai kyau, shi ya sa take son yin magana da ni.”

Abin farin ciki shi ne, wani bincike da aka yi a kwanan baya ya ba da rahoto cewa, matasa sun fi faɗin cewa iyaye da yara ba sa samun isashen lokaci na kasancewa tare. Me ya sa ba za ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki ba? Ka kasance tare da yaranka sosai, wato, a lokacin da ka ke hutawa, a wurin aiki, a gida, sa’ad da kake yin tafiya, da safe sa’ad da ka tashi da kuma daddare kafin ka yi barci. Idan zai yiwu, ka kai su duk inda za ka. Kamar yadda Kubawar Shari’a 6:7 ta ce, babu abin da ya fi kasancewa tare da ’ya’yanka muhimmanci.

Ka Koya Masu Halin Kirki

Mario, lauya ne kuma yana da yara biyu, ya ce: “Ka nuna wa yara kana ƙaunarsu, kuma ka yi masu karatu.” Amma, wannan ba batun motsa tunanin yaranka ba ne kawai. Ya kamata ka koya masu yadda za su san abin da ke da kyau da marar kyau. Mario ya daɗa cewa: “Ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su.”

Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi iyaye cewa: “Kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) A yawancin gidaje a yau, ba a ba da umurni game da ɗabi’a. Wasu sun yarda cewa ya kamata a bar yara su zaɓi irin ɗabi’ar da za su bi idan sun girma. Ka yarda da wannan? Kamar yadda jikin yaro yake bukatar abinci mai gina jiki don ya sami ƙarfi da kuma lafiya, haka ma zuciyarsa take bukatar umurni. Idan yaranka ba su koyi ɗabi’a mai kyau ba a gida, suna iya bin ra’ayin abokansu a makaranta da kuma malamansu ko ta hanyar watsa labarai.

Littafi Mai Tsarki zai taimaki iyaye su koya wa yaransu yadda za su bambanta abu mai kyau da marar kyau. (2 Timothawus 3:16, 17) Wani ƙwararren dattijo Kirista mai suna Jeff, wanda ya yi renon yara biyu ya ce, Littafi Mai Tsarki ne ya kamata a yi amfani da shi wajen koya wa yara halin kirki. Ya ce: “Yin amfani da Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa yara su fahimci ra’ayin Mahalicci game da abubuwa, ba na iyayensu kaɗai ba. Mun fahimci cewa Littafi Mai Tsarki yana shafar zuciya sosai. Idan muna son mu gyara mugun hali ko tunani, muna ɗaukan lokaci mu nemi nassin da ta tattauna matsalar. Bayan haka, sai mu kai yaron inda ba kowa kuma mu ce masa ya karanta nassin. Sau da yawa yaron zai soma kuka idan ya gama karatun. Hakan na ba mu mamaki. Littafi Mai Tsarki yana shafar su sosai fiye da duk wani abin da muke son mu faɗa ko mu yi.”

Ibraniyawa 4:12 ta bayyana: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa . . . tana kuwa da hamzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” Hakika, saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba ra’ayin mutanen da Allah ya yi amfanin da su su rubuta Littafi Mai Tsarki ba ne. Amma, yana ɗauke ne da ra’ayin Allah game da ayyuka na ɗabi’a. Wannan ya bambanta shi daga duka sauran shawarwari. Idan ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki a wajen koya wa yaranka, kana taimaka musu su kasance da ra’ayin Allah game da al’amura. Koyarwar ka za ta shafe su sosai, kuma kana da zarafin motsa zuciyar yaranka.

Catherine da aka ambata a baya, ta yarda da waɗannan kalaman. Ta ce: “Idan yanayin ya yi tsanani, muna neman shawara daga Kalmar Allah, kuma muna yin nasara!” Za ka iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki sosai a wajen koya wa yaranka yadda za su san abin da ke da kyau da marar kyau?

Ka Kasance da Daidaituwa

Manzo Bulus ya ambata wata ƙa’ida mai muhimmanci da za ta taimaka wajen renon yara. Ya aririce ’yan’uwa Kiristoci: “Ku bari jimrewarku [ko daidaituwa] ta sanu ga dukan mutane.” (Filibbiyawa 4:5) Hakika, wannan ya ƙunshi barin yaranmu su yi koyi da halinmu na daidaitawa. Ka tuna, daidaituwa tana nuna “hikima mai-fitowa daga bisa.”—Yaƙub 3:17.

Ta yaya ne daidaituwa ke da nasaba da koyar da ’ya’yanmu? Sa’ad da muke taimakonsu, kada mu nuna iko ga dukan abubuwan da suke aikatawa. Alal misali, Mario da aka ambata a baya yana ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah, kuma ya ce: “A kowane lokaci muna ƙarfafa yaranmu su yi baftisma, su yi hidima ta cikakken lokaci, da kuma waɗansu makasudai na ruhaniya. Amma muna fahimtar da su cewa zaɓin na su ne idan lokaci ya kai.” Menene sakamakon? Yanzu yaransu suna hidima ta cikakken lokaci.

Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi ubanni a Kolossiyawa 3:21: “Kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna, domin kada ransu ya yi suwu.” Catherine tana daraja wannan ayar. Idan iyaye ba sa haƙuri, hakan zai sa su jin haushi da sauri. Amma ta ce, “kada ka bukaci abubuwa da yawa daga wajen yaranka kamar yadda kai za ka iya yi.” Catherine Mashaidiyar Jehobah ce, kuma ta ce: “Ka mai da bautar Jehobah ya kasance da daɗi.”

Jeff da aka ambata a baya, ya ce: “Sa’ad da yaranmu suka girma, wani abokinmu na kud da kud ya gaya mana cewa a yawancin lokaci ba ya amincewa da abin da yaransa suke bukata. Wannan yana sa su baƙin ciki, yakan sa su ji kamar ana zaluntarsu. Domin guje wa yin haka, ya ba mu shawarar mu nemi hanyoyin da za mu yarda da roƙonsu.”

“Mun ga cewa wannan shawarar tana da kyau,” in ji Jeff. “Sai muka nemi zarafin da za mu amince wa yaranmu su yi abubuwa tare da wasu. Sai mu ce masu ‘Kun san cewa wāne yana yin abu kaza? Me ya sa kuma ba za ku je ba?’ Ko kuma idan yaran suka ce mu kai su wani wuri, za mu yi ƙoƙari mu kai su ko da mun gaji. Muna yin haka ne don kada mu ce a’a.” Wannan shi ne ainihin nuna daidaituwa, wato, ban da son kai, ba tare da taka mizanan da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba.

Albarka Daga Tabbatacciyar Shawara

Yawancin waɗannan ma’auratan sun zama kakanni yanzu. Suna farin cikin ganin cewa waɗannan ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki suna taimaka wa ’ya’yansu su yi nasara a matsayin iyaye. Za ka iya amfana daga shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

Sa’ad da Ruth da aka ambata a baya ta zama uwa, a wani lokacin ita da maigidanta sukan yi baƙin ciki domin babu mai ba su shawara. Amma ba haka ba ne, da shawara mafi kyau da ke cikin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah sun buga littattafan nazari masu kyau da za su taimaki iyaye. Waɗannan sun ƙunshi littattafai kamar su Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, Litafi Na na Labarun Bible, Questions Young People Ask—Answers That Work, The Greatest Man Who Ever Lived. Torlief maigidan Ruth, ya ce: “A yau akwai shawara masu yawa daga Littafi Mai Tsarki ga iyaye. Idan suka yi amfani da shi, zai taimake su su yi renon ’ya’yansu a duka fasaloli na rayuwa.”

[Box/Hoto a shafi na 4]

Abin da GWANAYE da . . . Kuma LITTAFI MAI TSARKI Suka ce

Game da Nuna Ƙauna:

A cikin littafinsa mai suna The Psychological Care of Infant and Child (a shekara ta 1928), Dakta John Broadus Watson ya aririce iyaye: “Kada ku rungumi ko kuma ku sumbaci” ’ya’yanku. “Kada ka bari su zauna a kan cinyarka.” A kwanan baya, Dakta Vera Lane da Dorothy Molneaux sun bayyana a jaridar Our Children (na Mayu a shekara ta 1999) cewa: “Bincike ya nuna cewa yaran da ba a taɓawa da kuma waɗanda ba a nuna wa ƙauna ba sa samun koshin lafiya.”

Akasarin haka, Ishaya 66:12 ta ce Allah yana nuna ƙauna ga mutanensa kamar yadda iyaye suke yi. Hakazalika, sa’ad da almajiran Yesu suka yi ƙoƙari su hana mutane su kawo ’ya’yansu wurin Yesu, ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni.” Sai “ya rungume su, ya sa masu albarka.”—Markus 10:14, 16.

Game da Koyar da Halin Kirki:

A cikin talifin New York Times Magazine na shekara ta 1969, Dakta Bruno Bettelheim ya nanata cewa yaro “yana da ’yancin ya yi abin da yake so, ba saboda yawan [maganar iyayensa] ba, amma domin abin da ya fuskanta a rayuwa.” Bayan shekara 30, Dakta Robert Coles, wanda ya rubuta littafin nan mai suna The Moral Intelligence of Children (a shekara ta 1997), ya ce: “Yara suna bukatar a nuna cewa an damu da su kuma a ja-gorance halayensu” wanda iyayensu da sauran mutane suka amince da shi.

Misalai 22:6 ta aririce iyaye: “Ka goyi yaro cikin hanya da za shi bi, ko lokacin da ya tsufa ba za ya rabu da ita ba.” Kalmar Ibrananci da aka fassara “goyi” tana nufin “soma,” kuma wannan yana nufin soma koyar da yara tun suna jarirai. An aririce iyaye su soma koya wa ’ya’yansu halin kirki tun suna jarirai. (2 Timothawus 3:14, 15) Za su riƙa tunawa da abin da suka koya a waɗannan shekarun.

Game da Horo:

Dakta James Dobson ya rubuta a littafinsa The Strong-Willed Child (a shekara ta 1978) cewa: “Idan iyaye masu ƙauna suka bugi yaro, wannan tarbiyya ce da ke kawar da mugun hali.” A wata sassa, a cikin talifin da aka ɗauko daga littafi na bakwai na Baby and Child Care, Dakta Benjamin Spock (a shekara ta 1998) ya ce: “Bugu yana koya wa yara cewa babban mutum yana da iko ya yi abin da yake so, ko yana da gaskiya ko ba shi da ita.”

Littafi Mai Tsarki ya ce iyaye su yi wa yaro horo a hanyar da ta dace. Misalai 29:15 ta ce: “Sanda da tsautawa suna bada hikima.” Duk da haka, ba dukan yara ba ne suke bukatar dukā. Misalai 17:10 ta ce: “Tsautawa ta fi shiga ma mai-fahimi Da bulala ɗari wurin wawa.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba