Bayin Jehovah Suna Da Bege Na Gaske
“Ringin Yaƙub kuma za ya kasance a cikin tsakiyar al’ummai dayawa kamar rāɓa daga wajen Ubangiji . . . wanda ba ya jiran mutum ba.”—MIKAH 5:7.
1. Ta yaya Isra’ila na ruhaniya tushen wartsakewa ne?
JEHOVAH ne Mahaliccin ruwan sama da raɓa, mai girma. Ba shi da amfani mu sa rai a mutane su ba mu raɓa ko ruwan sama. Manzo Mikah ya rubuta: “Ringin Yakubu kuma za ya kasance a cikin tsakiyar al’ummai dayawa kamar rāɓa daga wajen Ubangiji, kamar saukowar ruwa a bisa ciyawa; wanda ba ya jiran mutum ba, ba ya kuwa dakanta ma ’ya’yan mutane ba.” (Mikah 5:7) Su waye ne “ringin Yakubu” na zamanin yau? Isra’ilawa na ruhaniya ne, raguwar “Isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16) Ga “al’ummai dayawa” na duniya, suna kamar “rāɓa daga wajen Ubangiji” mai wartsakewa da kuma “ruwa a bisa ciyawa.” Hakika, shafaffu Kiristoci a yau tushen wartsakewa ne daga Allah ga mutane. Da yake su masu shelar Mulki ne, Jehovah yana amfani da su ya ba mutane saƙonsa na bege na gaskiya.
2. Me ya sa muke da bege na gaske ko da muna zama a wannan duniya da ta wahala?
2 Ba abin mamaki ba ne cewa wannan duniya ba ta da bege na gaske. Rashin kwanciyar hankali na siyasa, rashin tarbiyya, yin laifi, matsalar tattalin arziki, ta’addanci, yaƙe-yaƙe—muna zaton irin waɗannan abubuwa a duniya da Shaiɗan Iblis yake mallaka. (1 Yohanna 5:19) Mutane da yawa suna tsoron abin da za su fuskanta a nan gaba. Amma, mu masu bauta wa Jehovah, ba ma tsoro, muna da tabbataccen bege game da nan gaba. Bege na gaske ne domin daga Kalmar Allah ce. Muna da bangaskiya ga Jehovah da kuma Kalmarsa domin abin da ya faɗa yana kasancewa gaskiya kullayaumi.
3. (a) Me ya sa Jehovah zai yi maganin Isra’ila da Yahuda? (b) Me ya sa kalmomin Mikah suka shafe mu a yau?
3 Annabcin Mikah da Allah ya hure yana ƙarfafa mu mu yi tafiya cikin sunan Jehovah kuma ya ba mu dalilin bege na gaske. A ƙarni na takwas K.Z., sa’ad da Mikah ya yi annabci, an raba mutanen alkawari na Allah zuwa al’ummai biyu—Isra’ila da Yahuda—kuma duka sun yi watsi da alkawarin Allah. Sakamakon rashin tarbiyya ne, riyya ta addini, da kuma son abin duniya. Saboda haka, Jehovah ya yi gargaɗi cewa zai yi maganinsu. Hakika, gargaɗin Allah ga waɗanda suka yi zamani da Mikah ne. Amma yanayin a yau, ya yi daidai da na zamanin Mikah domin haka kalmominsa sun shafi zamaninmu. Wannan zai bayyana yayin da muka bincika wasu taƙaitawar surori bakwai na littafin Mikah.
Abin da Taƙaitawar ke Bayyanawa
4. Mikah surori 1 zuwa 3 sun ba da waɗanne bayani?
4 Bari mu ɗan duba abubuwa da littafin Mikah ya ƙunsa. A sura 1, Jehovah ya fallasa tawayen Isra’ila da Yahuda. Domin tawayensu, za a halaka Isra’ila a yi wa Yahuda horo da zai kai har ƙofofin Urushalima. Sura ta 2 ta bayyana cewa masu arziki da kuma masu iko suna zalunta gajiyayyu da marasa taimako. Duk da haka, Allah ya yi alkawari. Za a tattara mutanen Allah cikin haɗin kai. Sura ta 3 ta ba da rahoto game da la’anar Jehovah bisa shugabannin ƙasar da kuma annabawa masu laifi. Shugabannin suna yin ha’inci wajen shari’a, annabawan kuma suna furta ƙarairai. Duk da haka, ruhu mai tsarki na Jehovah ya ƙarfafa Mikah ya sanar da hukuncin Jehovah da ke zuwa.
5. Wane labari ke cikin Mikah surori 4 da 5?
5 Sura ta 4 ta annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, dukan al’ummai za su je wajen dutse mai girma na gidan Jehovah domin ya koyar da su. Amma kafin hakan, Yahuda za ta tafi bauta a Babila, kuma Jehovah zai cece ta. Sura ta 5 ta bayyana cewa za a haifi Almasihu a Baitalahmi ta Yahuda. Shi zai ja-goranci mutanensa kuma ya cece su daga al’ummai masu tsananta musu.
6, 7. Waɗanne darussa ne suke cikin surori 6 da 7 na annabcin Mikah?
6 Mikah sura ta 6 ta rubuta tuhumar da Jehovah ya yi wa mutanensa kamar a lokacin shari’a. Menene ya yi da za su yi tawaye? Babu. Gaskiyar ita ce, farillansa cike suke da sanin ya kamata. Yana son masu bauta masa su yi gaskiya wajen shari’a, kirki da kuma filako sa’ad da suke tafiya tare da shi. Maimakon su yi haka, Isra’ila da Yahuda suka bi tafarkin tawaye kuma dole su fuskanci sakamakon haka.
7 A sura ta ƙarshe na annabcinsa, Mikah ya hukunta muguntar mutanen zamaninsa. Amma bai kasala ba, domin ya ƙuduri aniyar ya “jira” Jehovah. (Mikah 7:7) Littafin ya kammala da furcin tabbaci cewa Jehovah zai ji ƙan mutanensa. Tarihi ya nuna cewa wannan begen ya cika. A shekara ta 537 K.Z., sa’ad da horon Jehovah ga mutanensa ya cika, ya ji ƙan raguwar mutanen, ya mai da su ƙasarsu.
8. Ta yaya za ka taƙaita abubuwa da ke cikin littafin Mikah?
8 Lallai wannan sanarwa ce kyakkyawa Jehovah ya bayyana ta bakin Mikah! Wannan hurarren littafi ya yi tanadin misalai na gargaɗi game da yadda Allah yake bi da waɗanda suke da’awar suna bauta masa amma ba su da aminci. Ya yi annabci game da abubuwa da suke faruwa a yau. Kuma ya ba da gargaɗi na Allah game da yadda za mu bi da kanmu a wannan lokacin wahala don mu ƙarfafa begenmu.
Jehovah Ubangiji Mamallaki Yana Magana
9. Bisa Mikah 1:2, menene Jehovah zai yi?
9 Bari yanzu mu bincika littafin Mikah filla-filla. A Mikah 1:2, mu karanta: “Ku ji, ku al’ummai, ku dukanku; ku kasa kunne, ya duniya, da abin da ke ciki duka; bari Ubangiji Allah kuma ya zama shaida a kanku, Ubangiji daga haikali nasa mai-tsarki.” Idan kana raye a zamanin Mikah, waɗannan kalmomin babu shakka za su ja hankalinka. Hakika, sun jawo hankalinka a yau domin Jehovah yana magana ne daga haikalinsa mai tsarki kuma yana magana ne ba da Isra’ila da Yahuda ba kawai amma da mutane ne a ko’ina. A zamanin Mikah, mutane sun ƙyale Jehovah Ubangiji Mamallaki da daɗewa. Ba da daɗewa ba wannan zai canja. Jehovah ya ƙuduri aniya ya yi maganinsu.
10. Me ya sa kalmomin Mikah 1:2 ke da muhimmanci a gare mu?
10 Haka yake game da zamaninmu. Ru’ya ta Yohanna 14:18-20 ta nuna cewa Jehovah har ila yana magana daga haikalinsa mai tsarki. Ba da ɗadewa ba zai aikata, kuma ayyuka masu muhimmanci za su jijjiga ’yan Adam. A wannan karon, mugun “anab ta duniya” za a zuba cikin wajen matse ruwan anab na fushin Jehovah, domin cikakkiyar halakar zamanin Shaiɗan.
11. Menene kalmomin Mikah 1:3, 4 suke nufi?
11 Ka saurari abin da Jehovah zai yi. Mikah 1:3, 4 sun ce: “Ga shi, Ubangiji yana fitowa daga wurinsa, za ya sauko, ya taka maɗaukakan wurare na duniya. Duwatsu kuma za su narke daga ƙarƙashinsa, kwaruruka kuma za su tsagu, kamar kakin zuma a gaban wuta, kamar ruwa da an zubar da shi a magangari mai-zurfi.” Shin Jehovah zai bar wajen zamansa a samaniya ya sauko a zahiri ya tattake duwatsu da kuma filayen Ƙasar Alkawari? A’a. Ba ya bukatar ya yi haka. Zai mai da hankalinsa kawai ga duniya domin nufinsa ya cika. Bugu da ƙari, ba duniya ba ce ta zahiri, amma mutane da suke cikinta ne za su sha wahalar abubuwa da aka kwatanta. Sa’ad da Jehovah ya zabura, sakamakon zai kasance bala’i ga marasa aminci—a ce duwatsu sun narke kamar kyandir kuma girgizar ƙasa ta rabe filayen bibbiyu.
12, 13. Cikin jituwa da 2 Bitrus 3:10-12, me ke tabbatar da begenmu?
12 Kalmomin annabci na Mikah 1:3, 4 za su tuna maka da wani hurarren annabci na ayyukan bala’i da za su faɗo wa duniya. Yadda aka rubuta a 2 Bitrus 3:10, manzo Bitrus ya rubuta: “Ranar Ubangiji kamar ɓarawo za ta zo; a cikinta fa sammai za su shuɗe tare da ƙara mai-girma, rundunan kuma za su narke da ƙuna mai-zafi, duniya kuwa da ayyukan da ke cikinta za su ƙone.” Kamar annabcin Mikah, kalmomin Bitrus ba su shafi sama da duniya ta zahiri ba. Suna nuni ga ƙunci mai tsanani ne da yake zuwa bisa wannan zamani marar ibada.
13 Duk da zuwan wannan bala’i, Kiristoci za su iya dogara da abin da ke zuwa a nan gaba, yadda Mikah ya yi. Ta yaya? Ta wajen bin gargaɗin da yake cikin ayoyi na gaba na wasiƙar Bitrus. Manzon ya ce: “Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma? kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai!” (2 Bitrus 3:11, 12) Begenmu ga abin da ke zuwa a nan gaba zai tabbata idan muka kasance da zuciya mai biyayya kuma muka tabbata cewa halinmu mai tsarki ne kuma rayuwarmu ta cika da ayyukan ibada. Don mu tabbata da begenmu, dole mu tuna cewa ranar Jehovah za ta zo.
14. Me ya sa Isra’ila da Yahuda suka cancanci a yi musu horo?
14 Jehovah ya yi bayanin dalilin da ya sa mutanensa na dā suka cancanci a yi musu horo. Mikah 1:5 ta ce: “Sabili da laifin Yakubu a ke yin wannan duka, domin zunuban gidan Isra’ila kuma. Menene laifin Yakubu? ba Samariya ba ce? masujadai na Yahuda fa? ba Urushalima ba ne?” Jehovah ne dalilin wanzuwar Isra’ila da Yahuda. Duk da haka, sun yi masa tawaye, kuma tawayensu ya kai har cikin manyan biranensu, Samariya da Urushalima.
Ayyukan Mugunta Sun Yawaita
15, 16. Mutanen zamanin Mikah suna da laifin waɗanne ayyukan mugunta?
15 Misalin muguntar mutanen zamanin Mikah an kwatanta shi sarai a Mikah 2:1, 2: “Kaiton waɗannan da su ke tuna dabarar zamba, suna aika mugunta a bisa gadajensu! lokacinda gari ya waye su kan aikata shi, domin yana cikin ikon hannunsu. Su kan yi ƙyashin gonaki, su ƙwace su kuma; gidaje kuma, har su amshe su: su kan zalunci mutum da gidansa; i, har mutum da gadōnsa.”
16 Mutane masu haɗama suna kwanciya daddare suna ƙulla yadda za su ƙwace gonaki da gidajen maƙwabtansu. Da safe, sai su hanzarta su cika ƙulle-ƙullensu. Ba za su yi irin wannan muguntar ba idan sun tuna da alkawarin Jehovah. Dokar Musa ta yi shiri ta yi tanadin kāre fakiri. A cikin dokar, babu iyalin da zai yi hasarar gadōnsa dindindin ba. Amma, wannan bai dami waɗannan mutane masu haɗama ba. Sun yi watsi da kalmomin Leviticus 19:18, wadda ta ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”
17. Menene zai iya faruwa sa’ad da waɗanda suke da’awa suna bauta wa Allah suka sa abin duniya na farko a rayuwa?
17 Wannan ya nuna abin da zai iya faruwa sa’ad da mutane da suke da’awa suna bauta wa Allah suka ƙyale burinsu na ruhaniya suka fara neman abin duniya. Bulus ya yi wa Kiristoci na zamaninsa gargaɗi: “Waɗanda suna so su zama mawadata su kan fāɗa cikin jaraba da tarko da sha’awoyi dayawa na wauta da ɓarna, irin da kan dulmaya mutane cikin hallaka da lalacewa.” (1 Timothawus 6:9) Sa’ad da mutum ya mai da neman kuɗi burinsa na rayuwa, watau, yana bauta wa allah na ƙarya—Mammon, ko Arziki. Wannan allah na ƙarya ba ya ba da tabbataccen bege game da nan gaba.—Matta 6:24.
18. Menene zai faru da waɗanda suke son abin duniya a zamanin Mikah?
18 Mutane da yawa a zamanin Mikah sun koya ta hanya mai wuya cewa dogara bisa abin duniya wofi ne kawai. Bisa ga Mikah 2:4, Jehovah ya ce: “A cikin wannan rana za su ɗauki misali a kanku, su yi kuka da kuka mai-ban tausayi, su ce, Mun lalace sarai; yana sāke rabon mutanena; duba yadda ya raba shi da ni! ya rarraba ma tawaye karkaranmu.” Hakika, waɗanda suke ƙwace gidaje da gonaki za su yi hasarar gadōn nasu iyali. Za a kwashe su zuwa wata ƙasa, kuma abin da suka mallaka za su zama ganimar mutane ‘marasa aminci’ watau, mutanen al’ummai. Dukan wani begen arziki a nan gaba zai zama banza.
19, 20. Menene ya faru wa Yahudawa da suka dogara ga Jehovah?
19 Amma, begen waɗanda suka dogara ga Jehovah ba zai lalace ba. Jehovah ya kasance mai aminci da alkawarinsa ga Ibrahim da kuma Dauda, kuma ya ji ƙan mutane kamar su Mikah da suke ƙaunarsa kuma suka yi baƙin ciki domin warewar mutanensu daga Allah. Domin mutane masu adalci, a lokaci na Allah za a sake maido da su.
20 Hakan ya faru a shekara ta 537 K.Z., bayan Babila ta fāɗi kuma raguwar Yahudawa suka koma ƙasarsu. A wannan lokaci, kalmomin Mikah 2:12 ta samu cikarta ta farko. Jehovah ya ce: “Lallai sai in tattara dukanku, ya Yakubu; lallai zan tattara ringin Isra’ila; zan harhaɗa su kamar tumakin Bozrah; kamar garke cikin tsakiyar makiyayarsu, za su yi babban ɗumi saboda yawan taro.” Hakika, Jehovah mai ƙauna ne! Bayan ya hori mutanensa, ya ƙyale raguwarsu su komo su bauta masa a ƙasar da ya ba kakaninsu.
Kamani na Musamman a Zamaninmu
21. Yaya yanayi na zamanin yau ya yi kama da na zamanin Mikah?
21 Kamar yadda muka bincika surori biyu na farko na Mikah, yadda abubuwa suka yi daidai da yau suna burge ka ne? Kamar yadda yake a zamanin Mikah, mutane da yawa yanzu suna da’awar suna bauta wa Allah. Duk da haka, kamar Yahuda da Isra’ila, suna rabe kuma sun yi yaƙe-yaƙe tsakaninsu. Da yawa cikin masu arziki a Kiristendam sun zalunta fakirai. Shugabannin addinai suna ƙara ƙyale ayyukan da Littafi Mai Tsarki ya haramta. Babu mamaki da Kiristendam ba da daɗewa ba za ta kai ƙarshenta tare da sauran “Babila Babba,” daular duniya na addinin ƙarya! (Ru’ya ta Yohanna 18:1-5) Duk da haka, bin tafarkin zamanin Mikah Jehovah yana da amintattun bayinsa a duniya.
22. Waɗanne rukuni biyu suka sa begensu a Mulkin Allah?
22 A shekara ta 1919, amintattun shafaffun Kiristoci suka ware kansu daga Kiristendam kuma suka fara shelar bisharar Mulki ga dukan al’ummai. (Matta 24:14) Suka fara ta wajen neman raguwar Isra’ila ta ruhaniya. Sai aka fara tattara “waɗansu tumaki,” kuma rukuni biyun suka haɗu suka zama “garke ɗaya, makiyayi ɗaya.” (Yohanna 10:16) Ko da yake yanzu suna bauta wa Allah a ƙasashe 234, dukan waɗannan masu bauta wa Jehovah masu aminci da gaske suna da ‘haɗin kai.’ Kuma a yanzu, garken yana cike da ‘mutane,’ mata da yara. Begensu ba a kan wannan zamanin ba ne, amma a kan Mulkin Allah ne, wanda ba da jimawa ba zai kawo aljanna bisa duniya.
23. Me ya sa ka tabbata cewa begenka tabbatacce ne?
23 Game da amintattu masu bauta wa Jehovah, aya ta ƙarshe ta Mikah sura 2 ta ce: “Sarkinsu ya wuce gabansu, Ubangiji kuma a kansu.” Ka ga kanka a tsakanin masu tafiyar nasara, kana bin Sarkinka, Yesu Kristi, da kuma Jehovah kansa yana shugabanci? Idan haka ne, ka sani cewa kana hanyar zuwa nasara kuma begenka tabbatacce ne. Wannan zai bayyana sarai sa’ad da muka ƙara bincika taƙaitawar annabcin Mikah.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa Jehovah ya yanke shawara ya yi maganin Yahuda da Isra’ila a zamanin Mikah?
• Menene zai faru sa’ad da waɗanda suke da’awa suna bauta wa Allah suka saka abin duniya farko a rayuwa?
• Bayan mun bincika Mikah surori 1 da 2, me ya sa ka tabbata cewa begenka tabbatacce ne?
[Hoto a shafi na 3]
Annabcin Mikah zai iya ƙarfafa mu a ruhaniya
[Hotuna a shafi na 4]
Kamar raguwar Yahudawa a shekara ta 537 K.Z., Isra’ilawa ta ruhaniya da abokansu suna ɗaukaka bauta ta gaskiya