Yadda Ya Kamata Mu Yi Magana Da “Mai-jin Addu’a”
“Ya mai-jin addu’a, a gareka dukan masu-rai za su zo.”—ZABURA 65:2.
1. Me ya sa ’yan adam suka bambanta da sauran halittu na duniya, kuma wane zarafi wannan ya ba mu?
A CIKIN dubban halittun da ke duniya, ’yan adam ne kawai suke bauta wa Mahalicci. ’Yan adam ne kawai suka fahimci cewa suna da bukata ta ruhaniya kuma suna sha’awar su gamsar da ita. Wannan ya ba mu zarafi na ƙulla dangantaka da Ubanmu na samaniya.
2. Yaya zunubi ya shafi dangantakar ’yan adam da Mahaliccinsu?
2 Allah ya halicci mutum ya iya magana da Mahaliccinsa. Adamu da Hauwa’u ba su da zunubi da aka halicce su. Da haka za su iya yi wa Allah magana yadda yaro zai yi da ubansa. Amma, ba su da wannan gatar kuma domin sun yi zunubi. Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah rashin biyayya kuma suka yi hasarar dangantakarsu na kud da kud da shi. (Farawa 3:8-13, 17-24) Wannan yana nufi ne cewa ’ya’yan Adamu ajizai ba za su iya magana da Allah ba? A’a, har ila Jehobah yana barin su su yi magana da shi idan sun cika wasu bukatu. Waɗanne bukatu ke nan?
Bukatu don Yin Magana da Allah
3. Yaya ya kamata ’yan adam masu zunubi su yi magana da Allah, wane misali ne ya nuna hakan?
3 Wani abu da ya faru da ya shafi ’ya’yan Adamu maza biyu ya taimake mu mu ga abin da Allah yake bukata wajen ’yan adam ajizai da suke son su yi magana da shi. Kayinu da Habila sun yi ƙoƙari su yi magana da Allah ta wajen yi masa hadayu. Allah ya karɓi hadayar Habila, amma ya ƙi na Kayinu. (Farawa 4:3-5) Me ya jawo hakan? Ibraniyawa 11:4 ta ce: “Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa ma Allah hadaya mafi kyau bisa ga ta Kayinu, ta wurin wannan kuwa aka bada shaida a kansa mai-adalci ne shi.” A bayyane yake cewa ana bukatar bangaskiya don a yi magana da Allah. An ga wata bukata a kalmomin Jehobah ga Kayinu: “Idan ka kyauta, ba za a amsa ba?” Hakika, da Allah ya yarda Kayinu ya kusance shi inda ya juya ga yin nagarin abu. Amma, Kayinu ya ƙi gargaɗin Allah, ya kashe Habila, kuma ya zama mai yawo a duniya. (Farawa 4:7-12) Saboda haka, da farko, an nanata muhimmancin yin magana da Allah cikin bangaskiya da yin ayyuka masu kyau.
4. Menene ya kamata mu fahimta game da yin magana da Allah?
4 Yana da muhimmanci mu fahimci yanayinmu na zunubi idan muna son mu yi magana da Allah. Dukan mutane masu zunubi ne, kuma zunubi tangarɗa ne wajen yin magana da Allah. Annabi Irmiya ya rubuta game da Isra’ila yana cewa: “Mun yi laifi, . . . ka ɓuya cikin girgije, domin kada addu’armu ta zarce zuwa gareka.” (Makoki 3:42, 44) Duk da haka, a dukan tarihin ’yan adam Allah ya nuna yana shirye ya amsa addu’o’in da mutane suka yi cikin bangaskiya da zukatan kirki, suna kiyaye dokokinsa. (Zabura 119:145) Su wanene waɗannan mutanen, kuma me za mu koya daga addu’o’insu?
5, 6. Menene za mu koya daga yadda Ibrahim ya yi wa Allah magana?
5 Ɗaya daga cikinsu shi ne Ibrahim. Allah ya yarda Ibrahim ya yi magana da shi, gama ya kira shi “aminina.” (Ishaya 41:8) Menene za mu koya daga yadda Ibrahim ya yi magana da Allah? Wannan uban iyali ya yi wa Jehobah magana game da magaji, yana cewa: “Ya Ubangiji Yahweh, mi za ka ba ni, da shi ke zan fita nan marar-ɗa.” (Farawa 15:2, 3; 17:18) A wani yanayi, ya nuna damuwarsa game da wanda zai tsira sa’ad da Allah ya zartar da hukunci a kan miyagu a Saduma da Gwamrata. (Farawa 18:23-33) Ibrahim ya yi addu’a domin wasu. (Farawa 20:7, 17) Kamar Habila, akwai lokacin da Ibrahim ya yi wa Jehobah magana ta wurin yi masa hadaya.—Farawa 22:9-14.
6 A waɗannan lokatai, Ibrahim ya saki jiki ya yi wa Jehobah magana. Amma, ’yancin maganarsa ya haɗa da sanin matsayinsa cikin tawali’u a gaban Mahaliccinsa. Ka lura da kalmominsa na ladabi da ke rubuce a Farawa 18:27: “Ga shi yanzu, na yi karambani in yi zance da Ubangiji, ni da ni ke ba komi sai turɓaya da toka.” Wannan hali ne mai kyau da za mu iya koya!
7. Waɗanne batutuwa ne ubanni suka yi wa Jehobah addu’a a kai?
7 Ubanni sun yi addu’a game da batutuwa dabam dabam, kuma Jehobah ya ji addu’arsu. Yakubu ya yi alkawari cikin addu’a. Bayan ya nemi taimakon Allah, ya yi alkawari: “Ni kuma hakika im ba ka ushira daga cikin dukan abin da za ka ba ni.” (Farawa 28:20-22) Bayan haka, sa’ad da yake son ya sadu da ɗan’uwansa, Yakubu ya roƙi Jehobah ya kāre shi, yana cewa: “Ka cece ni daga hannun ɗan’uwana, daga hannun Isuwa: gama ina jin tsoronsa.” (Farawa 32:9-12) Ayuba ya yi wa Jehobah addu’a a madadin iyalinsa, ya miƙa hadayu dominsu. Sa’ad da abokan Ayuba uku suka yi zunubi ta abin da suka faɗa, Ayuba ya yi addu’a dominsu, “Ubangiji kuwa ya yarda da Ayuba.” (Ayuba 1:5; 42:7-9) Waɗannan labaran sun nuna abubuwan da za mu yi wa Jehobah addu’a a kai. Mun kuma ga cewa Jehobah yana shirye ya ji addu’o’in da aka yi masa a hanyar da ta dace.
A Ƙarƙashin Dokar Alkawari
8. A ƙarƙashin Dokar alkawari, ta yaya ake yi wa Jehobah addu’a a madadin mutanen?
8 Bayan Jehobah ya ceci al’ummar Isra’ila daga Masar, ya ba su Dokar alkawari. Dokar ta faɗi tsarin yi wa Allah magana ta wajen firistoci da aka naɗa. An ba wa wasu Lawiyawa aikin firistoci a madadin mutanen. Idan batu da ya shafi dukan al’ummar ya taso, wakilin mutanen, wani lokaci sarki ko kuma annabi zai yi wa Allah addu’a game da batun. (1 Samuila 8:21, 22; 14:36-41; Irmiya 42:1-3) Alal misali, sa’ad da yake keɓe haikalin da ke Urushalima, Sarki Sulemanu ya yi wa Jehobah addu’a da dukan zuciyarsa. Jehobah kuma ya nuna ya karɓi addu’ar Sulemanu ta wurin cika haikalin da ɗaukakarsa kuma ya ce: “Kunnuwana kuma a buɗe ga jin addu’a da a ke yi a cikin wannan wuri.”—2 Labarbaru 6:12–7:3, 15.
9. Menene ake bukata don a yi magana da Jehobah yadda ya dace a wuri mai tsarki?
9 A Dokar da aka ba wa Isra’ilawa, Jehobah ya haɗa abin da suke bukatar su yi don su yi magana da shi a wuri mai tsarki. Menene za su yi? Ban da miƙa hadayu na dabbobi, kowace safiya da dare, ana bukatar babban firist ya ƙona turaren hayaki a gaban Jehobah. Daga baya, mataimakan firist su ma suna wannan hidima, ban da Ranar Kafara. Idan firistocin ba su yi irin wannan bauta na ladabi ba, Jehobah ba zai yi farin ciki da hidimarsu ba.—Fitowa 30:7, 8; 2 Labarbaru 13:11.
10, 11. Wane tabbaci ne muke da shi cewa Jehobah yana jin addu’o’in mutane?
10 A Isra’ila ta dā, ana magana da Allah ne kawai ta wurin wakilai da aka naɗa? A’a, Nassosi sun nuna cewa Jehobah yana farin cikin jin addu’o’in da mutane suka yi da kansu. Sa’ad da Sulemanu yake addu’ar keɓe haikali, ya roƙi Jehobah, yana cewa: “Komi addu’a ko gado da kowa za ya yi, ko da dukan jama’arka Isra’ila za su yi, . . . ya kuwa miƙe hannuwansa yana fuskanta wannan gida; sai ka ji daga sama wurin zamanka.” (2 Labarbaru 6:29, 30) Labarin Luka ya gaya mana cewa sa’ad da Zakariya, baban Yohanna Mai Baftisma yake ƙona turare a wuri mai tsarki, mutane da yawa masu bauta wa Jehobah da ba firistoci ba suna “waje suna addu’a.” Hakika, ya zama al’adar mutane su taru a waje a wuri mai tsarki suna addu’a sa’ad da ake miƙa wa Jehobah turare a kan bagadi na zinariya.—Luka 1:8-10.
11 Saboda haka, sa’ad da aka yi magana da Jehobah yadda ya dace, yana shirye ya ji roƙon waɗanda suke wakiltar al’ummar gabaki ɗaya da kuma waɗanda suka nemi su yi masa magana da kansu. Amma, a yau ba ma ƙarƙashin Dokar alkawari. Duk da haka, za mu iya mu koyi darussa masu muhimmanci game da addu’a daga hanyoyin da Isra’ilawa na dā suka yi wa Allah addu’a.
A Ƙarƙashin Tsarin Kirista
12. Wane tsari ne aka kafa don Kiristoci su kusanci Jehobah?
12 Yanzu muna ƙarƙashin tsarin da Kristi ya kafa. Babu haikali na zahiri inda firistoci suke wakiltan dukan mutanen Allah ko kuma inda za mu je mu yi wa Allah addu’a. Duk da haka, Jehobah har ila ya kafa tsarin da za mu yi magana da shi. Wane tsari ne? Haikali na ruhaniya ya soma aiki sa’ad da aka shafa Kristi da ruhu mai tsarki kuma aka naɗa shi Babban Firist a shekara ta 29 A.Z.a Wannan haikali na ruhaniya sabon tsari ne na yin magana da Jehobah bisa hadayar Yesu Kristi.—Ibraniyawa 9:11, 12.
13. Wane kamanin ne yake tsakanin haikali a Urushalima da haikali na ruhaniya game da addu’a.
13 Fasaloli da yawa na haikali a Urushalima suna kwatanta fannoni na haikali na ruhaniya, har da waɗanda suka shafi addu’a. (Ibraniyawa 9:1-10) Alal misali, menene turare da ake miƙawa da safe da yamma a kan bagadi a wuri Mai Tsarki na haikali ke alamta? In ji littafin Ru’ya ta Yohanna, “addu’o’in tsarkaka ke nan.” (Ru’ya ta Yohanna 5:8; 8:3, 4) An hura Dauda ya rubuta, yana cewa: “Ka bari addu’ata ta miƙu a gabanka kamar turaren ƙonawa.” (Zabura 141:2) Da haka, a tsarin Kirista, turare mai ƙanshi mai daɗi ya nuna cewa an karɓi addu’o’i da kuma yabo ga Jehobah.—1 Tassalunikawa 3:10.
14, 15. Menene za a ce game da yadda (a) Kiristoci shafaffu (b) “waɗansu tumaki” suke magana da Jehobah?
14 Wanene zai yi magana da Allah a wannan haikali na ruhaniya? A haikali na zahiri, firistoci da Lawiyawa suna da gata na hidima a farfajiya na ciki, amma firistoci ne kaɗai za su iya shiga wuri Mai Tsarki. Kiristoci shafaffu da suke da begen zama a sama suna more yanayi na ruhaniya na musamman da farfajiya ta ciki da kuma Mai Tsarki ke wakilta, wannan na taimakon su su yi addu’a kuma su yabi Allah.
15 Waɗanda suke da begen zama a duniya, wato “waɗansu tumaki” fa? (Yohanna 10:16) Annabi Ishaya ya nuna cewa mutanen al’ummai da yawa za su zo su bauta wa Jehobah “a cikin kwanaki na ƙarshe.” (Ishaya 2:2, 3) Ya kuma rubuta cewa “baƙi” za su ba da kansu ga Jehobah. Don ya nuna yana shirye ya karɓi addu’arsu, Allah ya ce: “[Zan] faranta zuciyarsu a cikin gidana na addu’a.” (Ishaya 56:6, 7) Ru’ya ta Yohanna 7:9-15 sun ba da ƙarin bayani, sun kwatanta “taro mai-girma” daga “dukan al’ummai” waɗanda suka taru don su bauta wa Allah su kuma yi masa addu’a “dare da rana” yayin da suke tsaye a farfajiya na waje na haikali na ruhaniya. Yana da ban ƙarfafa cewa dukan bayin Allah a yau za su yi wa Allah addu’a da cikakken tabbaci cewa zai ji su!
Waɗanne Addu’o’i Ne Ake Karɓa?
16. Menene za mu koya game da addu’a daga Kiristoci na farko?
16 Kiristoci na farko mutane ne masu yin addu’a. Waɗanne batutuwa ne suke addu’a a kai? Dattawan Kiristoci sun nemi ja-gora wajen zaɓan mutane don ayyuka na ƙungiyar. (Ayukan Manzanni 1:24, 25; 6:5, 6) Abafras ya yi addu’a domin ’yan’uwa masu bi. (Kolossiyawa 4:12) Waɗanda suke cikin ikilisiya a Urushalima sun yi wa Bitrus addu’a sa’ad da aka saka shi a fursuna. (Ayukan Manzanni 12:5) Kiristoci na farko sun gaya wa Allah ya ba su ƙarfin zuciya sa’ad da suke fuskantar hamayya, suna cewa: “Ubangiji, ka dubi kashedinsu: ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfinzuciya duka.” (Ayukan Manzanni 4:23-30) Almajiri Yakubu ya aririci Kiristoci su yi wa Allah addu’a don su kasance da hikima sa’ad da suke fuskantar gwaji. (Yaƙub 1:5) Kana haɗa irin waɗannan batutuwa sa’ad da kake wa Jehobah addu’a?
17. Addu’o’in su waye ne Jehobah yake amsawa?
17 Ba dukan addu’o’i ba ne Allah yake karɓa. To, ta yaya za mu yi addu’a da tabbaci cewa za a karɓe ta? Mutane masu aminci da Allah ya saurare su a dā sun yi masa addu’a cikin gaskiya da zuciyar kirki. Sun kasance da bangaskiya ta yin ayyuka masu kyau. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai saurari waɗanda suka yi masa addu’a hakan nan a yau.
18. Idan suna son a ji addu’o’insu, waɗanne bukatu ne Kiristoci za su cika?
18 Da akwai ƙarin bukatu. Manzo Bulus ya ba da bayanin wannan, yana cewa: “Ta wurinsa . . . muna da yarjin isowa cikin Ruhu ɗaya zuwa wurin Uban.” Wanene Bulus yake maganarsa sa’ad da ya rubuta, “ta wurinsa”? Yesu Kristi ne. (Afisawa 2:13, 18) Hakika, za mu yi wa Uban magana ta wurin Yesu ne kaɗai.—Yohanna 14:6; 15:16; 16:23, 24.
19. (a) Yaushe ne hadayar turare a Isra’ila yake zama abin ƙyama ga Jehobah? (b) Ta yaya za mu tabbata cewa addu’o’inmu sun zama kamar turare mai ƙanshi mai daɗi ga Jehobah?
19 Kamar yadda aka riga aka faɗa, turare da firistoci na Isra’ila suka miƙa na wakiltar addu’o’in bayin Allah masu aminci. Amma, wani lokaci, Jehobah ba ya karɓan hadayun turare na Isra’ilawa. Hakan ya faru sa’ad da Isra’ilawa suke ƙona turare a haikali amma kuma suna bauta wa gumaka. (Ezekiel 8:10, 11) Hakanan ma a yau, Jehobah ba ya sauraran addu’o’in waɗanda suke da’awa suna bauta masa amma suna ayyuka da suka saɓa wa dokokinsa. (Misalai 15:8) Bari mu ci gaba da kasancewa da tsabta a dukan fannonin rayuwarmu domin addu’o’inmu su zama kamar turare mai ƙanshi mai daɗi ga Allah. Jehobah yana farin ciki da addu’o’in waɗanda suke bin hanyoyinsa na adalci. (Yohanna 9:31) Amma, har ila da wasu tambayoyi. Yaya ya kamata mu yi addu’a? Za mu yi addu’a a kan menene? Ta yaya Allah yake amsa addu’o’inmu? Talifinmu na gaba zai bincika wannan da wasu tambayoyi.
[Hasiya]
a Ka dubi Hasumiyar Tsaro, 15 ga Mayu, 2001, shafi na 27 na Turanci.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Ta yaya mutane ajizai za su yi magana da Allah kuma ya saurare su?
• Ta yaya za mu yi koyi da ubanni sa’ad da muke addu’a?
• Menene muka koya daga addu’o’in Kiristoci na farko?
• Ta yaya addu’o’inmu za su zama kamar turare mai ƙamshi mai daɗi ga Allah?
[Hoto a shafi na 19]
Me ya sa Allah ya karɓi hadayar Habila ba na Kayinu ba?
[Hoto a shafi na 20]
“Ni da ni ke ba komi sai turɓaya da toka”
[Hoto a shafi na 21]
“Ni kuma hakika im ba ka ushira”
[Hoto a shafi na 22]
Addu’o’inka suna kama da turare mai ƙamshi mai daɗi ga Jehobah?