“Ku Bar Roƙe Roƙenku Su Sanu Ga Allah”
“Cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.”—FILIBBIYAWA 4:6.
1. Da wa muke da gatar yin magana, me ya sa hakan yake da ban al’ajabi?
IDAN ka ce kana son ka yi magana da shugaban ƙasarku, wace irin amsa za ka samu? Wani ne zai zo ya yi maka magana, amma da kyar ne a yarda ka yi magana da shi. Amma, yanayin ya bambanta wurin Jehobah Allah, Sarki mafi girma da kuma Mamallakin sararin samaniya. Muna iya yi masa magana a ko’ina muke kuma a kowane lokaci da muke so. Koyaushe yana saurarar addu’o’i masu kyau. (Misalai 15:29) Wannan abin ban al’ajabi ne! Ya kamata godiya don wannan ya motsa mu mu yi addu’a a kai a kai ga Wanda ya dace a kira shi “Mai-Jin addu’a.”—Zabura 65:2.
2. Menene ake bukata don Allah ya karɓi addu’o’inmu?
2 Amma, wani zai iya tambaya, ‘Waɗanne addu’o’i ne Allah yake karɓa?’ Littafi Mai Tsarki ya ba da bayanin wani abu da yake da muhimmanci don a saurari addu’a sa’ad da ya ce: “Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Hakika, yadda aka bayana a talifin da ya gabata, muna bukatar bangaskiya don mu yi wa Allah addu’a. Allah yana shirye ya saurari addu’o’in waɗanda suke magana da shi, amma dole ne su yi hakan cikin bangaskiya da yin ayyuka masu kyau da gaske da zuciyar kirki.
3. (a) Kamar yadda addu’o’in bayi masu aminci na dā ya nuna, waɗanne abubuwa ne za mu iya haɗa cikin addu’o’inmu? (b) Waɗanne irin addu’o’i ne za mu iya yi?
3 Manzo Bulus ya aririce Kiristoci a zamaninsa: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.” (Filibbiyawa 4:6, 7) Littafi Mai Tsarki na ɗauke da misalai da yawa na waɗanda suka yi wa Allah addu’a don damuwarsu. Hannatu, Iliya, Hezekiya, da Daniel suna cikin irin waɗannan mutanen. (1 Samuila 2:1-10; 1 Sarakuna 18:36, 37; 2 Sarakuna 19:15-19; Daniel 9:3-21) Ya kamata mu bi misalinsu. Ka lura kuma cewa kalmomin Bulus sun nuna za a iya yin addu’o’i iri dabam dabam. Ya ambata yin godiya, wato, za mu yi wa Allah addu’a muna godiya don abin da ya yi mana. Muna iya yabonsa sa’ad da muke hakan. Roƙo addu’a ne da ake yi da tawali’u cikin rinjaya ta ƙwarai. Kuma muna iya yin addu’a ko kuma mu roƙi wani abu na ainihi. (Luka 11:2, 3) Ubanmu na samaniya yana farin ciki mu yi magana da shi ta waɗannan hanyoyin.
4. Ko da Jehobah ya san bukatunmu, me ya sa har ila muna roƙonsa?
4 Wasu suna iya cewa, ‘Ai, Jehobah ya riga ya san dukan bukatunmu.’ Wannan gaskiya ne. (Matta 6:8, 32) To, me ya sa har ila yake so mu gaya masa damuwarmu? Ka yi la’akari da wannan misalin: Mai kanti yana iya ba wa wasu masu yi masa ciniki kyauta. Amma, don su sami wannan kyautar, dole ne masu cinikin su zo wurin mai kantin su karɓa. Waɗanda ba sa son su yi hakan suna nuna cewa ba sa son kyautar. Hakanan ma, idan ba mu faɗi damuwarmu ta yin addu’a ba, muna nuna cewa ba ma godiya don abin da Jehobah ya yi tanadinsa. Yesu ya ce: “Ku yi roƙo, za ku karɓa.” (Yohanna 16:24) Ta haka, muna nuna cewa mun dogara ga Allah.
Yaya Ya Kamata Mu Yi Magana da Allah?
5. Me ya sa muke bukatar mu yi addu’a cikin sunan Yesu?
5 Jehobah bai kafa dokoki da yawa a kan yadda za a yi addu’a ba. Duk da haka, muna bukatar mu koyi yadda ya dace a yi wa Allah addu’a, kamar yadda aka bayana a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Yesu ya koya wa mabiyansa cewa: ‘Idan kun roƙi komi ga Uba, za ya ba ku a cikin sunana.’ (Yohanna 16:23) Shi ya sa muke bukatar mu yi addu’a cikin sunan Yesu, mu fahimci cewa ta wurin Yesu ne kaɗai dukan ’yan adam za su sami albarkar Allah.
6. Sa’ad da muke addu’a, wane matsayi ya kamata mu kasance a ciki?
6 Wane matsayi ne ya kamata mu kasance a ciki sa’ad da muke addu’a? Ba a ambata wani matsayi da za mu kasance a ciki ba a Littafi Mai Tsarki don a ji addu’o’inmu. (Sarakuna 8:22; Nehemiah 8:6; Markus 11:25; Luka 22:41) Abin da yake da muhimmanci shi ne a yi wa Allah addu’a cikin gaskiya da zuciyar kirki.—Joel 2:12, 13.
7. (a) Menene ma’anar kalmar nan “amin”? (b) Ta yaya ake amfani da shi yadda ya dace sa’ad da ake addu’o’i?
7 Yin amfani da kalmar nan “amin” fa? Nassosi sun nuna cewa wannan kammalawa ne da ya dace sa’ad da muka yi addu’a, musamman addu’a na jama’a. (Zabura 72:19; 89:52) Kalmar nan ‘amin’ a Ibrananci tana nufin “hakika.” Littafi na McClintock and Strong Cyclopedia ya yi bayani cewa muhimmancin faɗan “Amin” a ƙarshen addu’a shi ne a “tabbatar da kalmomin da aka faɗa, kuma a gaskata cewa za su cika.” Da haka, ta wajen kammalawa da kalmar nan “Amin,” wanda ya yi addu’a ya nuna yadda yake ji da gaske game da abin da ya faɗa. Sa’ad da Kirista wanda yake addu’a a madadin ikilisiya ya kammala da wannan furcin, waɗanda suke saurarawa suna iya faɗan “Amin” a zuciyarsu ko kuma da murya don su nuna sun yarda da abin da aka faɗa.—1 Korinthiyawa 14:16.
8. Ta yaya wasu cikin addu’o’inmu za su yi kama da addu’o’in Yakubu ko Ibrahim, kuma menene wannan zai nuna game da mu?
8 Da akwai lokacin da Allah zai ƙyale mu mu nuna zurfin damuwarmu game da batutuwa da muke addu’a a kansu. Muna iya zama kamar Yakubu na dā, da ya yi kokawa da mala’ika dukan dare domin ya sami albarka. (Farawa 32:24-26) Wani yanayi na iya bukatar mu zama kamar Ibrahim, wanda ya roƙi Jehobah a kai a kai domin Lutu da wasu mutane masu adalci da ƙila suna Saduma. (Farawa 18:22-33) Muna iya roƙon Jehobah game da abubuwa da muke ɗauka da tamani, muna hakan bisa yin gaskiyarsa, alheri, da jinƙai.
Menene Za Mu Roƙa?
9. Menene ya kamata ya zama damuwarmu ta ainihi sa’ad da muke addu’a?
9 Ka tuna cewa Bulus ya ce: ‘Cikin kowane abu . . . bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.’ (Filibbiyawa 4:6) Shi ya sa, addu’o’i na kanmu za su iya shafan kusan kowane fasali na rayuwarmu. Amma, damuwarmu ta farko ya kamata ta zama abubuwa da suka shafi Jehobah. Daniel ya kafa misali mai kyau game da wannan. Sa’ad da Isra’ilawa suke shan wahala domin zunubansu, Daniel ya roƙi Jehobah ya yi musu jinƙai, yana cewa: “Kada ka yi jinkiri; sabili da kanka, ya Allahna.” (Daniel 9:15-19) Addu’o’inmu suna nuna cewa tsarkake sunan Jehobah da cikar nufinsa sune damuwarmu ta musamman kuwa?
10. Ta yaya muka sani cewa ya dace mu yi addu’a game da batutuwa na kanmu?
10 Ya kuma dace mu yi roƙo game da batutuwa na kanmu. Alal misali, kamar mai zabura, muna iya addu’a don mu fahimci abubuwa na ruhaniya sosai. Ya yi addu’a: “Ka fahimtadda ni, ni kuma zan maida hankali ga shari’arka; hakika zan kiyaye ta da dukan zuciyata.” (Zabura 119:33, 34; Kolossiyawa 1:9, 10) Yesu “ya miƙa addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai-zafi da hawaye ga wanda yana da iko ya cece shi daga cikin mutuwa.” (Ibraniyawa 5:7) Ta yin haka, ya nuna cewa ya dace mutum ya nemi ƙarfi sa’ad da yake fuskantar haɗari ko kuma gwaji. Sa’ad da yake koya wa almajiransa addu’a ta misali, Yesu ya haɗa wasu damuwa ta mutane, kamarsu gafarta wa kuskure da samun abincin yini.
11. Ta yaya addu’a za ta taimake mu kada mu faɗa ga gwaji?
11 A wannan addu’ar misali, Yesu ya ambata wannan roƙon: “Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga Mugun.” (Matta 6:9-13) Bayan haka ya ba da gargaɗi: “Ku yi tsaro, ku yi addu’a, kada ku shiga cikin jarraba.” (Matta 26:41) Addu’a tana da muhimmanci sa’ad da muke fuskantar gwaji. Muna iya fuskantar gwaji mu yi banza da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a wajen aiki ko a makaranta. Waɗanda ba Shaidu ba suna iya gayyatarmu mu bi su yin ayyuka da ba su da kyau. Ana iya gaya mana mu yi abubuwa da suka taka ƙa’idodi na adalci. A irin wannan lokacin yana da kyau mu bi gargaɗin Yesu mu yi addu’a kafin mu fuskanci gwaji ko kuma lokacin da muke cikin gwajin, mu gaya wa Allah ya taimake mu kada mu faɗi.
12. Waɗanne abubuwa ne da ke kawo alhini za su iya motsa mu mu yi addu’a, menene Jehobah zai yi?
12 Bayin Allah a yau suna fuskantar matsi da alhini dabam dabam a rayuwa. Ciwo da matsi na sosuwar zuciya su ne ainihin dalilin da ya sa mutane da yawa suke alhini. Mugun yanayi da ya kewaye mu na sa rayuwa ta kasance da matsi. Talauci yana sa ya kasance da wuya a biya bukatar rayuwa. Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Jehobah yana sauraron bayinsa da suke kai masa waɗannan batutuwa! Zabura 102:17 ta ce game da Jehobah: “Ya ji addu’ar masu-mayata, ba ya rena addu’arsu ba.”
13. (a) Waɗanne batutuwa na kanmu ne ya dace mu yi addu’a game da su? (b) Ka ba da misalin irin wannan addu’ar.
13 Hakika, ya dace mu haɗa kowane batu da ya shafi hidimarmu ga Jehobah ko kuma dangantakarmu da shi cikin addu’a. (1 Yohanna 5:14) Idan za ka tsai da shawara game da aure ko kuma aiki ko game da faɗaɗa hidimarka, kada ka ɓata lokaci ka nemi ja-gorar Allah. Alal misali, wata budurwa a ƙasar Philippines tana son ta shiga hidima ta cikakken lokaci. Amma, ba ta da aiki da zai taimake ta ta biya bukatunta. Ta ce: “Wata ranar Asabar, na yi wa Jehobah addu’a ainihi game da aikin majagaba. Da na fita aikin wa’azi a ranar, na ba wa wata matashiya littafi. Farat ɗaya, yarinyar ta ce: ‘Ki je makarantarmu a ranar Litinin da safe.’ Sai na ce ‘Me ya sa?’ Ta yi mini bayani cewa akwai aikin da ake bukatar ma’aikaci nan da nan. Na je, sai na soma aiki nan da nan. Duka sun faru babu ɓata lokaci.” Shaidu da yawa a dukan duniya sun taɓa fuskantar irin wannan yanayin. Saboda haka, kada ka yi jinkirin yi wa Allah addu’a da dukan zuciyarka!
Idan Mun Yi Zunubi Fa?
14, 15. (a) Me ya sa ya kamata mutum ya yi addu’a ko da ya yi zunubi? (b) Ban da addu’o’i na kanmu, menene kuma zai taimaki mutum ya farfaɗo daga zunubi?
14 Ta yaya addu’a za ta taimaka idan mutum ya yi zunubi? Domin kunya, wasu da suka yi zunubi suna ƙin yin addu’a. Amma, wannan ba tafarki ba ne mai kyau da za a bi. Alal misali: Matuƙan jirgin sama sun sani cewa idan sun ɓace, za su iya magana da masu ja-gorar jiragen sama don su sami taimako. Idan matuƙin jirgin sama ya ƙi yi wa masu ja-gorar jiragen sama magana domin yana jin kunya ya ɓata fa? Wannan zai kawo haɗari! Haka nan ma, mutumin da ya yi zunubi kuma yana jin kunyar yi wa Allah addu’a zai faɗa cikin haɗari. Kunya domin zunubi bai kamata ya hana mu yi wa Jehobah magana ba. Hakika, Allah yana gayyatar waɗanda suka yi kuskure mai tsanani su yi masa addu’a. Annabi Ishaya ya aririci masu zunubi na zamaninsa su yi addu’a ga Jehobah, “gama za ya yi gafara a yalwace.” (Ishaya 55:6, 7) Hakika, mutum na iya ‘biɗan yardar Jehobah’ ta wajen kasancewa da tawali’u, ya daina bin mummunar tafarki, kuma ya tuba da gaske.—Zabura 119:58; Daniel 9:13.
15 Idan muka yi zunubi, yana da muhimmanci mu yi addu’a don wani dalili. Almajiri Yakubu ya ce game da wani da yake bukatar taimako na ruhaniya: “Sai shi kira dattiɓan ikilisiya su yi addu’a a bisansa, . . . Ubangiji kuwa za ya tashe shi.” (Yaƙub 5:14, 15) Hakika, ya kamata mutumin ya yi addu’a ya yi ikirarin zunubinsa ga Jehobah, amma zai iya gaya wa dattawa su yi addu’a a madadinsa. Wannan zai taimake shi ya sami warkewa na ruhaniya.
Yadda Ake Amsa Addu’o’i
16, 17. (a) Ta yaya Jehobah yake amsa addu’o’i? (b) Waɗanne labarai ne suka nuna cewa addu’a da aikin wa’azi suna da nasaba?
16 Ta yaya ake amsa addu’o’i? Ana amsa wasu da sauri kuma ya kasance a bayyane. (2 Sarakuna 20:1-6) Wasu za su ɗan ɗauki lokaci, kuma ba za a fahimci an amsa addu’ar ba. Kamar yadda aka nuna a kwatancin Yesu game da gwauruwa da ta ci gaba da zuwa wurin alƙali, mutum na iya ci gaba da yi wa Allah addu’a game da batun. (Luka 18:1-8) Amma, mu kasance da tabbaci cewa sa’ad da muka yi addu’a cikin jituwa da nufin Allah, Jehobah ba zai taɓa gaya mana: “Kada ka dame ni” ba.—Luka 11:5-9.
17 A yawancin yanayi, mutanen Jehobah sun fahimci cewa an amsa addu’arsu. Hakan na faruwa sau da yawa a hidimarmu ta fage. Alal misali, ’yan’uwa mata biyu a Philippines suna ba da littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki a wani ƙauye. Sa’ad da suka ba wata mata warƙa, sai idanunta suka cika da hawaye. Ta ce: “Jiya daddare na yi addu’a Allah ya aiki wani ya koya mini Littafi Mai Tsarki, ina ganin wannan amsa ce ga addu’ata.” Ba da daɗewa ba, matar ta soma halartan taro a Majami’ar Mulki. A wani bangaren Kudu maso gabashin Asiya, wani ɗan’uwa yana jin tsoron wa’azi a gidajen da suke da tsaro sosai. Amma, ya yi wa Jehobah addu’a, ya yi ƙarfin zuciya, kuma ya shiga gidan. Ya ƙwanƙwasa ƙofar wani gida, kuma wata budurwa ta fito. Sa’ad da ɗan’uwan ya bayyana dalilin ziyararsa, sai ta soma kuka. Ta ce, da daɗewa take neman Shaidun Jehobah kuma ta yi addu’a ta sami taimako don ta same su. Ɗan’uwan da farin ciki ya taimake ta ta sami ikilisiya na Shaidun Jehobah.
18. (a) Idan aka amsa addu’o’inmu, me ya kamata mu yi? (b) Wane tabbaci ne za mu kasance da shi idan muka yi addu’a a kowane zarafi?
18 Hakika, addu’a tanadi ne mai ban al’ajabi. Jehobah yana shirye ya saurara kuma ya aikata ga addu’o’inmu. (Ishaya 30:18, 19) Duk da haka, muna bukatar mu lura da yadda Jehobah yake amsa addu’o’inmu. Ba koyaushe yake kasancewa yadda muke so ba. Duk da haka, sa’ad da muka fahimci ja-gorarsa, kada mu manta mu yi masa godiya kuma mu yabe shi. (1 Tassalunikawa 5:18) Ƙari ga haka, koyaushe ka tuna da gargaɗin Bulus: “Cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.” Hakika, ka yi amfani da kowane zarafi ka yi wa Allah magana. Ta haka, za ka ci gaba da ganin gaskiyar abin da Bulus ya faɗa game da waɗanda ake amsa addu’arsu: “Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku.”—Filibbiyawa 4:6, 7.
Za Ka Iya Amsawa?
• Waɗanne irin addu’o’i ne za mu iya yi?
• Yaya ya kamata mu yi addu’a?
• Waɗanne batutuwa ne za mu haɗa a cikin addu’armu?
• Menene hakkin addu’a sa’ad da mutum ya yi zunubi?
[Hotuna a shafi na 25]
Addu’a da dukan zuciya za ta taimake mu kada mu faɗa wa gwaji
[Hotuna a shafi na 27]
Ta wurin addu’a, muna furta godiyarmu, damuwa, da roƙe-roƙenmu ga Allah