Ka Himmantu Ga Ruhu Ka Rayu!
“Himmantuwar ruhu rai ne.”—ROMAWA 8:6.
1, 2. Wane bambanci Littafi Mai Tsarki ya nuna tsakanin “jiki” da “ruhu”?
BA SHI da sauƙi a riƙe ɗabi’a mai tsarki a gaban Allah a tsakanin lalaccaciyar jama’a da ke ɗaukaka sha’awa irin ta halin mutuntaka. Amma, Nassosi sun nuna bambanci tsakanin “jiki” da “ruhu,” wannan yana bayyana dalla-dalla sakamakon mutum ya bar kansa jiki na zunubi ya rinjaye shi da kuma albarkar bin tasirin ruhu mai tsarki na Allah.
2 Alal misali, Yesu Kristi ya ce: “Ruhu ne yana rayarwa; jiki ba ya amfana komi ba: zantattuka waɗanda na faɗa maku ruhu ne, da rai kuma” (Yohanna 6:63) Zuwa ga Kiristoci a cikin Galatiya, manzo Bulus ya rubuta: “Jiki yana sha’awa gāba da Ruhu; Ruhu kuma gāba da jiki; gama waɗannan biyu gāba su ke da junansu.” (Galatiyawa 5:17) Bulus kuma ya ce: “Wanda ya shuka ga jiki nasa, daga wurin jiki za ya girbe ruɓa; amma wanda ya shuka ga Ruhu, daga wurin Ruhu za ya girbe rai na har abada.”—Galatiyawa 6:8.
3. Menene ake bukata don a ’yantu daga munanan sha’awoyi da nufe-nufe?
3 Ruhu mai tsarki na Jehovah—ikon aikinsa—zai iya kawar da “sha’awoyi na jiki” da kyau da kuma iko da ke kawo ɓarna ga jikinmu na zunubi. (1 Bitrus 2:11) Don mu yantu daga garkuwar munanan nufe-nufe, yana da muhimmanci mu samu taimakon ruhun Allah, domin Bulus ya rubuta: “Himmantuwar jiki mutuwa ce: amma himmantuwar ruhu rai ne da lafiya.” (Romawa 8:6) Menene ake nufi da a himmanta ruhu?
“Himmantuwar Ruhu”
4. Menene “himmantuwar ruhu” take nufi?
4 Yayin da Bulus ya yi rubutu game da “himmantuwar ruhu,” ya yi amfani da kalmar Helenanci da ke nufin “hanyar tunani, kafa zuciya, . . . maƙasudi, buri, yin fama.” Fi’ili mai kama da wannan yana nufin “yi tunani, mai da hankali a wata hanya.” Da haka himmantu ga ruhu yana nufin ikon aikin Jehovah ya ja-goranci, rinjayi, kuma ya motsa mu. Yana nufin cewa da yardan rai muna barin tunaninmu, nufe-nufe, da buri su zo ƙarƙashin cikakken rinjaya na ruhu mai tsarki na Allah.
5. Yaya yawan yadda ya kamata mu ba da kai ga rinjayar ruhu mai tsarki?
5 Bulus ya nanata yawan yadda ya kamata mu ba da kai ga tasirin ruhu mai tsarki lokacin da ya yi maganar zama ‘bayi ta ruhu.’ (Romawa 7:6) Bisa bangaskiyarsu cikin hadayar fansa ta Yesu, an ’yantar da Kiristoci daga ikon zunubi da haka suka “mutu” ga yanayinsu na dā da yake su bayinsa ne. (Romawa 6:2, 11) Waɗanda ta alama suka mutu a hanyar nan har ila suna da rai a zahiri kuma suna da ’yanci yanzu su bi Kristi, sun zama “bayin adalci.”—Romawa 6:18-20.
Juyawa ta Ban Mamaki
6. Wane canji ne waɗanda suka zama “bayin adalci” suka yi?
6 Canjawa daga zaman “bayin zunubi” zuwa bauta wa Allah na “bayin adalci,” abin ban mamaki ne da gaske. Game da wasu da suka yi irin wannan canjin, Bulus ya rubuta: “An wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Kristi, da kuma ruhun Allahnmu.”—Romawa 6:17, 18; 1 Korinthiyawa 6:11.
7. Me ya sa yake da muhimmanci a kasance da ra’ayin Jehovah game da batutuwa?
7 Don mu ga irin wannan canji ta ban mamaki, muna bukatar da farko mu koya ra’ayin Jehovah game da batutuwa. Ƙarnuka da suka shige, Dauda mai Zabura ya roƙi Allah ƙwarai da gaske: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka . . . Ka bishe ni cikin gaskiyarka, ka koya mini.” (Zabura 25:4, 5) Jehovah ya saurari Dauda, kuma zai amsa irin wannan addu’a ga bayinsa na zamanin yau ma. Tun da yake hanyoyin Allah da gaskiyarsa suna da tsabta da kuma tsarki, yin bimbini a kansu zai taimake mu idan an jarabe mu biya bukatar sha’awace-sha’awace na halin mutuntaka marasa tsarki.
Muhimmin Matsayin Kalmar Allah
8. Me ya sa wajibi ne mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki?
8 Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, aikin ruhunsa ne. Da haka, hanya ɗaya da take da muhimmanci mu yarda wannan ruhu ya yi aiki a kanmu shi ne ta karatu da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki—idan zai yiwu kowacce rana. (1 Korinthiyawa 2:10, 11; Afisawa 5:18) Cika azancinmu da zuciyarmu da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da kuma mizanai zai taimake mu mu jure farmaki a kan ruhaniyarmu. Hakika, yayin da jarabar lalata ta taso, ruhun Allah zai sa mu tuna Nassi da mizanai da za su ƙarfafa shawararmu na mu aikata daidai da nufin Allah. (Zabura 119:1, 2, 99; Yohanna 14:26) Saboda haka, ba za a ruɗe mu mu bi munanan tafarki ba.—2 Korinthiyawa 11:3.
9. Yaya nazarin Littafi Mai Tsarki yake ƙarfafa ƙudurinmu na adana dangantakarmu da Jehovah?
9 Yayin da muka ci gaba da nazarinmu na Nassosi da gaske kuma da ƙwazo tare da taimakon littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki, ruhun Allah yana taɓa azancinmu da zuciyarmu, yana sa darajarmu na mizanan Jehovah ya yi zurfi. Dangantakarmu da Allah ta zama aba mafi muhimmanci a rayuwarmu. Yayin da muke fuskantar jaraba, ba za mu yi tunani ba game da yadda zai yi kyau mu yi laifi. Maimako, damuwarmu na nan da nan shi ne mu riƙe aminci ga Jehovah. Daraja dangantakarmu sosai da shi yana motsa mu mu yaƙi kowanne nufi da zai ɓata ko halaka ta.
“Ina Ƙaunar Shari’arka ba Misali!”
10. Me ya sa yin biyayya ga dokar Jehovah wajibi ne don mu himmantu ga al’amuran ruhu?
10 Idan za mu himmantu ga al’amuran ruhu, sanin Kalmar Allah kawai bai isa ba. Sarki Sulemanu ya fahimci mizanan Jehovah da kyau, amma a kusan ƙarshen rayuwarsa, bai yi amfani da su ba. (1 Sarakuna 4:29, 30; 11:1-6) Idan muna da ruhaniya, za mu ga bukatar ba kawai na sanin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ba amma kuma na yin biyayya ga dokar Allah da zuciya ɗaya. Wannan yana nufin bincika mizanan Jehovah sosai da yin ƙoƙari mu bi su. Mai Zabura yana da irin wannan halin. Ya rera waƙa: “Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.” (Zabura 119:97) Idan muna damuwa da gaske game da bin dokar Allah, za mu motsu mu nuna inganci na ibada. (Afisawa 5:1, 2) Maimako mu zama da son yin mugunta, muna nuna ’ya’yan ruhu, kuma sha’awar faranta wa Jehovah rai tana juya mu daga munanan “ayyukan jiki.”—Galatiyawa 5:16, 19-23; Zabura 15:1, 2.
11. Yaya za ka bayyana cewa dokar Jehovah da ta hana fasikanci kāriya ce a gare mu?
11 Yaya za mu gina daraja sosai da ƙauna ga dokar Jehovah? Hanya ɗaya ita ce ta bincika amfaninsa sosai. Ka yi la’akari da dokar Allah da ta halalta jima’i ga masu aure kawai kuma ta haramta fasikanci da zina. (Ibraniyawa 13:4) Shin yin biyayya ga wannan dokar tana hana wani abu ne mai kyau? Uba mai ƙauna zai yi doka da za ta hana mu abu mai kyau ne? Babu! Ka dubi abin da yake faruwa a rayuwar mutane da yawa da ba sa rayuwa cikin jituwa da mizanan ɗabi’a na Jehovah. Cikin shege sau da yawa yana sa su zubar da ciki ko wataƙila su yi aure na gaggawa da babu farin ciki. Mutane da yawa suna renon yara babu miji ko mata. Ƙari ga haka, waɗanda suke fasikanci suna ba da kansu ga cututtuka da ake ɗauka ta wajen jima’i. (1 Korinthiyawa 6:18) Idan bawan Jehovah ya yi fasikanci, jiye-jiyensa zai dame shi sosai. Yin ƙoƙarin ɗaure lamiri mai laifi zai jawo rashin barci da baƙin ciki. (Zabura 32:3, 4; 51:3) Shin ba a bayyane yake ba cewa dokar Jehovah da ke hana fasikanci an shirya ne ta kāre mu? Hakika, akwai amfani mai girma a riƙe ɗabi’a mai tsabta!
Ka Yi Addu’a don Taimakon Jehovah
12, 13. Me ya sa ya dace mu yi addu’a yayin da sha’awace-sha’awace na zunubi sun kewaye mu?
12 Himmantuwa ga al’amuran ruhu babu shakka ya bukaci addu’a daga zuciya. Ya dace a roƙi taimakon ruhun Allah, domin Yesu ya ce: “Idan ku . . . da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa.” (Luka 11:13) Cikin addu’a, za mu iya furta dogararmu a kan ruhun don taimako game da kumamancinmu. (Romawa 8:26, 27) Idan mun gane cewa sha’awace-sha’awace na zunubi ko halaye suna shafan mu, ko kuma ɗan’uwa mai bi cikin ƙauna ya gaya mana wannan, zai yi kyau mu faɗi takamaiman matsalar cikin addu’o’inmu kuma mu roƙi taimakon Allah don mu magance waɗannan halaye.
13 Jehovah zai taimake mu mu mai da hankali ga abubuwa da ke daidai, tsattsarka, mafifici, da sun cancanci yabo. Ya dace mu yi masa addu’a na gaske don “salama kuwa ta Allah” ta tsai da zukatanmu da tunaninmu! (Filibbiyawa 4:6-8) Saboda haka, bari mu yi addu’a don taimakon Jehovah mu “guje ma waɗannan abu; [mu] bi adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, haƙuri, tawali’u.” (1 Timothawus 6:11-14) Da taimakon Ubanmu na samaniya, alhini da jaraba ba za su yi girma ba har su fi ƙarfinmu. Maimako, rayuwarmu za ta alamta kwanciyar rai da Allah ya bayar.
Kada Ku Ɓata wa Ruhu Rai
14. Me ya sa ruhun Allah ne ikon kasancewa da tsarki?
14 Bayin Jehovah da sun manyanta suna amfani da gargaɗin Bulus: “Kada ku ɓice Ruhu Mai-tsarki.” (1 Tassalunikawa 5:19) Tun da yake ruhun Allah ‘ruhu ne tsarkakka,’ yana da tsabta, tsarki, tsarkakke. (Romawa 1:4) Yayin da yake aiki a kanmu, wannan ruhu shi ne ikon tsarkaka, ko kuma tsabta. Yana taimakonmu mu ci gaba a hanyar rayuwa mai tsabta da ke nuna biyayya ga Allah. (1 Bitrus 1:2) Kowanne ayyuka marasa tsarki suna banza ne da wannan ruhu, wannan zai iya kawo sakamako na bala’i. Ta yaya?
15, 16. (a) Ta yaya za mu ɓata wa ruhun Allah rai? (b) Ta yaya za mu guji ɓata wa ruhun Jehovah rai?
15 Daidai ne Bulus ya rubuta: “Kada kuwa ku ɓata zuciyar Ruhu Mai-tsarki na Allah, wanda aka hatimce ku a cikinsa zuwa ranar fansa.” (Afisawa 4:30) Nassosi sun nuna ruhun Jehovah hatimi ne, ko kuma ‘kaɗan daga abin da za a yi nan gaba,’ ga amintattu shafaffun Kiristoci. Wannan rayuwa mara mutuwa ta sama ce. (2 Korinthiyawa 1:22; 1 Korinthiyawa 15:50-57; Ru’ya ta Yohanna 2:10) Ruhun Allah zai iya ja-gorar shafaffu da abokan tarayyarsu da suke da begen mallakar duniya cikin rayuwa ta aminci kuma zai taimake su su guje wa ayyuka na zunubi.
16 Manzon ya yi kashedi game da halaye nan ƙarya, sata, banzan hali, da sauransu. Idan mun bar irin wannan abubuwa su janye hankalinmu, za mu yi banza da gargaɗin Kalmar Allah wanda ruhu ne ya hure shi. (Afisawa 4:17-29; 5:1-5) Da haka, a wasu hanya za mu na ɓata wa ruhun Allah rai, babu shakka abin da za mu so mu guje wa ke nan. Game da wannan, idan waninmu ya soma yin banza da gargaɗin Kalmar Jehovah, za mu iya fara gina halaye da za su sa yin zunubi da gangan da kuma hasarar tagomashin Allah gabaki ɗaya. (Ibraniyawa 6:4-6) Ko da ba za mu na yin zunubi yanzu ba, wataƙila muna kan wannan hanyar. Ta ci gaba da yin abin da ya saɓa wa ja-gorar ruhun, za mu ɓata masa rai ke nan. Za mu na tsayayya wa da kuma ɓata wa Jehovah rai, tushen ruhu mai tsarki. Da shi ke muna ƙaunar Allah, ba za mu so mu yi haka ba. Maimako, bari mu yi addu’a don taimakon Jehovah domin kada mu ɓata wa ruhunsa rai amma mu ɗaukaka sunansa mai tsarki ta wurin ci gaba da himmantuwa ga al’amuran ruhu.
Ka Ci Gaba da Himmantuwa ga Al’amuran Ruhu
17. Waɗanne makasudai na ruhaniya za mu iya kafa wa kan mu, kuma me ya sa yin aiki don mu cika su abin hikima ne?
17 Hanya ta musamman da za mu ci gaba da himmantuwa ga al’amuran ruhu ita ce mu kafa makasudai na ruhaniya kuma mu yi ƙoƙari mu same su. Bisa ga bukatu da kuma yanayinmu, makasudinmu zai ƙunshi gyara halinmu na nazari, ƙara sa hannu cikin aikin wa’azi, ko yin burin gatar hidima ta musamman, irin su hidimar cikakken lokaci na majagaba, hidima a Bethel, ko aikin wa’azi na ƙasan waje. Wannan zai sa zuciyarmu ta shagala da bukatu na ruhaniya kuma zai taimake mu mu tsayayya wa miƙa kai ga kumamancinmu na ’yan Adam ko kuma son abin duniya da sha’awace-sha’awace da ba na Nassi ba da ke ko’ina a wannan tsarin abubuwa su rinjaye mu. Wannan babu shakka tafarkin hikima ne, gama Yesu ya aririce mu: “Kada ku ajiye wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke cinyewa, inda ɓarayi kuma ke hudawa suna sata: amma ku ajiye wa kanku dukiya cikin sama, inda asu da tsatsa ba su cinyewa, ɓarayi kuma ba su hudawa su yi sata ba: gama wurinda dukiyarka ta ke, can zuciyarka za ta kasance kuma.”—Matta 6:19-21.
18. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da himmantuwa ga al’amuran ruhu a wannan zamanin ƙarshe?
18 Himmantuwa ga al’amuran ruhu da guje wa sha’awace-sha’awace na duniya babu shakka tafarkin hikima ne a wannan “zamanin ƙarshe.” (2 Timoti 3:1-5) Ballantana ma, “duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:15-17) Alal misali, idan matashi Kirista ya biɗi makasudin hidima ta cikakken lokaci, wannan zai iya zama abin ja-gora a shekarun kaluɓale na ƙuruciya. Idan an matsa wa mutum ya karya ƙa’ida, irin wannan mutum zai tuna abin da shi ko ita ya ko take so ta cim ma a hidimar Jehovah. Irin wannan mutum na ruhaniya zai san ba hikima ba ce, wawanci ne ma, ya yi hasarar cim ma makasudai na ruhaniya don neman abin duniya ko kuma more romon da zunubi zai kawo. Ka tuna cewa Musa mai ruhaniya ya ‘gwammaci ya jure shan wuya tare da jama’ar Allah, da ya mori romon zunubi, mai saurin wucewa.’ (Ibraniyawa 11:25) Ko mu matasa ne ko manya, muna irin wannan zaɓen yayin da muka ci gaba da himmantuwa ga al’amuran ruhu maimakon ajizin jiki.
19. Waɗanne fa’idoji za mu more idan mun ci gaba da himmantuwa ga al’amuran ruhu?
19 “Himmantuwar jiki gāba ce da Allah,” yayin nan kuma “himmantuwar ruhu rai ne da lafiya.” (Romawa 8:6, 7) Idan mun ci gaba da himmantuwa ga al’amuran ruhu, za mu sami salama mai tamani. Zuciyarmu da tunaninmu za su kasance a tsare sosai daga rinjaya ta yanayinmu na zunubi. Za mu fi tsayayya wa jaraba na yin laifi. Kuma za mu samu taimakon Allah mu jure wa kokawa da ke ci gaba tsakanin halin mutuntaka da ruhu.
20. Me ya sa za mu tabbata cewa zai yiwu mu yi nasara a yaƙi tsakanin halin mutuntaka da kuma na ruhu?
20 Ta ci gaba da himmantuwa ga al’amuran ruhu, za mu kiyaye mahaɗi mai muhimmanci da Jehovah, tushen rai da kuma ruhu mai tsarki. (Zabura 36:9; 51:11) Shaiɗan Iblis da mabiyansa suna iyakacin ƙoƙarinsu su halaka dangantakarmu da Jehovah Allah. Suna ƙoƙari su samu zuciyarmu, sun san cewa idan mun fāɗi, wannan zai kai ga magabtaka da Allah sai kuma mutuwa. Amma za mu iya nasara a wannan yaƙi tsakanin halin mutuntaka da kuma ruhu. Haka yake ga Bulus, da ya rubuta game da nasa yaƙin, da farko ya ce: “Wanene za ya tsamo ni daga cikin jikin nan na mutuwa?” Sa’annan, don ya nuna cewa tsira za ta yiwu, ya ce: “Na gode ma Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Romawa 7:21-25) Mu ma za mu iya gode wa Allah ta wurin Kristi don tanadin hanyar da za mu jure da kumamanci na ’yan Adam kuma mu ci gaba da ƙwallafa rai ga al’amuran ruhu da bege mai ban al’ajabi na rai madawwami.—Romawa 6:23.
Ka Tuna?
• Menene ake nufi a himmantu ga al’amuran ruhu?
• Yaya za mu bar ruhun Jehovah ya yi aiki a kanmu?
• Ka bayyana dalilin da ya sa a yaƙinmu gāba da zunubi, yana da muhimmanci mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki, mu yi biyayya ga dokar Jehovah, kuma mu yi addu’a gare shi.
• Yaya kafa makasudai na ruhaniya zai sa mu ci gaba a tafarkin rai?
[Hoto a shafi na 14]
Nazarin Littafi Mai Tsarki yana taimakonmu mu jure yaƙi wa ruhaniyarmu
[Hoto a shafi na 15]
Daidai ne mu yi addu’a don taimakon Jehovah mu sha kan sha’awar zunubi
[Hotuna a shafi na 16]
Makasudai na ruhaniya zai taimake mu mu ci gaba da himmatuwa ga al’amuran ruhu