Waye Ne Shugaban da Ya Dace a Yau?
A shekara ta 1940, an sami matsalar shugabanci a Majalisar Dattawa ta Britaniya. David Lloyd George, ɗan shekara 77 wanda ya saurari muhawwara, ya ja-goranci Britaniya ta yi nasara a lokacin Yaƙin Duniya na I, kuma yawan shekarun da ya yi a siyasa ya sa ya auna a tsanake ayyukan manyan ma’aikata. A jawabinsa ga Majalisar Wakilai a ranar 8 ga Mayu, ya ce: “Al’umma tana shirye ta saɗaukar da kome idan dai za ta sami shugabanci na ƙwarai, idan kuma Gwamnati za ta nuna a fili abin da take so ta cim ma kuma idan al’umma za ta sami tabbacin cewa waɗanda suke yi mata ja-gora suna yin iyakacin ƙoƙarinsu.”
KALMOMIN Llyod George sun nuna a fili cewa mutane suna sa rai shugabanninsu su dace kuma suna yin ƙoƙari su ga abubuwa sun kyautata. Wata ’yar kamfen na siyasa ta ce: “Sa’ad da mutane suka jefa ƙuri’a ga shugaban ƙasa, suna ba da amanar rayukansu, rayuwarsu, da ’ya’yansu ne.” Riƙe irin wannan amana jan aiki ne. Me ya sa?
Duniyarmu ta cika da matsaloli marasa magani. Alal misali, wane shugaba ne ya nuna shi mai hikima ne ƙwarai mai iko, ya hana yin laifi da yaƙi? Waye tsakanin shugabanni na yau, yake da arziki da kuma tausayin talakawa, da ya yi wa dukan mutane tanadin abinci, ruwa mai tsabta, da kuma hanyar kula da lafiyar jiki? Waye yake da sanin yadda zai kāre mahalli daga gurɓacewa, kuma ya gyara shi? Waye ya isa ya tabbatar da cewa dukan mutane suna samun farin ciki kuma suna more tsawon rai?
’Yan Adam ba Za Su Iya Wannan Aiki Ba
Hakika wasu shugabanni sun yi ɗan nasara. Duk da haka, za su yi mulki na ’yan shekaru ne kawai, sai, wa zai kasance na gaba? Wani shugaba da duk inda shugaba ya kai ya kai, da ya rayu a dā, Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā, shi ya yi wannan tambayar. Kuma ya amsa da cewa: “Daga cikin dukan abin da na samu kan aikin da na yi, ba su da wata ma’ana a gare ni, gama na sani zan bar wa magajina ne. Wa ya sani ko shi mai hikima ne, ko kuma wawa ne? Duk da haka shi zai mallaki dukan abin da na sha wahalar tanadinsa. Dukan aikin da na yi na hikima a wannan duniya aikin banza ne.”—Mai Hadishi 2:18, 19.
Sulemanu bai sani ba ko magajinsa zai ci gaba da aikin kirki da ya yi ko kuma zai lalata su. A ganinsa, sake tsohon shugaba da sabo “aikin banza ne.”
A wasu lokatai, an yi amfani da ƙarfi wajen canja shugabanni. An kashe wasu shugabanni da suka ƙware sa’ad da suke aikinsu. Abraham Lincoln, wanda ya taɓa shugabancin ƙasar Amirka, ya taɓa faɗa wa masu sauraronsa: “An zaɓe ni in ɗauki babban matsayi na ɗan lokaci, amma a idanunku yanzu, ina da rinjaya da zai shuɗe nan da nan.” Hakika, hidimarsa ta ɗan lokaci ne. Duk da abubuwa da ya yi da kuma muradin ya kyautata wa mutanensa, Shugaban ƙasa Lincoln ya shugabanci ƙasarsa na shekara huɗu ne kawai. A farkon shekarar wa’adinsa na biyu, mutumin da yake son canji a gwamnati ne ya kashe shi.
Shugabanni ’yan adam komin cancantarsu ba za su iya tabbatar da rayuwarsu ta gaba ba. Saboda haka, ya kamata ne ka dogara a kansu domin su tabbatar da taka? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ka dogara ga shugabanni, ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba. Sa’ad da suka mutu sai su koma turɓaya, a wannan rana dukan shirye-shiryensu sun ƙare.”—Zabura 146:3, 4.
Shawarar nan kada ka dogara ga shugabanni za ta kasance da wuyar sha’ani. Amma, Littafi Mai Tsarki bai ce ’yan adam ba za su taɓa samun shugabancin kirki mai ɗorewa ba. “Wata rana za a yi wani sarki mai adalci,” in ji Ishaya 32:1. Jehovah Allah kansa, Mahaliccin mutum, ya shirya “sarki,” Shugaba da zai mallaki duniya nan ba da daɗewa ba. Wanene shi? Annabcin Littafi Mai Tsarki ya yi bayani a kansa.
Wanda Ya Cancanci Ya Yi Shugabanci
Shekara dubu biyu da ta shige, mala’ika ya gaya wa wata budurwa mai suna Maryamu: “Za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda, zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada, mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” (Luka 1:31-33) Hakika, Yesu Banazare shi ne Sarkin annabci na Littafi Mai Tsarki.
Ana zana Yesu ɗan jariri a zane-zane na addini, ko kuma mutum mai rauni marar koshi, ko kuma mutum marar farin ciki mai miƙa kai ga dukan abin da ya faru da shi. Irin waɗannan zane-zane ba sa sa mutane su kasance da tabbaci cewa shi Sarki ne. Amma ainihin Yesu Kristi na Littafi Mai Tsarki, ya girma ya zama gwarzon mutum. Kuma yana da wasu halayen da suka sa ya cancanci shugabanci. (Luka 2:52) Waɗannan halaye na gaba kaɗan ne kawai cikin halayensa na musamman.
Yesu ya kasance da cikakken aminci. Domin ɗabi’arsa ta kirki ce ya ƙalubalanci magabtansa su kawo shaidar tuhumar da suke masa. Ba su da shaida. (Yahaya 8:46) Koyarwarsa marar riyya ta sa mutane masu gaskiya sun zama mabiyansa.—Yahaya 7:46; 8:28-30; 12:19.
Yesu ya keɓe kansa gabaki ɗaya ga Allah. Ya ƙuduri anniyar kammala aikin da Allah ya ba shi da babu wanda ya ci nasarar hana shi, mutum ko aljan. Hari daga abokan gaba bai razana shi ba. (Luka 4:28-30) Gajiya da yunwa ba su ƙarya masa lago ba. (Yahaya 4:5-16, 31-34) Ko da yake abokansa sun guje shi, bai gusa daga makasudinsa ba.—Matiyu 26:55, 56; Yahaya 18:3-9.
Yesu ya nuna damuwa sosai ga mutane. Ya ba wa mayunwata abinci. (Yahaya 6:10, 11) Ya yi jaje ga masu baƙin ciki. (Luka 7:11-15) Ya warkar da makafi, kurame, da kuma waɗanda suke bukatar magani. (Matiyu 12:22; Luka 8:43-48; Yahaya 9:1-6) Ya ƙarfafa manzanninsa masu ƙoƙari. (Yahaya, surori 13–17) Ya kasance “makiyayi mai kyau” wanda ya kula da tumakinsa.—Yahaya 10:11-14.
Yesu yana da niyar aiki. Ya wanke ƙafaffun manzanninsa domin ya koya musu muhimmin darasi. (Yahaya 13:4-15) Shi kansa ƙafafunsa sun yi kūra domin ya yi wa’azin bishara yana tafiya a hanyoyi masu kūra na Isra’ila. (Luka 8:1) Har a lokacin da yake shirin ya huta “a wurin da ba kowa,” ya yi wa’azi da jama’a ta taru masa. (Markus 6:30-34) Da haka ya kafa misalin ƙwazo ga dukan Kiristoci.—1 Yahaya 2:6.
Yesu ya kammala aikinsa ya bar duniya. Ladar da aka yi masa domin amincinsa, shi ne Jehovah Allah ya ba shi sarauta da madawwamin rai a samaniya. Game da Yesu da aka ta da daga matattu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tun da ya ke an ta da Almasihu daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba ke nan, mutuwa ba ta da sauran wani iko a kansa.” (Romawa 6:9) Ka tabbata cewa shi ne Shugaba mafi kyau ga ’yan adam. Da zarar Yesu Kristi ya karɓi ikon duniya, babu dalilin ba wa wani iko, ko kuma dalilin sauya shugabanci. Ba za a kifar da gwamnatinsa ba, ba kuma magajin da zai ɓata aikin da ya yi. Amma menene takamaimai zai yi domin ya amfani ’yan adam?
Abin da Wannan Sabon Shugaba Zai Yi
Zabura ta 72 ta yi bayani dalla-dalla game da yadda wannan kamiltaccen madawwamin sarki zai yi sarauta. Ayoyi na 7 da 8, sun ce: “Adalci ya bunƙasa a zamaninsa, wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa. Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku, daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.” A sarautarsa mai ni’ima, mazauna duniya za su more madawwamiyar kwanciyar hankali. Zai halaka dukan makamai kuma ya kawar da muradin yaƙi a zukatan mutane. Mutane da a yau suke kai hari ga wasu kamar mayunwacin zaki ko kuma mahaukaciyar karyar daji za su canja halinsu gaba ɗaya. (Ishaya 11:1-9) Za a sami cikakkiyar lumana.
Zabura ta 72 ta ci gaba da cewa a ayoyi na 12 zuwa 14: “Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi, da waɗanda suke da bukata, da waɗanda ba a kula da su. Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta, yakan ceci rayukan waɗanda ke da bukata. Yakan cece su daga zalunci da kama-karya, rayukansu kuma da daraja a gare shi.” Gajiyayyu, matalauta, da waɗanda aka zalunta za su kasance cikin iyali guda mai farin ciki, a ƙarƙashin sarautar Sarki Yesu Kristi. Farin ciki, ba baƙin ciki da tsoro ba zai kasance a rayuwarsu.—Ishaya 35:10.
Aya ta 16 ta yi alkawari: ‘Za a sami hatsi mai yawa a ƙasar, amfanin gona ya cika tuddan.’ Yunwa ita ce taguwar miliyoyin mutane yau a duniya. Siyasa da haɗama sukan hana raba isashen abinci, saboda haka miliyoyi, musamman yara, sukan mutu domin yunwa. Amma a ƙarƙashin sarautar Yesu Kristi hakan zai shuɗe. Duniya za ta sami albarka ta girbe abinci mai ɗanɗano. Dukan ’yan adam za su ci su tumbutsa.
Za ka so ka more wannan albarka ta shugabancin kirki? To, muna masu ƙarfafa ka ka koyi game da wannan Shugaba da zai karɓi iko bisa duniya ba da daɗewa ba. Shaidun Jehovah za su yi farin cikin taimaka maka ka yi haka. Ba za ka kunyata ba, domin Jehovah Allah da kansa ya ce game da Ɗansa: “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka, Na naɗa sarkina.”—Zabura 2:6.
[Akwati a shafi na 5]
KWACE IKO BA ZATO BA TSAMMANI
Mai sarauta yakan dangana ne ga daraja da kuma goyon bayan mutane da ke ƙarƙashinsa idan ya kyautata musu wajen ba su ɗan lumana da kwanciyar hankali. Saboda da haka, idan mutane suka ƙi shi saboda wani dalili, to, sai a wayi gari wani yana zaune a gadon sarauta. Ga wasu misalai na yanayi da suka sa aka tuge gwarzayen sarakuna daga iko.
Mummunan yanayin rayuwa. A wajajen ƙarshen ƙarni na 18, da yawa cikin Faransawa suna rayuwar ƙunci na biyan haraji ga kuma ƙarancin abinci. Wannan ya kai da Sauyi na Faransa, wanda ya sa a shekara ta 1793 aka fille kan Sarki Lois na XVI.
Yaƙi. Yaƙin Duniya na I ya kawo ƙarshen yawancin gwarzayen sarakuna na tarihi. Alal misali, a shekara ta 1917 ƙarancin abinci da yaƙi ya yi sanadiyarsa a St. Petersburg, na Rasha, wannan ya rikiɗa ya zama neman Sauyi na Fabrairu. Wannan neman sauyin ya sauke Sarki Nicholas II kuma ya kai ga Kwaminisanci. A watan Nuwamba ta shekarar 1918, Jamus suna bukatar salama, amma sojojin kawance ba za su daina faɗa ba sai an sami canji a sarauta. Saboda haka, aka tilas ta wa Sarki Wilhelm II na Jamus zuwa hijira a ƙasar Holan.
Bukatar wani salon gwamnati. A shekara ta 1989 aka rushe Labulen Ƙarfe. Salon sarauta da suke da ƙarfi kamar ƙarfe suka rukuto sa’ad da talakawansu suka ƙi Kwaminisanci suka kafa wasu salon sarauta.
[Hotuna a shafi na 7]
Yesu ya ciyar da mayunwata, ya warkar da marasa lafiya, kuma ya kafa misali mai kyau ga dukan Kiristoci
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 4]
Lloyd George: Hoto daga Kurt Hutton/Picture Post/Getty Images