Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 4/1 pp. 14-19
  • Kiristoci Na Farko Da Dokar Musa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kiristoci Na Farko Da Dokar Musa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sabon Fahimi a Koyarwar Kirista
  • Wasu Sun Ci Gaba da Bin “Mai-Tsaron”
  • Bayan Jayayya—Aka Haɗa Kai!
  • Kiristoci Yahudawa Fa?
  • Ba Su Fahimci Batun da Sauri Ba
  • Yin Amfani da Darasin a Yau
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Dokar ‘Jehobah Cikakkiya Ce’
    Ka Kusaci Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 4/1 pp. 14-19

Kiristoci Na Farko Da Dokar Musa

“Shari’a ta zama mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi.”—GALATIYAWA 3:24.

1, 2. Yaya Isra’ilawa suka amfana da suka yi biyayya da Dokar Musa?

ASHEKARA ta 1513 K.Z., Jehovah ya ba Isra’ilawa tsarin dokoki. Ya gaya wa mutanen cewa idan sun yi masa biyayya, zai albarkace su kuma za su more rayuwa mai ma’ana na farin ciki.—Fitowa 19:5, 6.

2 Wannan tsarin Doka, da ake kira Dokar Musa, ko kuma kawai “shari’a” “tsatsarka ce, mai-adalci kuwa, tagari ce.” (Romawa 7:12) Ta ƙarfafa halaye masu kyau kamar su alheri, yin gaskiya, tarbiyya, da maƙwabtaka. (Fitowa 23:4, 5; Leviticus 19:14; Kubawar Shari’a 15:13-15; 22:10, 22) Dokar ta kuma motsa Yahudawa su ƙaunaci juna. (Leviticus 19:18) Bugu kan ƙari, ba za su yi cuɗanya da ko kuma su auri mata daga mutanen Al’ummai da ba sa ƙarƙashin Dokar ba. (Kubawar Shari’a 7:3, 4) Kamar “bango” da ya raba Yahudawa da mutanen Al’ummai, Dokar Musa ta sa mutanen Allah ba su ƙazanta a tunaninsu ba da kuma ayyukan arnanci.—Afisawa 2:14, 15; Yohanna 18:28.

3. Tun da yake babu wanda zai iya bin Dokar daidai, wane sakamako yake da shi?

3 Duk da haka, har Yahudawa da suke biyayya ba su iya bin Dokar Allah daidai ba. Jehovah yana bukatar abin da ya fi ƙarfinsu ne? A’a. Dalili ɗaya da ya sa aka ba Isra’ila Dokar “saboda ƙetaren doka” ne. (Galatiyawa 3:19) Dokar ta sa Yahudawa na gaskiya suka san cewa suna bukatar Mai Ceto. Sa’ad da wannan Ya zo, Yahudawa masu aminci suka yi murna. Cetonsu daga zunubi da mutuwa ya yi kusa!—Yohanna 1:29.

4. A wane azanci ne Dokar “mai-tsaronmu [ne] ga Kristi”?

4 An nufa Dokar Musa ta kasance shiri ne na ɗan lokaci. Da yake rubuta wa ’yan’uwa Kiristoci, manzo Bulus ya kwatanta shi da “mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi.” (Galatiyawa 3:24) A lokacin dā, mai-tsaro na raka yara zuwa makaranta kuma yana mai da su gida. Ba shi ba ne malamin; yana raka yara kawai zuwa wurin malamin. Haka nan ma, an shirya Dokar Musa ta kai Yahudawa masu jin tsoron Allah zuwa Kristi. Yesu ya yi alkawari cewa zai kasance da mabiyansa “kullayaumi har matuƙar zamani.” (Matta 28:20) Saboda haka, muddin aka kafa ikilisiyar Kirista, “mai-tsaron”—Dokar—zai zama babu amfani. (Romawa 10:4; Galatiyawa 3:25) Amma, wasu Yahudawa Kiristoci ba su fahimci muhimmiyar gaskiyar nan da nan ba. Saboda haka, sun ci gaba da yin biyayya da wasu farillai na Dokar bayan tashin Yesu daga matattu. Amma, wasu sun gyara tunaninsu. Ta yin haka, sun kafa mana misali mai kyau a yau. Bari mu ga yadda suka yi haka.

Sabon Fahimi a Koyarwar Kirista

5. Wane umurni aka ba Bitrus a wahayi, me ya sa ya yi mamaki?

5 A shekara ta 36 A.Z., Kirista manzo Bitrus, ya ga wahayi na ban mamaki. A lokacin, murya daga sama ta umurce shi ya yanka kuma ya ci tsuntsaye da dabbobi da Dokar ta ce ba su da tsabta. Bitrus ya yi mamaki! Bai taɓa “cin wani abu haram ko mai-ƙazanta ba daɗai.” Amma muryar ta gaya masa: “Abin da Allah ya tsarkake, kada kai ka maishe shi haram.” (Ayukan Manzanni 10:9-15) Maimakon manne wa Dokar, Bitrus ya gyara ra’ayinsa. Wannan ya sa ya sami fahimi game da nufe-nufen Allah sosai.

6, 7. Menene ya taimaki Bitrus ya kammala cewa zai iya yi wa mutane na Al’umma wa’azi, waɗanne ƙarin kammalawa mai yiwuwa ya yi?

6 Ga abin da ya faru. Mutane uku suka je gidan da Bitrus yake da zama, su gaya masa ya bi su zuwa gidan wani ɗan Al’umma mai tsoron Allah mai suna Karniliyus. Bitrus ya gayyaci waɗannan mutane cikin gida kuma suka shaƙata. Da yake ya fahimci ma’anar wannan wahayi, washegari Bitrus ya bi su zuwa gidan Karniliyus. A nan Bitrus ya ba da cikakkiyar shaida game da Yesu Kristi. A lokacin, Bitrus ya ce: “Hakika na gane Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowacce al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” Ba Karniliyus kaɗai ba ya ba da gaskiya ga Yesu amma har da danginsa da aminai sai “ruhu Mai-tsarki ya fāɗo ma dukan waɗanda suna jin magana.” Da ya fahimci cewa Jehovah ne ya kawo wannan al’amari haka, Bitrus ya “umurta a yi musu baftisma a cikin sunan Yesu Kristi.”—Ayukan Manzanni 10:17-48.

7 Menene ya taimaki Bitrus ya kammala cewa mutane na Al’umma da ba sa ƙarƙashin Dokar Musa yanzu za su iya zama mabiyan Yesu Kristi? Fahimi na ruhaniya. Tun da yake Allah ya nuna ya amince da na Al’umma da ba su yi kaciya ba, ya zuba ruhunsa a kansu, Bitrus ya gane cewa za a iya amincewa da su don baftisma. A wannan lokacin, Bitrus ya fahimci cewa Allah ba ya bukatar Kiristoci na Al’umma su bi farillan Dokar Musa kafin a yi musu baftisma. Idan kana rayuwa lokacin, za ka kasance da yardan rai kamar Bitrus ka gyara ra’ayinka?

Wasu Sun Ci Gaba da Bin “Mai-Tsaron”

8. Wane ra’ayi ne game da kaciya ya bambanta da na Bitrus da wasu Kiristoci na Urushalima suke yaɗawa, kuma me ya sa?

8 Bayan ya bar gidan Karniliyus, Bitrus ya tafi Urushalima. Labarin cewa mutane na Al’umma marasa kaciya sun “karɓi maganar Allah” ya kai ikilisiyar wajen, wasu almajirai Yahudawa sun damu game da batun. (Ayukan Manzanni 11:1-3) Ko da sun yarda cewa na Al’umma za su iya zama mabiyan Yesu, “waɗanda su ke na kaciya” suka nace cewa waɗannan mutane na al’ummai da ba Yahudawa ba dole su bi Dokar domin su sami ceto. A wata sassa, wuraren da mutane na Al’umma suke musamman, inda Yahudawa Kiristoci kalilan ne, kaciya ba batu ba ne na jayayya. Waɗannan ra’ayoyi biyu sun kasance wajen shekara 13. (1 Korinthiyawa 1:10) Wannan gwaji ne ga waɗancan Kiristoci na farko—musamman ga waɗanda suke na Al’umma da suke da zama a tsakanin Yahudawa!

9. Me ya sa yake da muhimmanci a warware batun kaciya?

9 Batun ya zo ƙarshensa a shekara ta 49 A.Z., sa’ad da Kiristoci daga Urushalima suka zo Antakiya ta Suriya, inda Bulus yake wa’azi. Suka soma koyar da cewa mutane na Al’umma da suka tuba ya kamata su yi kaciya bisa Doka. Aka yi rashin jituwa da jayayya ƙwarai tsakaninsu, da kuma tsakanin Bulus da Barnaba! Idan ba a warware wannan batu ba, wasu Kiristoci, na Yahudawa ko kuma daga mutane na Al’umma, babu shakka za su yi tuntuɓe. Saboda haka, aka yi shiri Bulus da wasu mutane kalilan suka je Urushalima suka gaya wa hukumar mulki ta Kirista ta warware batun dindindin.—Ayukan Manzanni 15:1, 2, 24.

Bayan Jayayya—Aka Haɗa Kai!

10. Waɗanne abubuwa hukumar mulki ta bincika kafin ta tsai da shawara game da matsayin mutane na Al’umma?

10 A taron da suka shirya, babu shakka wasu sun ce a yi kaciya wasu kuma sun ce kada a yi. Amma motsin zuciya bai yi nasara ba. Bayan an yi ta jayayya, manzanni Bitrus da Bulus suka kwatanta alamu da Jehovah ya yi tsakanin masu bi marasa kaciya. Sun yi bayani cewa Allah ya zuba ruhu mai tsarki a kan mutane na Al’umma da ba su yi kaciya ba. Wato, sun yi tambaya ne, ‘Ikilisiyar Kirista za ta ƙi waɗanda Allah ya amince da su ne?’ Sai almajiri Yaƙub ya karanta aya ta Nassi da ta taimaki dukan waɗanda suka halarta su fahimci nufin Jehovah a batun.—Ayukan Manzanni 15:4-17.

11. Wace shawara ce game da kaciya ba a bincika ba, kuma menene ya nuna cewa Jehovah ya albarkaci shawarar?

11 An mai da wa hukumar mulki hankali. Domin su Yahudawa ne za su ce a ci gaba da kaciya? A’a. Waɗannan maza masu aminci sun ƙuduri aniya su bi Nassosi da ja-gorar ruhu mai tsarki na Allah. Bayan sun ji muhimmiyar shaida, hukumar mulki ta yarda cewa babu amfani Kiristoci na Al’umma su yi kaciya a ƙarƙashin Dokar Musa. Sa’ad da ’yan’uwa suka ji game da wannan shawara, suka yi murna, kuma ikilisiyoyi suka soma “ƙaruwa kowace rana.” Waɗannan Kiristoci da suka bi ja-gora ta tsarin Allah aka albarkace su da amsa da ke bisa Nassosi. (Ayukan Manzanni 15:19-23, 28, 29; 16:1-5) Duk da haka, da akwai muhimmiyar tambaya da ba a amsa ba.

Kiristoci Yahudawa Fa?

12. Wace tambaya ce ba a amsa ba?

12 Hukumar Mulki ta nuna sarai cewa Kiristoci na Al’umma ba sa bukatar su yi kaciya. Kiristoci Yahudawa fa? Shawarar hukumar mulki ainihi ba ta amsa wannan ɓangaren tambayar ba.

13. Me ya sa ba daidai ba ne a ce kiyaye Dokar Musa wajibi ne domin a sami ceto?

13 Wasu Kiristoci Yahudawa da suke da “kishi bisa zancen shari’a” suka ci gaba da yi wa yaransu kaciya da kuma bin wasu abubuwa na Dokar. (Ayukan Manzanni 21:20) Wasu suka yi fiye da haka, suka nace wai wajibi ne Yahudawa Kiristoci su kiyaye Dokar domin su sami ceto. Wannan, kuskure ne ƙwarai. Alal misali, ta yaya Kirista zai miƙa dabba domin gafarar zunubai? Hadayar Kristi ta sa irin wannan hadaya ba ta da amfani kuma. Farillan Dokar da ta ce Yahudawa su guje cuɗanya ta kusa da mutane na Al’umma fa? Zai yi wuya sosai Kirista mai wa’azin bishara da himma ya kiyaye waɗannan hani kuma ya cika umurni na a koya wa mutane na Al’umma dukan abin da Yesu ya koyar. (Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 1:8; 10:28)a Ba abin da ya nuna cewa an sasanta wannan batun a taron da hukumar mulki ta yi. Duk da haka, ikilisiyar tana da taimako.

14. Wace ja-gora ce game da Dokar hurarrun wasiƙu na Bulus suka bayar?

14 Ja-gora ta zo, ba ta wasiƙa daga hukumar mulki ba, amma ta ƙarin hurarrun wasiƙu da manzanni suka rubuta. Alal misali, manzo Bulus ya aika da saƙo mai huɗubantarwa ga Yahudawa da mutane na Al’umma da suke da zama a Roma. A wasiƙarsa zuwa wajensu, ya yi bayani cewa Bayahude na gaske shi ne “wanda ke Bayahude a zuciya, . . . kaciya kuwa ta zuciya ce, cikin ruhu.” (Romawa 2:28, 29) A cikin wannan wasiƙar, Bulus ya ba da misali ya nuna cewa Kiristoci ba sa ƙarƙashin Doka. Ya ce mace ba za ta auri maza biyu a lokaci ɗaya ba. Amma, idan mijinta ya mutu, tana da ’yanci ta sake yin aure. Sai Bulus ya yi amfani da misalin, ya nuna cewa shafaffu Kiristoci ba za su kasance ƙarƙashin Dokar Musa kuma su zama na Kristi ba. Ya kamata su zama ‘matattu ga Dokar’ don su kasance cikin jituwa da Kristi.—Romawa 7:1-5.

Ba Su Fahimci Batun da Sauri Ba

15, 16. Me ya sa wasu Kiristoci Yahudawa suka kasa fahimtar batun game da Dokar, menene wannan ya nuna game da bukatar a kasance a faɗake a ruhaniya?

15 Maganar Bulus game da Dokar ba za a iya jayayya ba. To, me ya sa wasu Kiristoci Yahudawa suka kasa fahimtar batun? Abu ɗaya shi ne, ba su da fahimi na ruhaniya. Alal misali, sun ƙyale cin abinci mai ƙarfi na ruhaniya. (Ibraniyawa 5:11-14) Ba sa halartar taron Kirista a kai a kai. (Ibraniyawa 10:23-25) Wani dalili da ya sa wasu ba su fahimci batun ba domin irin Dokar ne kanta. An kafa ta ne a kan abubuwa da za a iya gani a taɓa, kamar su haikali da tsarin firistoci. Yana da sauƙi wanda ba shi da ruhaniya ya yi na’am da Dokar maimako ya yi na’am da ƙa’idodin Kiristanci masu zurfi, da ke game da al’amura da ba sa ganuwa.—2 Korinthiyawa 4:18.

16 Bulus ya lissafa wani dalili da ya sa wasu masu da’awar Kiristanci suke ɗokin bin Dokar a wasiƙarsa zuwa ga Galatiyawa. Ya yi bayani cewa waɗannan mutane suna so a daraja su, waɗanda suke cikin addini da yawancin mutane suke darajawa. Maimakon su kasance da yardan rai a san su da Kiristoci a jama’ar, suna son su shirka don su kasance ɓangaren jama’ar. Sun fi so su sami tagomashin mutane maimakon su sami amincewar Allah.—Galatiyawa 6:12.

17. Yaushe ne ra’ayi da ya dace game da kiyaye Dokar ya bayyana?

17 Kiristoci masu fahimi da suka yi nazarin rubuce-rubucen Bulus da wasu da Allah ya hure sun zo ga cikakkiyar kammala game da Dokar. Amma, sai a shekara ta 70 A.Z., ne duka Kiristoci Yahudawa suka karɓi ra’ayi da ya dace game da Dokar Musa. Wannan ya faru ne sa’ad da Allah ya ƙyale aka halaka Urushalima, haikalinta, da rubuce-rubuce game da tsarin firistocinta. Wannan ya sa bai yiwu ba a bi dukan fannoni na Dokar.

Yin Amfani da Darasin a Yau

18, 19. (a) Waɗanne halaye ya kamata mu kasance da su kuma waɗanne halaye dole mu guje musu domin mu kasance lafiyayyu a ruhaniya? (b) Menene misalin Bulus ya koya mana game da bin ja-gorar da muka samu daga ’yan’uwa da suka manyanta? (Dubi akwati a shafi na 18.)

18 Bayan ka bincika waɗannan aukuwa na dā can, wataƙila kana mamakin: ‘Da ina raye lokacin, yaya zan yi yayin da ake bayyana nufin Allah a hankali? Da zan manne wa ra’ayina ne game da Dokar? Ko zan jira ne sai fahimi da ya dace ya bayyana? Kuma sa’ad da aka sami fahimi da ya dace, zan yarda da shi da dukan zuciyata?’

19 Hakika, ba za mu san abin da da mun yi ba da muna raye a lokacin. Amma za mu iya tambayar kanmu: ‘Yaya nake ɗaukan bayanin fahimi na Littafi Mai Tsarki sa’ad da aka yi bayani game da su a yau? (Matta 24:45) Sa’ad da aka ba da ja-gora ta Nassi, ina ƙoƙari na yi amfani da shi, ina bin ba wasiƙar dokar ba amma ruhunta? (1 Korinthiyawa 14:20) Ina jiran Jehovah da haƙuri sa’ad da ba a amsa wasu tambayoyi na ba?’ Yana da muhimmanci mu yi amfani da kyau da abinci na ruhaniya da muke da shi a yau “domin kada mu zakuɗa.” (Ibraniyawa 2:1) Sa’ad da Jehovah yake tanadin ja-gora ta Kalmarsa, ruhunsa, da ƙungiyarsa ta duniya, bari mu saurara da kyau. Idan mun yi haka, Jehovah zai albarkace mu da rai marar matuƙa mai kawo farin ciki da gamsarwa.

[Hasiya]

a Sa’anda Bitrus ya ziyarci Antakiya ta Suriya, ya more cuɗanya mai daɗaɗawa da mutane na Al’umma masu bi. Amma, sa’ad da Kiristoci Yahudawa suka zo daga Urushalima, Bitrus “ya noƙe, ya ware kansa dabam, yana jin tsoron waɗanda ke na kaciya.” Lallai waɗannan mutane na Al’umma ba su ji daɗi ba ƙwarai sa’ad da manzon da suke daraja ya ƙi cin abinci da su.—Galatiyawa 2:11-13.

Yaya Za Ka Amsa?

• A wane azanci ne Dokar Musa take kamar “mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi”?

• Yaya za ka yi bayanin hanyoyi dabam dabam da Bitrus da “waɗanda su ke na kaciya” suka bi gyara a fahimi na gaskiya?

• Menene ka koya game da hanyar da Jehovah yake bayyana gaskiyar a yau?

[Box/Hoto a shafi na 18]

Bulus Ya Fuskanci Gwaji da Tawali’u

Bayan tafiye-tafiye na wa’azi, Bulus ya isa Urushalima a shekara ta 56 A.Z. A wajen, gwaji na jiransa. Labarin cewa yana koyar da cewa an daina amfani da Dokar ya kai ikilisiyar. Dattawa suna tsoron cewa Kiristoci Yahudawa sababbi za su yi tuntuɓe don yadda Bulus yake magana a kan batun Dokar, ƙila su kammala cewa Kiristoci ba sa daraja tsarin Jehovah. A cikin ikilisiyar, akwai Kiristoci Yahudawa huɗu da suka yi alkawari, wataƙila alkawari na Nazaranci. Dole su je haikali domin su cika farillai na alkawarin.

Dattawan suka gaya wa Bulus ya raka mutane huɗun zuwa haikalin kuma ya biya kuɗin da suka kashe. Bulus ya rubuta aƙalla wasiƙu biyu da ya yi bayani cewa ba a bukatar bin Dokar domin ceto. Amma, ya yi la’akari da lamirin wasu. Dā ya rubuta: ‘Ga waɗanda [suke] . . . ƙarƙashin doka na kasance ƙarƙashin doka . . . domin in ribato waɗanda suke ƙarƙashin doka.’ (1 Korinthiyawa 9:20-23) Ko da bai yi shirka ba game da muhimman ƙa’idodi na Nassi, Bulus ya ji zai iya bin shawarar dattawan. (Ayukan Manzanni 21:15-26) Ba laifi ba ne ya yi hakan. Ba za a ce shirin yin alkawari ba daga nassi ba ne, ana kuma amfani da haikali don tsarkakkiyar bauta ce, ba don bautar gumaka ba. Domin kada a ba da dalilin tuntuɓe, Bulus ya yi yadda dattawa suka gaya masa. (1 Korinthiyawa 8:13) Babu shakka, wannan ya bukaci Bulus ya kasance da tawali’u, abin da yake sa mu daraja shi.

[Hoto a shafi nas 16, 17]

Na wasu shekaru, ra’ayoyi dabam dabam game da Dokar Musa ya kasance tsakanin Kiristoci

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba