Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 8/1 p. 7
  • Allah Ya Share Hawayenta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Ya Share Hawayenta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance Da Ƙarfi A Ruhaniya Yayin Da Kake Kula Da Dangi Marar Lafiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Matsalolin Tattalin Arziki​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi
    Karin Batutuwa
  • Ka Ba Ni Karfin Hali
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 8/1 p. 7

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

Allah Ya Share Hawayenta

MUTANE da suka canja rayuwarsu suka jitu da dokoki da ƙa’idodin Jehovah an albarkace su sosai. Ko da yin canje-canje da ya kamata ba kullum ne yake da sauƙi ba, ana ba da taimako da ƙarfafa. (Zabura 84:11) Labari na gaba daga Kudu maso gabashin Asiya ya nuna haka.

Yayin da take hutu, wata Mashaidiya daga Faransa ta yi wa wata mai kanti mai suna Kima magana game da nufin Jehovah game da duniya. Ta kuma ba Kim littafin nan Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna A Duniya. Da take duba littafin, sai Kim ta ga kalmomin, “za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) “Wannan aya ta motsa ni sosai,” in ji Kim. “Gani ina farin ciki a kanti, wa zai san cewa daga na isa gida da yamma, zan yi ta kuka har na yi barci?” Da take bayyana dalilin baƙin cikinta, ta ce: “Ina zama da wani mutum shekara 18 yanzu kuma ina baƙin ciki domin ya ƙi ya aure ni. Ina son in daina irin wannan rayuwa, amma ba ni da ƙarfin zuciya da zan yi haka domin mun daɗe muna tare.”

Ba da daɗewa ba bayan haka, Kim ta yarda wata Mashaidiyar Jehovah mai suna Linh ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. “Ina son in yi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa,” in ji Kim. “Alal misali, na daina bauta wa kakannina, ko da yake wannan ya jawo hamayya daga iyalina. Ƙari ga haka, na yi ƙoƙari mu yi aure, amma abokina ya ƙi. A wannan lokaci mai wuya, Mashaidiyar daga Faransa ta ci gaba da aiko mini littattafai na Littafi Mai Tsarki, kuma Linh tana ƙarfafa ni. Haƙuri da taimako mai kyau na waɗannan ’yan’uwa mata ya taimake ni na ci gaba har na ga ainihin halin abokina. Na gane cewa yana da ‘mata’ 5 da yara 25! Wannan ya ba ni ƙarfin zuciya na bar shi.

“Barin babban gida mai kyau zuwa ƙaramin gida ba shi da sauƙi. Ban da haka ma, abokina na dā ya nace in zo in sake zama da shi, ya yi burgar cewa zai zuba mini ruwan batir in na ƙi. Da taimakon Jehovah, na iya yin abin da yake daidai.” Kim ta ci gaba da ci gaba kuma a ƙarshe ta yi baftisma a watan Afrilu 1998. Ƙari ga haka, ƙannenta mata biyu da ɗanta mai shekara goma sha suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah.

“Ina tunani cewa rayuwa za ta zama banza,” in ji Kim. “Amma, yau, ina farin ciki, kuma ba na kuka cikin dare. Jehovah ya riga ya share hawaye daga idanuna.”

[Hasiya]

a An canja sunayen.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba