Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Zabura na Biyar
MAWADATA suna iya cewa: “ ’Ya’yanmu maza za su zama kamar dashe dashe waɗanda sun yi girma tun cikin ƙuruciyarsu; ’ya’yanmu mata kuma kamar duwatsu na ƙusurwoyi sassaƙaƙu bisa fasalin gini na fāda. Sa’anda rumbunanmu suna cike, . . . tumakinmu kuma suna hayayyafa dubbai da dubbai goma.” Ƙari ga haka, masu arziki suna iya furtawa: “Masu-farin zuciya ne mutane waɗanda suna da wannan irin zama!” Amma, akasarin haka, mai zabura ya ce: “Masu-farin zuciya ne mutane, waɗanda Ubangiji ne Allahnsu.” (Zabura 144:12-15) Yaya ta kasance hakan? Jehobah Allah mai farin ciki ne, kuma waɗanda suke bauta masa suna farin ciki. (1 Timothawus 1:11) Tari na ƙarshe na waƙoƙin da Allah ya hure, da ke Zabura ta 107 zuwa 150 sun nuna cewa wannan gaskiya ne.
Littafin Zabura na Biyar ya kuma nanata halayen Jehobah mafi kyau, har da ƙaunarsa ta alheri, gaskiya da kuma nagarta. Idan mun ƙara samun fahimi game da mutuntakar Allah, za mu daɗa ƙaunarsa kuma mu ji tsoronsa. Wannan zai sa mu yi farin ciki. Muna da saƙo mai tamani a Littafin Zabura na Biyar!—Ibraniyawa 4:12.
FARIN CIKI DOMIN ƘAUNA TA ALHERI NA JEHOBAH
(Zabura 107:1–119:176)
Da suke dawowa daga bauta a Babila, Yahudawa sun rera waƙa suna cewa: “Da dai mutane suka yarda su yabi Ubangiji domin alherinsa, da al’ajabansa da ya ke yi ma ’yan Adam kuma.” (Zabura 107:8, 15, 21, 31) Da yake yabon Allah, Dauda ya rera waƙa ya ce: “Gaskiyarka kuma ta kai har ga sararin sama.” (Zabura 108:4) A waƙa ta gaba ya yi addu’a: “Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga jinƙanka.” (Zabura 109:18, 19, 26) Zabura ta 110 annabci ne na sarautar Almasihu. “Tsoron Ubangiji mafarin hikima ne,” in ji Zabura ta 111:10. Zabura ta gaba ta ce, “mai-albarka ne mutum wanda ya ke tsoron Ubangiji.”—Zabura 112:1.
Ana kiran Zabura 113 zuwa 118 Zabura ta Yabo, an kira su hakan domin a kai a kai sun yi amfani da furci nan “Hallelujah,” ko kuma ‘Ka Yabi Jehobah!’ Bisa rubutun Mishnah da aka yi a ƙarni na uku inda aka rubuta al’ada na farko, ana rera waɗannan waƙoƙi a Idin Ƙetarewa da kuma bukkoki uku da Yahudawa suke yi a kowace shekara. Zabura ta 119 ce ta fi yawa a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ta ɗaukaka kalmar Jehobah ko saƙo da aka bayyana.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
109:23—Menene Dauda yake nufi sa’ad da ya ce: “Na shuɗe kamar inuwa sa’anda ta miƙe”? A alamance Dauda yana faɗan cewa yana jin kamar mutuwarsa ta yi kusa.—Zabura 102:11.
110:1, 2—Menene Yesu Kristi ‘Ubangijin [Dauda]’ yake yi sa’ad da yake zama a hannun dama na Allah? Bayan tashinsa daga matattu, Yesu ya koma sama kuma ya jira a hannun dama na Allah har sai shekara ta 1914 da ya soma sarauta. A lokacin, Yesu ya yi sarauta bisa mabiyansa shafaffu, yana yi musu ja-gora a aikinsu na wa’azi da almajirantarwa kuma yana shirya su su yi sarauta da shi a Mulkinsa.—Matta 24:14; 28:18-20; Luka 22:28-30.
110:4—Wace rantsuwa ce Jehobah ya yi da ‘ba za shi tuba ba’? Wannan rantsuwar alkawari ne da Jehobah ya yi da Yesu Kristi don ya yi hidima na Sarki da Babban Firist.—Luka 22:29.
113:3—Ta yaya za a yabi sunan Jehobah “tun daga mafitar rana har mafaɗatta”? Wannan ba rukunin masu bauta wa Allah kowace rana kawai ba ne. Daga fitowar rana a gabas zuwa faɗuwarta a yamma, tsirkiyar rana tana haskaka dukan duniya. Hakanan ma, za a yabi Jehobah a dukan duniya. Ba za a cim ma wannan ba tare da haɗa hannu ba. Da yake mu Shaidun Jehobah ne, muna da gatar yabon Allah kuma muna aikin shelar Mulki da himma.
116:15—Ta yaya yake ‘a ganin Ubangiji Mutuwar tsarkaka abu mai-daraja ne’? Masu bauta wa Jehobah suna da tamani a gare shi, ba zai ƙyale mutuwarsu na rukuni ba domin yana ɗaukansa abu mai tamani sosai. Idan Jehobah ya ƙyale wannan ya faru, zai zama kamar magabtansa sun fi shi ƙarfi. Ban da haka, idan hakan ya faru, ba wanda zai zama tushen sabuwar duniya.
119:71—Menene amfanin shan wahala? Wahala za ta iya koya mana mu dogara sosai ga Jehobah, mu yi masa addu’a sosai, kuma mu ƙara yin ƙwazo wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da yin abin da ya ce. Ƙari ga haka, yadda muka aikata ga wahala zai iya nuna kasawa da za a daidaita. Wahala ba za ta sa mu baƙin ciki ba idan muka ƙyale ta ta gyara mu.
119:96—Menene ake nufi da “ƙarshen dukan kamalta”? Mai zabura yana magana game da kamalta ta ra’ayin ’yan adam. Mai yiwuwa yana magana cewa ra’ayin ’yan adam game da kamalta yana da iyaka. Amma, dokar Allah ba ta da irin wannan iyaka. Ja-gorarsa ta shafi dukan fannonin rayuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Na ga ƙarshen dukan kamalta; amma dokarka tana da fāɗi ƙwarai.”
119:164—Menene ma’anar yabon Allah “so bakwai rana ɗaya”? Adadin nan sau bakwai, a yawancin lokaci yana nufin cikakke. Saboda haka, mai zabura yana cewa Jehobah ya cancanci a riƙa yabonsa shi kaɗai.
Darussa Dominmu:
107:27-31. Hikimar duniya za ta ‘zama banza’ sa’ad da Armageddon ya zo. (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Ba zai ceci kowa daga halaka ba. Sai waɗanda suka dogara ga Jehobah don ceto ne kawai za su yi rayuwa “su yabe [shi] saboda alherinsa.”
109:30, 31; 110:5. Garkuwa da ake riƙewa a hannun hagu ba ta kāre hannun damar da soja yake riƙe takobi da ita. A alamance, Jehobah yana “hannun daman” bayinsa don ya kāre su. Ta haka, yana kāre su da kuma taimakonsu, wannan dalili ne mai kyau na “yi [masa] babbar godiya!”
113:4-9. Jehobah maɗaukaki ne da zai ƙasƙantar da kansa don “ya duba abubuwan da ke cikin sama.” Duk da haka, yana juyayin matalauci, da kuma bakararriya. Ubangiji Jehobah Mai Ikon Mallaka mai tawali’u ne kuma yana son masu bauta masa su yi koyi da hakan.—Yaƙub 4:6.
114:3-7. Koyo daga ayyuka masu ban al’ajabi da Jehobah ya yi domin mutanensa a Jar Teku, a Kogin Urdun, da kuma Dutsen Sinai ya kamata su motsa mu sosai. Ya kamata ’yan adam da “duniya” ke wakilta su ji tsoro, wato a alamance su “yi rawan tsoro” domin Ubangiji.
119:97-101. Samun hikima, basira, da fahimi na Kalmar Allah na kāre mu daga lahani na ruhaniya.
119:105. Kalmar Allah fitila ce domin za ta iya taimakonmu mu bi da matsaloli na yanzu. A alamance tana haskaka hanyarmu, tun da yake tana annabta nufin Allah don nan gaba.
SUNA FARIN CIKI DUK DA WAHALA
(Zabura 120:1–145:21)
Ta yaya za mu bi da yanayi na gwaji kuma mu tsira wa wahala? Zabura ta 120 zuwa 134 sun ba da amsar da ta fita sarai ga wannan tambayar. Muna kauce wa wahala kuma mu ci gaba da farin ciki ta wajen neman taimakon Jehobah. Wataƙila Isra’ilawa ne suka rera wannan zabura, da aka kira Waƙoƙi na Hawa, sa’ad da suke zuwa Urushalima don idodinsu na kowace shekara.
Zabura ta 135 da 136 sun nuna cewa Jehobah ne Mai Yin kowane abu da yake so, ya bambanta da gumaka da ba sa taimako. Zabura ta 136 waƙar amshi ce, an rera sashe na ƙarshe na kowace aya don a amsa na farkon. Zabura ta gaba ta yi maganar mugun yanayi na Yahudawa a Babila da suke son su bauta wa Jehobah a Sihiyona. Dauda ne ya rera zabura ta 138 zuwa 145. Yana son ya yi wa Jehobah ‘godiya da dukan zuciyarsa.’ Me ya sa? Ya ce: “Gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa.” (Zabura 138:1; 139:14) A zabura biyar ta gaba, Dauda ya yi addu’a don samun kāriya daga mugaye, a tsauta masa cikin adalci, a cece shi daga matsananta, kuma a yi masa ja-gora a halinsa. Ya nanata farin cikin mutanen Jehobah. (Zabura 144:15) Bayan ya maimaita girman Allah da nagartansa, Dauda ya ce: “Bakina za ya faɗi yabon Ubangiji; Bari dukan abu mai-rai kuma shi albarkaci sunansa mai-tsarki har abada abadin.”—Zabura 145:21.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
122:3—Ta yaya Urushalima ta zama birni da ke “harhaɗe wuri ɗaya”? Kamar yadda yake a birane na dā, an gina gidajen da ke Urushalima harhaɗe a wuri ɗaya. Birnin a haɗe yake kuma wannan ya sa yana da sauƙi a kāre shi. Ban da haka, da yake gidajen na kusa da juna wannan ya sa waɗanda suke cikin birnin su dogara da juna don taimako da kāriya. Wannan yana nuna haɗin kai na ruhaniya na ƙabilun Isra’ila 12 sa’ad da suka taru don bauta.
123:2—Menene ma’anar kwatanci na idanun bayi? Bayi maza da mata suna neman taimakon ubangida ko uwargida don dalilai biyu: don su san abin da yake so ko take so kuma su sami kāriya da bukatun rayuwa. Hakanan ma, mun dogara ga Jehobah don mu fahimci nufinsa kuma mu sami tagomashinsa.
131:1-3—Ta yaya Dauda ya ‘kwantadda ransa ya kawaita shi; kamar ’ya’yayyen yaro wurin uwarsa’? Kamar yadda yaro da aka yaye yake son uwarsa ta maida masa hankali, Dauda ya koyi ya kwantar kuma ya kawaita ransa kamar “ ’ya’yayyen yaro wurin uwatasa.” Ta yaya? Ba ya girman kai da kuma kwaɗayi kuma ba ya biɗan manyan abubuwa. Maimakon ya nemi girma, Dauda ya fahimci kasawarsa kuma ya kasance da tawali’u. Yana da kyau mu yi koyi da halinsa, musamman idan muna burin aikin kula da ikilisiya.
Darussa Dominmu:
120:1, 2, 6, 7. Tsegumi da furcin reni za su iya sa wasu baƙin ciki sosai. Mai da hankali ga abin da muke faɗa hanya ɗaya ce ta nuna cewa muna ‘biɗan’ salama.
120:3, 4. Idan za mu jimre da wanda yake da “harshe mai-algus,” mu sami ƙarfafa da sanin cewa Jehobah zai daidaita al’amura a nasa lokacin. Masu tsegumi za su sha wahala a hannun “manyan mutane.” “Garwashi na juniper” na wakiltan hukuncin Jehobah a kansu.
127:1, 2. A dukan abubuwa da muke yi, ya kamata mu nemi ja-gorar Jehobah.
133:1-3. Haɗin kan mutanen Jehobah na kwantar da rai, yana da kyau, kuma yana wartsakewa. Bai kamata mu ɓata haɗin kan nan ba ta wurin neman laifi, jayayya, ko kuma yin gunaguni.
137:1, 5, 6. Masu bauta wa Jehobah da suka tafi bauta sun manne wa Sihiyona wadda take wakiltar ƙungiyar Allah. Mu kuma fa? Mun manne wa ƙungiyar da Jehobah yake amfani da ita cikin aminci a yau?
138:2. Jehobah yana ‘girmama kalmarsa bisa ga dukan sunansa,’ domin cikar dukan abubuwan da ya yi alkawari cikin sunansa za su fi kome da muke tsammaninsa. Hakika, muna da bege mai girma nan gaba.
139:1-6, 15, 16. Jehobah ya san ayyukanmu, tunaninmu, da kalmominmu kafin ma mu furta su. Ya san mu tun kafin gaɓaɓuwanmu su cika, kafin a san kowane sashen jikinmu. Yadda Allah ya san mu yana da ban ‘al’ajabi’ da ba za mu iya fahimta ba. Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Jehobah yana ganin yanayi na gwaji da muke fuskanta kuma ya fahimci yadda hakan ke shafanmu!
139:7-12. Ba inda za mu je da Allah ba zai iya ƙarfafa mu ba.
139:17, 18. Ilimin Jehobah ya zama abu mai daɗi a gare mu kuwa? (Misalai 2:10) Idan haka ne, mun sami farin ciki da ba ya ƙarewa. Tunanin Jehobah “sun fi yashi yawa.” Da ƙarin abubuwa da za mu koya game da shi.
139:23, 24. Ya kamata mu so Jehobah ya bincika muradinmu ko akwai wata “hanyar mugunta,” wato, tunani, sha’awoyi, da nufe-nufen da ba su dace ba, kuma ya taimake mu mu kawar da su.
143:4-7. Ta yaya za mu jimre wahala mai tsanani? Mai zabura ya ba da amsar: Ka yi bimbini a kan ayyukan Jehobah, mu maida hankali sosai ga ayyukansa, kuma mu yi addu’a don taimakonsa.
“Hallelujah!”
Kowane tari huɗu na zabura na farko ya ƙare da furcin yabo ga Jehobah. (Zabura 41:13; 72:19, 20; 89:52; 106:48) Tari na ƙarshe ya kammala da waɗannan kalmomin. Zabura 150:6 ta ce: “Abin da yake da numfashi duka shi yi yabon Ubangiji. Hallelujah!” Hakan zai zama gaskiya a sabuwar duniya ta Allah.
Yayin da muke sauraron lokacin nan na farin ciki, muna da dalili mai kyau na ɗaukaka Allah na gaskiya kuma mu yabi sunansa. Idan muka yi tunanin farin ciki da muke yi domin mun san Jehobah kuma muna more dangantaka mai kyau da shi, ba ma farin ciki mu yabe shi da zuciya da take cike da godiya?
[Hoto a shafi na 30]
Ayyukan Jehobah suna da ban al’ajabi
[Hoto a shafi na 31]
Tunanin Jehobah “sun fi yashi yawa”