Neman Shugaba na Kirki
“Ka ba mu wuri, na ce, mun riga mun gama da kai. Don Allah ka ɓace mana da gani!”—in ji Leopold Amery, ɗan Majalisar Wakilai na Britaniya, ya yi ƙaulin Oliver Cromwell.
Yaƙin Duniya na II ya yi taɓargaza na watanni takwas, kuma haka bai yi wa Britaniya da kawayenta daɗi ba. Ga Leopold Amery da wasu da suke gwamnati, ana bukatar canji wajen shugabanci. Saboda haka, a ranar 7 ga Mayu, 1940, a Majalisar Wakilai, Mista Amery ya yi ƙaulin wannan furci na baya ga Firayim Minista Neville Chamberlain. Bayan kwana uku, Mista Chamberlain ya sauka daga makaminsa, aka naɗa Winston Churchill.
SHUGABANCI abu ne da ’yan adam suke bukata, amma ba kowane shugaba ba ne zai dace. Har a cikin iyali ma, dole ne mai gida ya kasance mai ja-gora, kafin matarsa da ’ya’yansa su zama masu farin ciki. To, ka yi tunanin abin da ake bukata daga shugaban ƙasa ko kuma shugaba a duniya! Ba abin mamaki ba ne da samun shugabanni na kirki yake da wuya.
Saboda haka, cikin shekaru aru-aru da suka shige, an naɗa sarakuna, an yi sauye-sauye, an kifar da gwamnatoci, an yi naɗe-naɗe, an yi zaɓaɓɓuka, an yi kashe kashe, an kuma sauya gwamnatoci. Sarakuna, firayim ministoci, gwamnoni, manyan magatakarda, shugabannin ƙasashe, da kuma masu baƙin mulki sun ga samun iko da rashinsa. Sauyi na ba zato ba tsammani ya sami har gwarzayen sarakuna. (Dubi akwati nan “Kwace Iko ba Zato ba Tsammani,” a shafi na 5) Duk da haka, shugabanci na kirki mai ɗorewa ya yi wuyan samu.
“Dole ne Mu Yi Jimiri”—Ko Yaya?
Ba abin mamaki ba ne da mutane da yawa suka fid da rai daga samun shugabanci na kirki. A wasu ƙasashe yadda mutane suke nuna ko oho yana bayyana musamman a lokacin zaɓe. Goeff Hill, ɗan jarida a Afirka, ya lura cewa: “Halin ko oho da kuma ƙaurace wa zaɓe yana zama ruwan dare gama duniya sa’ad da mutane suke ganin babu yadda za su yi su canja matsalolin rayuwarsu. . . . A Afirka, sa’ad da mutane suka ƙaurace wa zaɓe, ba sun gamsu ba ne, a’a. Sau da yawa kukan taimako ne daga waɗanda suke jin babu wanda ya damu da sha’aninsu.” Hakazalika, marubucin jarida a ƙasar Amirka ya rubuta game da zaɓe mai zuwa: “Da ma a ce kamilin mutum ne ya nemi a zaɓe shi.” Sai ya daɗa da cewa: “Babu irin wannan mutumin. Ba a ma taɓa yin irinsa ba. Dole ne mu yi jimiri.”
Shin haka ne, ’yan adam ba su da zaɓi sai dai su jimre shugabanci na ajizai? Domin shugabanni sun kasa biyan bukatun mutanen da ke ƙarƙashinsu ya nuna cewa ba za mu taɓa samun shugabanci na kirki ba? A’a. Za a sami shugabanci nagari. Talifi na gaba zai bincika waye ne shugaba da ya dace ga ’yan adam da kuma yadda hidimarsa za ta amfani miliyoyin mutane daga ko’ina, har ma da kai kanka.
[Hotuna a shafi na 3]
Na sama a hagu: Neville Chamberlain
Na sama a dama: Leopold Amery
A ƙasa: Winston Churchill
[Inda aka Daukos]
Chamberlain: Hoto daga Jimmy Sime/Central Press/Getty Images; Amery: hoto daga Kurt Hutton/Picture Post/Getty Images; Churchill: The Trustees of the Imperial War Museum (MH 26392)