Me Ya Sa Za Ka Yi Baftisma?
“Ku tafi . . . ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma.”—Matta 28:19.
1, 2. (a) Cikin waɗanne yanayi ne aka yi wa wasu baftisma? (b) Waɗanne tambayoyi suka taso game da baftisma?
SARKIN Farankisawa Charlemagne, ya tilasta wa dukan ’yan Saxon da ya ci a yaƙi su yi baftisma a shekara ta 775-77 A.Z. “Ya tilasta musu juyowa zuwa Kiristanci,” in ji ɗan tarihi John Lord. Hakazalika, sarkin Rasha Vladimir na I, bayan da ya auri gimbiyar Orthodox a shekara ta 987 A.Z., ya tsai da shawarar cewa dukan talakawansa tilas su zama ‘Kirista.’ Ya umurci a yi wa jama’arsa baftisma tare—a bakin ransu in sun ƙi!
2 Irin wannan Baftisma daidai take kuwa? Tana da wata ma’ana ta gaske? Kowa ne kawai za a yi wa baftisma?
Baftisma—Yaya Ake Yinta?
3, 4. Me ya sa yafawa ko kuma zuba ruwa a kai ba baftisma ba ce da ta dace ta Kirista?
3 Sa’ad da Charlemagne da Vladimir na I suka tilasta wa mutane su yi baftisma, abin da waɗannan sarakuna suka yi bai jitu ba da Kalmar Allah. Hakika, babu amfani idan baftisma ta ƙunshi yafa ruwa, zuba ruwa a ka, ko ma a nitsar da mutanen da ba a koyar da su gaskiyar Nassi ba.
4 Ka yi la’akari da abin da ya faru yayin da Yesu na Nazarat ya je wajen Yohanna Mai Baftisma a shekara ta 29 A.Z. Yohanna yana yi wa mutane baftisma cikin Kogin Urdun. Sun zo wajensa ne da yarda ransu don a yi musu baftisma. Ya sa su tsaya ne kawai a cikin Urdun yayin nan ya zuba ɗan ruwa a kansu ko kuma ya yayyafa musu ruwa? Me ya faru lokacin da Yohanna ya yi wa Yesu baftisma? Matta ya ba da labari cewa bayan an yi wa Yesu baftisma “ya fita nan da nan daga cikin ruwa.” (Matta 3:16) Yana cikin ruwan, bayan an nitsar da shi cikin Kogin Urdun. Hakanan, aka yi wa Habashin bābān baftisma a “wani ruwa.” Ana bukatar irin wannan babban ruwan, domin baftismar Yesu da na almajiransa ta ƙunshi nitsarwa gabaki ɗaya.—Ayukan Manzanni 8:36.
5. Ta yaya ne Kiristoci na farko suka yi wa mutane baftisma?
5 Kalmomin Helenanci da aka fassara “yi baftisma,” “baftisma,” da sauransu, na nuni ga nitsarwa, ko kuma tsomawa cikin ruwa. Smith’s Bible Dictionary ya ce: “Baftisma da ke daidai kuma a zahiri tana nufin nitsarwa.” Wasu fassara na Littafi Mai Tsarki sun ambaci “Yohanna mai nitsarwa” da kuma “Yohanna mai tsomawa.” (Matta 3:1, Rotherham; Diaglott.) History of the Christian Religion and Church, During the Three First Centuries na Augustus Neander ya ce: “Ainihi ana yin baftisma ta wajen nitsarwa ne.” Wani sharhi na harshen Faransa Larousse du XXe Siècle (Paris, 1928) ya ce: “Kiristoci na farko an yi musu baftisma ta wajen nitsar da su a duk inda aka samu ruwa.” Littafin New Catholic Encyclopedia ya ce: “Tabbas yake cewa Baftisma a Coci na farko ta wurin nitsarwa ne.” (1967, Littafi na II, shafi na 56) Saboda haka a yau, yin baftisma na Mashaidin Jehovah mataki ne na yardan rai da ya ƙunshi nitsarwa gabaki ɗaya a cikin ruwa.
Sabon Dalilin Yin Baftisma
6, 7. (a) Mecece manufar baftismar da Yohanna ya yi wa mutane? (b) Menene sabon abu a baftisma ta mabiyan Yesu?
6 Baftismar da Yohanna ya yi manufarta ta bambanta da wadda mabiyan Yesu suka yi. (Yohanna 4:1, 2) Yohanna ya yi wa mutane baftisma alamar tubarsu daga zunubansu a kan Doka.a (Luka 3:3) Amma akwai wani sabon abu cikin baftismar mabiyan Yesu. A Fentakos na shekara ta 33 A.Z., manzo Bitrus ya aririci masu sauraronsa: “Ku tuba, a yi ma kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi zuwa gafarar zunubanku.” (Ayukan Manzanni 2:37-41) Ko da yake yana zance ne da Yahudawa da shigaggu, ba zancen baftisma domin nuna alamar tuba a kan Doka Bitrus yake yi ba; ba ya kuma nufin cewa baftisma cikin sunan Yesu yana nufin wanke zunubai.—Ayukan Manzanni 2:10.
7 A lokacin, Bitrus ya yi amfani da “maƙullai na mulki” na farko. Domin me? Domin ya bayyana wa masu sauraronsa sani game da zarafi na shiga Mulkin sama. (Matta 16:19) Tun da Yahudawan sun ƙi Yesu Almasihu, tuba da kuma kasancewa da bangaskiya cikinsa sabon abu ne kuma abu ne muhimmi a biɗa da kuma samun gafarar Allah. Suna iya ba da tabbaci a fili na wannan bangaskiyar ta wajen ƙyale a nitsar da su a ruwa cikin sunan Yesu Kristi. A wannan hanyar ne za su nuna alamar keɓe kansu ga Allah ta wurin Kristi. Dole ne dukan waɗanda suke son samun amincewar Allah a yau su kasance da irin wannan bangaskiyar, su keɓe kansu ga Jehovah Allah, kuma su yi baftisma ta Kirista alamar keɓe kai babu ragi ga Allah Mafi Girma.
Ana Bukatar Cikakken Sani
8. Me ya sa ba kowa ne ke isa a yi masa baftisma ta Kirista?
8 Ba kowa ne ya isa a yi masa baftisma ta Kirista ba. Yesu ya umurci mabiyansa: “Ku tafi . . . , ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Kafin su yi baftisma, dole a ‘koyar [da mutane] su kiyaye dukan iyakar abin da Yesu ya umurci almajiransa.’ Saboda haka, baftismar da ake tilasta wa waɗanda ba su da imani bisa cikakken sanin Kalmar Allah babu amfani kuma ya saɓa wa aikin da Yesu ya ba wa mabiyansa na gaskiya.—Ibraniyawa 11:6.
9. Menene yake nufi a yi baftisma “cikin sunan Uba”?
9 Menene yake nufi a yi baftisma“cikin sunan Uba”? Yana nufin cewa mai son ya yi baftismar ya fahimci matsayin Ubanmu na samaniya da kuma ikonsa. Ta haka, ana ɗaukaka Mahaliccinmu, “Maɗaukaki bisa dukan duniya,” kuma Mamallakin Dukan Halitta.—Zabura 83:18; Ishaya 40:28; Ayukan Manzanni 4:24.
10. Menene yin baftisma ‘cikin sunan Ɗan’ ke nufi?
10 Yin baftisma‘cikin sunan Ɗan’ na nufin fahimtar matsayin Yesu da kuma ikonsa na Ɗan Allah makaɗaici. (1 Yohanna 4:9) Waɗanda suka cancanci a yi musu baftisma sun amince, Yesu shi ne wanda ta wurinsa Allah ya yi tanadin “fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28; 1 Timothawus 2:5, 6) Waɗanda za su yi baftisma dole ne su fahimci “mafificiyar ɗaukaka” da Allah ya ɗaukaka Ɗansa da ita.—Filibbiyawa 2:8-11; Ru’ya ta Yohanna 19:16.
11. Menene yin baftisma ‘cikin sunan ruhu mai tsarki’ ke nufi?
11 Mecece manufar baftisma ‘cikin sunan ruhu mai tsarki’? Wannan na nufin cewa mai yin baftismar ya fahimci cewa ruhu mai tsarki ne ikon aiki na Jehovah, da yake amfani da shi a hanyoyi da yawa cikin jituwa da nufinsa. (Farawa 1:2; 2 Samu’ila 23:1, 2; 2 Bitrus 1:21) Waɗanda suka isa a yi musu baftisma sun fahimci cewa ruhu mai tsarki na taimakonsu su fahimci “zurfafa na Allah,” don su yi aikin wa’azi na Mulki, kuma su ba da ’ya’yan ruhu na “ƙauna ne, farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.”—1 Korinthiyawa 2:10; Galatiyawa 5:22, 23; Joel 2:28, 29.
Muhimmancin Tuba da Juyowa
12. Yaya ne baftisma ta Kirista take da alaƙa da tuba?
12 Baftisma da Allah ya amince da ita alama ce da take da alaƙa da tuba, a batun Yesu mutum marar zunubi ne kawai ya bambanta. Sa’ad da muka tuba, mukan yi nadama ko kuma mukan yi baƙin ciki, a kan wani abin da muka yi ko kuma muka kasa yi. Yahudawa na ƙarni na farko da suke son su faranta wa Allah rai dole su tuba daga zunubansu ga Kristi. (Ayukan Manzanni 3:11-19) Wasu masu bi daga Al’ummai cikin Koranti suka tuba daga fasikanci, bautar gumaka, sata, da wasu zunubai masu tsanani. Domin tubarsu, aka “wanke” su cikin jinin Yesu; aka “tsarkake,” ko kuma aka ware su domin hidimar Allah; kuma aka ‘tsarkake’ su cikin sunan Kristi kuma da ruhu mai tsarki. (1 Korinthiyawa 6:9-11) Tuba muhimmin mataki ne na samun lamiri mai kyau da kuma sauƙi da Allah ke bayarwa daga alhakin zunubi.—1 Bitrus 3:21.
13. Game da baftisma, me juyowa ta ƙunsa?
13 Dole ne mu juyo kafin mu yi baftisma mu zama Mashaidin Jehovah. Juyowa abin da duk wanda ya tsai da shawarar zai bi Kristi Yesu da zuciya ɗaya zai yi ne da yardan rai. Irin waɗannan mutane sun ƙi mummunar tafarkinsu kuma sun ƙudiri aniyar yin abin da ke daidai a idanun Allah. A cikin Nassosi, aikatau na Ibrananci da na Helenanci da suke da ma’ana ta juyowa suna da ma’anar juya baya, sake juyawa. Wannan yana nufin juyowa daga mummunar hanya zuwa ga Allah. (1 Sarakuna 8:33, 34) Juyowa na bukatar ‘ayyuka waɗanda sun cancanci tuba.’ (Ayukan Manzanni 26:20) Tana bukatar mu yi watsi da bautar ƙarya, mu yi aiki daidai da dokokin Allah, kuma mu bauta wa Jehovah shi kaɗai. (Kubawar Shari’a 30:2, 8-10; 1 Samu’ila 7:3) Juyowa na kawo canji a tunaninmu, nufi, da kuma mutuntaka. (Ezekiel 18:31) Mun ‘juyo’ sa’ad da muka sake munanan halayen da sabon hali.—Ayukan Manzanni 3:19; Afisawa 4:20-24; Kolossiyawa 3:5-14.
Ana Bukatar Keɓe Kai da Zuciya Ɗaya
14. Menene keɓewar kai na mabiyan Yesu yake nufi?
14 Dole ne kuma mabiyan Yesu su keɓe kai ga Allah da zuciya ɗaya kafin su yi baftisma. Keɓewa na nufin a ware domin tsarkaken nufi. Wannan mataki yana da muhimmanci ƙwarai da ya kamata mu gaya wa Jehovah shawararmu na bauta masa shi kaɗai har abada, cikin addu’a. (Kubawar Shari’a 5:9) Hakika, keɓe kanmu ba ga aiki ba ne ko kuma ga wani mutum amma ga Allah ne kansa.
15. Me ya sa ake nitsar da waɗanda suke son su yi baftisma?
15 Yayin da muka keɓe kanmu ga Allah ta wurin Kristi, muna furta ƙudurinmu ne mu yi amfani da ranmu a yin nufin Allah yadda yake a cikin Nassosi. Alamar wannan keɓewar ce, ake nitsar da waɗanda suke son su yi baftisma cikin ruwa, yadda aka yi wa Yesu baftisma cikin Kogin Urdun alamar ba da kansa ga Allah. (Matta 3:13) Abin lura ne cewa Yesu ya yi addu’a a wannan muhimmin lokaci.—Luka 3:21, 22.
16. Ta yaya za mu nuna farin cikinmu yadda ya dace sa’ad da muka ga mutane za su yi baftisma?
16 Baftismar Yesu lokaci ne na natsuwa amma kuma na farin ciki. Haka ma yake da baftisma ta Kirista na zamanin yau. Yayin da muka ga mutane suna nuna alamar keɓe kansu ga Allah, muna nuna farin cikinmu a tafa hannu da daraja da kuma yaba musu da kyau. Amma ya kamata a guji yin sowa, fito, da sauransu domin tsarkakkar wannan nuna bangaskiya. Mu nuna farin cikinmu ta hanya mai daraja.
17, 18. Me ke taimakawa a sani ko mutum ya isa a yi masa baftisma?
17 Ba kamar waɗanda suke yafa wa jarirai ruwa ba ko masu tilasta wa jama’a da ba a koyar da su Nassosi ba su yi baftisma, Shaidun Jehovah ba sa tilasta wa kowa yin baftisma. Hakika ba sa yi wa waɗanda ba su ƙware ba a ruhaniya baftisma. Kafin mutum ya zama mai wa’azin bishara marar baftisma, dattawa Kiristoci za su tabbata cewa mutumin ya fahimci muhimman koyarwan Littafi Mai Tsarki, ya yi rayuwa daidai da su, kuma ya ba da tabbatacciyar amsa ga tambayar nan, “Kana son ka zama Mashaidin Jehovah?”
18 A yawancin yanayi, mutanen da suke shagala cikin aikin wa’azi na Mulki da suke furta burinsu a yi musu baftisma, dattawa Kiristoci sukan yi mahawara da su, su tabbata cewa su masu bi ne da sun keɓe kansu ga Jehovah kuma sun cika farillan Allah don yin baftisma. (Ayukan Manzanni 4:4; 18:8) Yadda suka amsa tambayoyi fiye da 100 a kan koyarwan Littafi Mai Tsarki yana taimakon dattawan su sani ko waɗanda suke ba da amsar sun cika farillan Nassi na nitsarwa. Wasu ba su ƙware ba saboda haka ba a yarda su yi baftisma ta Kirista ba.
Akwai Abin da Ke Hana Ka Ne?
19. Game da Yohanna 6:44, su wa za su zama magāda tare da Yesu?
19 Mutane da yawa da aka tilasta musu su yi baftisma ƙila an gaya musu za su sama idan suka mutu. Amma game da mabiyansa, Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Jehovah ya riga ya jawo magādan Mulki na samaniya da Kristi 144,000. Baftisma da ake tilasta bai taɓa sa wani ya cancanta ba zuwa wannan wuri mai ɗaukaka cikin tsarin Allah.—Romawa 8:14-17; 2 Tassalunikawa 2:13; Ru’ya ta Yohanna 14:1.
20. Me zai iya taimakon wasu da ba su yi baftisma ba tukun?
20 Tun a tsakiyar shekarun 1930 musamman, babban garke da suke da begen su tsira daga “babban tsananin” kuma su rayu a duniya har abada sun haɗu cikin rukunin “waɗansu tumaki.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14; Yohanna 10:16) Sun ƙware a yi musu baftisma domin sun sa rayuwarsu ta jitu da Kalmar Allah kuma suna ƙaunarsa da ‘dukan zuciya, rai, ƙarfi, da kuma azanci.’ (Luka 10:25-28) Ko da yake wasu mutane sun fahimci cewa Shaidun Jehovah suna ‘bauta wa Allah cikin ruhu da gaskiya,’ ba su bi misalin Yesu ba tukuna su nuna a fili tabbacin sahihiyar ƙauna da bauta wa Jehovah shi kaɗai ta wurin yin baftisma. (Yohanna 4:23, 24; Kubawar Shari’a 4:24; Markus 1:9-11) Sahihiyar addu’a kuma takamammiya game da wannan muhimmin mataki zai taimake su a motsa su da gaba gaɗi su bi Kalmar Allah daidai, su keɓe kansu babu ragi ga Jehovah Allah, kuma a yi musu baftisma.
21, 22. Domin waɗanne dalilai ne wasu suke ƙin keɓe kai da yin baftisma?
21 Wasu suna ƙin keɓe kai da yin baftisma domin sun shagala cikin harkokin duniya ko kuma biɗan dukiya da ya sa ba su da lokaci don abubuwa na ruhaniya. (Matta 13:22; 1 Yohanna 2:15-17) Lallai za su yi farin ciki idan suka canja ra’ayoyinsu da makasudi! Kusantar Jehovah zai sa su wadata a ruhaniya, ya taimake su su kawar da alhini, kuma ya kawo musu salama da gamsuwa da sakamakon yin nufin Allah ne.—Zabura 16:11; 40:8; Misalai 10:22; Filibbiyawa 4:6, 7.
22 Wasu suna cewa suna ƙaunar Jehovah amma ba sa son su keɓe kansu kuma su yi baftisma domin suna jin a ta haka ne za su iya guje wa ɗaukan hakki. Amma kowa dole ya ba da lissafi ga Allah. Muna da hakki yayin da muka ji maganar Jehovah. (Ezekiel 33:7-9; Romawa 14:12) ‘Mutane zaɓaɓu,’ Isra’ilawa na dā sun kasance cikin al’umma da ta keɓe kai ga Jehovah, saboda haka suna da hakkin bauta masa da aminci cikin jituwa da dokokinsa. (Kubawar Shari’a 7:6, 11) Babu wanda aka haifa cikin wannan al’ummar a yau, amma idan mun sami cikakkiyar koyarwa ta Nassi, muna bukatar mu aikata cikin bangaskiya.
23, 24. Wane tsoro ne bai kamata ya sa mutum ya ja da baya ba daga yin baftisma?
23 Wasu suna tsoron cewa ba su da isashen ilimi sai su ja da baya a yin baftisma. Duk da haka, akwai abubuwa da yawa da dukanmu za mu koya ‘mutane ba za su iya bincika aikin Allah na gaskiya ba da ya yi tun farko har ƙarshe.’ (Mai-Wa’azi 3:11) Ka yi la’akari da Habashi bābān. Shigagge ne, yana da ɗan sanin Nassosi, amma ba zai iya amsa dukan tambayoyi ba game da nufe-nufen Allah. Bayan da ya koyi tanadin Jehovah don ceto ta wurin fansar hadaya, bābān nan da nan ya yi baftisma a ruwa.—Ayukan Manzanni 8:26-38.
24 Wasu suna jinkirin keɓe kai ga Allah domin suna tsoron kasawa. Monique ’yar shekara 17 ta ce: “Na yi ta jan baya daga baftisma da tsoron ba zan iya cika hakkin keɓe kaina ba.” Amma, idan muka dogara ga Jehovah da dukan zuciyarmu, ‘zai kiyaye tafarkinmu.’ Zai taimake mu mu ci gaba da “tafiya cikin gaskiya” mu bayinsa masu aminci da suka keɓe kai.—Misalai 3:5, 6; 3 Yohanna 4.
25. Waɗanne tambayoyi muke bukatar bincikawa?
25 Domin cikakkiyar dogara ga Jehovah da kuma ƙauna daga zuciya gare shi, kowacce shekara dubbai suna motsawa su keɓe kansu kuma su yi baftisma. Kuma da gaske dukan bayin Allah da suka keɓe kai gare shi suna son su kasance da aminci gare shi. Har ila, muna cikin miyagun lokatai, kuma muna fuskantar gwajin bangaskiya iri-iri. (2 Timothawus 3:1-5) Me za mu iya yi don mu cika keɓe kanmu ga Jehovah? Za a bincika wannan a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Tun da yake Yesu ba mai zunubi ba ne, bai yi baftisma domin nuna tuba ba. Baftismarsa alamar ba da kansa ne ga Allah ya yi nufin Ubansa.—Ibraniyawa 7:26; 10:5-10.
Ka Tuna?
• Yaya ake yin baftisma ta Kirista?
• Wane sani mutum ke bukata don a yi masa baftisma?
• Waɗanne matakai ke kai wa ga baftisma ta Kirista na gaskiya?
• Me ya sa wasu ke ja da baya daga yin baftisma, amma yaya za a iya taimakonsu?
[Hotuna a shafi na 25]
Ka san abin da yake nufi a yi baftisma ‘cikin sunan Uba, da na Ɗa, da kuma na ruhu mai tsarki’?