Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 3/1 pp. 4-9
  • Ranar Shari’a Ta Jehovah Ta Gabato!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ranar Shari’a Ta Jehovah Ta Gabato!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehovah Ya Miƙa Hannunsa
  • Ƙarshen Kiristendam Ya Kusa!
  • Jim Kaɗan—Ranar Kururuwa Za ta Zo!
  • “Babbar Ranar Ubangiji ta Gabato”
  • Ka Nemi Jehovah Kafin Ranar Hasalarsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Zafaniya
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Mutanen Jehovah Da Suka Komo Suna Yabonsa A Dukan Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • “Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 3/1 pp. 4-9

Ranar Shari’a Ta Jehovah Ta Gabato!

“Babbar ranar Ubangiji ta gabato, tana gabatowa da sauri.”—ZAFANIYA 1:14.

1. Wane kashedi Allah ya yi ta hannun Zafaniya?

JIM KAƊAN Jehovah Allah zai faɗā wa miyagu. Ka saurara! Wannan gargaɗinsa ne: “Zan shafe mutum . . . Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.” (Zafaniya 1:3) An faɗi waɗannan kalmomi na Ubangiji Jehovah Mai Ikon Mallaka ta wurin annabinsa Zafaniya, wataƙila shi tattaɓa-kunne ne na Sarki Hezekiya mai aminci. Wannan furci, da aka yi a kwanakin Sarki Yosiya, ya faɗi mummunar sakamako ga miyagu da ke zaune cikin ƙasar Yahuza.

2. Me ya sa ayyukan Yosiya bai hana ranar shari’a ta Jehovah ba?

2 Babu shakka annabci da Zafaniya ya yi ya sa Sarki Yosiya matashi ya fahimci bukatar kawar da sujjada mara tsabta daga Yahuza. Amma ayyukan sarkin na kawar da addinin ƙarya daga ƙasar bai share dukan mugunta da ke tsakanin mutanen ba ko kuma ya yi kafarar zunuban kakansa, Sarki Manassa, wanda ya “cika Urushalima da jinin marasa laifi.” (2 Sarakuna 24:3, 4; 2 Tarihi 34:3) Saboda haka, ranar shari’a ta Jehovah lalle za ta zo.

3. Ta yaya za mu tabbata cewa zai yiwu mu tsira daga “ranar hasalar Ubangiji”?

3 Duk da haka, akwai waɗanda za su tsira daga ranar nan mai ban tsoro. Saboda haka, annabin Allah ya aririta: “Kafin a zartar da umarni, kafin a kore ku kamar ƙaiƙayi, kafin kuma zafin fushin Ubangiji ya auko muku, kafin ranar hasalar Ubangiji ta auko muku. Ku nemi Ubangiji, dukanku masu tawali’u na duniya, ku waɗanda ke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali’u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.” (Zafaniya 2:2, 3) Da begen tsira daga ranar shari’a ta Jehovah a zuciya, bari mu bincika littafin Zafaniya a cikin Littafi Mai Tsarki. An rubuta shi a Yahuza kafin shekara ta 648 K.Z., sashe ne na “kalmar annabci” ta Allah, wadda dukanmu ya kamata mu mai da hankali da dukan zuciya.—2 Bitrus 1:19.

Jehovah Ya Miƙa Hannunsa

4, 5. Ta yaya Zafaniya 1:1-3 ya cika a kan miyagu a Yahuza?

4 ‘Maganar Jehovah’ ga Zafaniya ta fara da kashedi da aka nuna da farko. Allah ya ce: “Ni Ubangiji na ce, zan shafe dukan kome da ke a duniya. Zan shafe mutum da dabba, zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku, zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye, zan kuma datse ɗan adam daga duniya.”—Zafaniya 1:1-3.

5 Hakika, Jehovah zai kawo ƙarshen mugunta a ƙasar Yahuza. Wanene Allah zai yi amfani da shi ya “shafe dukan kome da ke a duniya”? Tun da yake Zafaniya ya yi annabci ne a farkon lokacin sarautar Sarki Yosiya, wanda ya fara a shekara ta 659 K.Z., waɗannan kalmomin annabci sun cika a lokacin da Babila ta halaka Yahuza da babban birninta, Urushalima, a shekara ta 607 K.Z. A lokacin an ‘shafe’ miyagu a Yahuza.

6-8. Menene aka annabta a Zafaniya 1:4-6, yaya wannan annabci ya cika a bisa Yahuza ta dā?

6 Da yake annabta ayyukan Allah a kan masu sujjadar ƙarya, Zafaniya 1:4-6 ya ce: “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuza da dukan mazaunan Urushalima. A wurin nan zan datse saura waɗanda ke bauta wa Ba’al, da kuma sunayen firistocin gumaka tare da firistocina, da kuma waɗanda ke durƙusa wa rundunan sama a kan bene, waɗanda suka durƙusa, su rantse da Ubangiji, duk da haka kuma sai su rantse da Milkom, da kuma waɗanda suka juya, suka bar bin Ubangiji, waɗanda ba su neman Ubangiji, ba su kuma roƙonsa.”

7 Jehovah ya miƙa hannunsa gāba da mutanen Yahuza da Urushalima. Ya ƙudiri aniyyar datse masu yin sujjada wa Ba’al allahn ni’ima na Kan’ana. Ana kiran alloli dabam dabam na yankin Ba’al domin masu yi musu sujjada suna tunani cewa su ne suke da iko a wurare na musamman. Alal misali, da akwai Ba’al da Mowabawa da Midiyanawa suke bauta wa a Dutsen Peor. (Littafin Ƙidaya 25:1, 3, 6) A duk cikin Yahuza, Jehovah zai datse firistocin Ba’al, haɗe da firistoci Lawiyawa marasa aminci waɗanda suke karya dokar Allah ta yin zumunci da su.—Fitowa 20:2, 3.

8 Allah kuma zai datse waɗanda ke “durƙusa wa rundunan sama,” babu shakka duba da taurari da kuma yi wa rana sujjada. (2 Sarakuna 23:11; Irmiya 19:13; 32:29) Allah zai hukunta waɗanda suke ƙoƙari su haɗa sujjadar gaskiya da addinin ƙarya ta ‘rantse wa da Jehovah da kuma Milkom.’ Milkom wataƙila wani suna ne na Molek, babban allahn Ammoniyawa. Bautar Molek ta ƙunshi hadayar yara.—1 Sarakuna 11:5; Irmiya 32:35.

Ƙarshen Kiristendam Ya Kusa!

9. (a) Game da menene Kiristendam suke da laifi? (b) Ba kamar marasa aminci na Yahuza ba, me ya kamata mu yi aniyyar yi?

9 Dukan waɗannan sun tunasar mana da Kiristendam, wanda ya ƙware a addinin ƙarya da kuma duba da taurari. Matsayinsa a hadayar rayukan miliyoyi a kan goyon bayan limamai a yaƙe-yaƙe, abin ƙyama ne ƙwarai! Kada mu zama marasa aminci kamar waɗanda suke Yahuza, waɗanda ‘sun yi ridda daga bin Jehovah,’ ba su da marmari kuma ba sa biɗansa, ba sa kuwa neman ya yi musu ja-gora. Maimako, bari mu riƙe gaskiyarmu ga Allah.

10. Yaya za ka bayyana ma’anar annabci na Zafaniya 1:7?

10 Kalmomin annabin na gaba sun dace da miyagu na Yahuza da miyagu na zamaninmu. Zafaniya 1:7 ta ce: “Ku yi tsit a gaban Ubangiji Allah! Gama ranar Ubangiji ta gabato. Ubangiji ya shirya ranar shari’a, ya kuma keɓe waɗanda za su aikata hukuncinsa.” Babu shakka, waɗannan ‘baƙin’ Kaldiyawa ne abokan gaban Yahuza. ‘Hadayar’ Yahuza ce kanta, haɗe da babban birninta! Da haka Zafaniya ya yi shelar nufin Allah ya halaka Urushalima, amma wannan annabci yana nuni ne ga halaka ta Kiristendam. Domin ranar shari’ar Allah ta kusa sosai a yau, ya kamata dukan duniya su ‘yi tsit a gaban Ubangiji Allah’ su ji abin da yake faɗa ta “ƙaramin garke” na shafaffun mabiyan Yesu da abokan tarayyarsu, “waɗansu tumaki” nasa. (Luka 12:32; Yahaya 10:16) Halaka tana jirar dukan waɗanda ba su saurara ba, da kuma waɗanda suka kafa kansu gaba da Sarautar Allah.—Zabura 2:1, 2.

Jim Kaɗan—Ranar Kururuwa Za ta Zo!

11. Menene ma’anar Zafaniya 1:8-11?

11 Game da ranar Jehovah, Zafaniya 1:8-11 suka daɗa cewa: “A ranar shari’a, ni Ubangiji zan hukunta shugabanni da hakimai, da dukan waɗanda ke bin al’adun ƙasashen waje. A wannan rana zan hukunta duk wanda ke tsalle a bakin ƙofa, da waɗanda ke cika gidan maigidansu da zalunci da ha’inci. Ni Ubangiji na ce, a wannan rana, za a ji kuka a Ƙofar Kifi, za a ji kururuwa kuma daga unguwa ta biyu, da amon ragargajewa daga kan tuddai. Ku yi kururuwa, ku mazaunan Maktesh, Gama ’yan kasuwa sun ƙare, an kuma datse dukan waɗanda ke awon azurfa.”

12. Yaya aka iske wasu suna “bin al’adun ƙasashen waje”?

12 Yehowahaz, Yehoyakim, da Yekoniya ne za su ɗauki matsayin Sarki Yosiya. Sai kuma halakar Urushalima za ta zo wadda ke nuna somi na sarautar Zadakiya. Ko da suna fuskantar irin wannan bala’i, wasu da babu shakka sun nemi al’ummai maƙwabta su amince da su suna “bin al’adun ƙasashen waje.” Hakanan ma, mutane da yawa a yau suna nuna a hanyoyi dabam dabam cewa su ba sa cikin sashen ƙungiyar Jehovah. Da yake suna sashen ƙungiyar Shaiɗan, za a hora su.

13. Cikin jituwa da annabcin Zafaniya, menene zai faru lokacin da Babiloniyawa za su kai wa Urushalima farmaki?

13 “Wannan rana” ta hisabi a kan Yahuza ta yi daidai da ranar Jehovah ta zartar da hukunci a kan magabtansa, ya kawo ƙarshen mugunta, kuma ya nuna mafificin ikonsa. Yayin da Babiloniyawa sun kai wa Urushalima farmaki, za a ji kuka daga Ƙofar Kifi. Mai yiwuwa an kira ta da wannan suna domin ta yi kusa da kasuwar kifi. (Nehemiya 13:16) Rundunar Babila za su shiga ɓangare da ake kira unguwa ta biyu, da “amon ragargajewa daga kan tuddai” mai yiwuwa yana nufin amon Kaldiyawa da suke tafe. Mazauna Maktesh za su “yi kururuwa,” wataƙila Kwarin Tyropoeon ta samansa. Me ya sa za su yi kururuwa? Domin kasuwanci zai ƙare, haɗe da na “waɗanda ke awon azurfa.”

14. Yaya yawan binciken Allah na waɗanda suke da’awar suna masa sujjada?

14 Har yaya binciken Jehovah na waɗanda suke da’awar suna masa sujjada zai kai? Annabcin ya ci gaba: “A lokacin nan, zan bincike Urushalima da fitilu, zan kuwa hukunta marasa kulawa waɗanda suke zaman annashuwa, waɗanda ke cewa a zukatansu, ‘Ubangiji ba zai yi alheri ba, ba kuma zai yi mugunta ba!’ Za a washe dukiyarsu, za a kuwa rurrushe gidajensu, ko da ya ke sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba, Ko da ya ke sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”—Zafaniya 1:12, 13.

15. (a) Menene zai faru da firistoci da suka yi ridda na Urushalima? (b) Menene ke jiran waɗanda suke bin addinin ƙarya a yau?

15 Firistoci da suka yi ridda na Urushalima suna haɗa sujjadar Jehovah da arnanci. Ko da suna ji suna da kwanciyar rai, Allah zai samo su da fitilu masu haskakawa da za su haskaka duhu na ruhaniya a inda suke ɓoye. Babu wanda zai tsira daga shelar da kuma zartar da hukunci na Allah. Waɗannan ’yan ridda da suke da halin babu ruwanmu suna zaune kamar tsaki a gindin randa. Ba sa so a dame su da shelar Allah na sa hannu a harkokin ’yan Adam, amma ba za su tsira daga zartar da hukunci na Allah a kansu ba. Waɗanda suke yin addinin ƙarya a yau ba za su tsira ba, haɗe da waɗanda suke Kiristendam da waɗanda suka yi ridda daga sujjadar Jehovah. Suna musu cewa waɗannan “kwanaki na ƙarshe” ne, suna cewa a zuciyarsu, “Ubangiji ba zai yi alheri ba, ba kuma zai yi mugunta ba.” Amma sun yi kuskure!—2 Timoti 3:1-5; 2 Bitrus 3:3, 4, 10.

16. Menene zai faru lokacin da aka zartar da hukuncin Allah a kan Yahuza, yaya ya kamata sanin wannan ya taɓa mu?

16 An yi wa ’yan ridda na Yahuza kashedi cewa Babiloniyawa za su washe dukiyarsu, su rurrushe gidajensu, su kuma kwashe ’ya’yan gonakin inabinsu. Abin duniya zai zama banza a lokacin da aka zartar da hukunci na Allah a kan Yahuza. Hakan zai zama lokacin da ranar hukunci ta Jehovah za ta zo kan wannan tsarin abubuwa. Bari mu ci gaba a ruhaniya kuma mu ‘tara dukiya a sama’ ta wajen sa hidimar Jehovah farko a rayuwanmu!—Matiyu 6:19-21, 33.

“Babbar Ranar Ubangiji ta Gabato”

17. Bisa Zafaniya 1:14-16, yaya kusan gabatowar ranan hukunci na Jehovah?

17 Yaya kusan ranar Jehovah take? Bisa ga Zafaniya 1:14-16, Allah ya ba da wannan tabbaci: “Babbar ranar Ubangiji ta gabato, tana gabatowa da sauri. Ku ji muryar ranar Ubangiji! Jarumi zai yi kuka mai zafi. Wannan rana ta hasala ce, ranar azaba da wahala, ranar lalatarwa da hallakarwa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu, ranar busar ƙaho da yin kururuwar yaƙi gāba da birane masu garu da hasumiyai masu tsawo.”

18. Me ya sa bai kamata mu kammala da cewa ranan hukunci ta Jehovah za ta faru ne can gaba ba da nesa ba?

18 An yi wa firistoci masu zunubi, hakimai, da mutanen Yahuza kashedi cewa ‘babbar ranar Jehovah ta gabato.’ Ga Yahuza ‘ranar Jehovah tana gabatowa da sauri ainun.’ Hakanan ma a lokacinmu, kada kowa ya yi tunani cewa zartar da hukunci na Jehovah a kan miyagu zai faru can gaba ne da nesa. Maimako, yadda Allah ya aikata da sauri a Yahuza, haka zai yi ‘sauri’ a ranarsa ta zartar da hukunci. (Wahayin Yahaya 16:14, 16) Lokacin baƙin ciki ne ga dukan waɗanda suka yi banza da gargaɗin Jehovah da Shaidunsa suka bayar da kuma waɗanda suka kasa karɓan sujjada ta gaskiya!

19, 20. (a) Menene wasu fanni na zartar da hasalar Allah a kan Yahuza da Urushalima? (b) Game da halaka da aka ware da ke fuskantar wannan tsarin abubuwa, waɗanne tambayoyi ne suka taso?

19 Zartar da hasalar Allah a kan Yahuza da Urushalima “ranar azaba da wahala” ce. Masu halakarwa na Babiloniya sun haddasa wahala da yawa ga mazauna Yahuza, haɗe da baƙin ciki na ƙwarai a lokacin mutuwa da halaka. Wannan “ranar lalatarwa da hallakarwa” na duhu, gizagizai, da baƙin duhu ne, wataƙila ba ta alama ba ce kawai, amma kuma ta zahiri ce, saboda hayaki da kuma mutane da aka kashe sun cika ko’ina. “Ranar busar ƙaho da yin kururuwar yaƙi” ce, amma an yi kashedi a banza.

20 Masu tsaro na Urushalima ba su da taimako yayin da raguna masu halakarwa na Babiloniyawa za su ci “hasumiyai masu tsawo.” Makamin wannan mugun tsarin abubuwa za su zama banza ga matattarin makaman sama na Allah, wanda zai yi amfani da su wajen halaka waɗanda aka ware. Kana da begen tsira? Ka tsaya da ƙarfi a gefen Jehovah, ‘wanda yake kiyaye dukan waɗanda ke ƙaunarsa amma wanda zai hallaka mugaye duka’?—Zabura 145:20.

21, 22. Yaya Zafaniya 1:17, 18 za ta cika a zamaninmu?

21 An annabta ranar hukunci mai ban tsoro ƙwarai a Zafaniya 1:17, 18! “Zan aukar wa mutane da wahala,” in ji Jehovah Allah, “za su kuwa yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura, namansu kuwa kamar taroso. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su a ranar hasalar Ubangiji ba, a cikin zafin kishinsa dukan duniya za ta halaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.”

22 Kamar yadda ya yi a zamanin Zafaniya, Jehovah ba da jimawa ba zai kawo wahala a kan “duniya duka,” na waɗanda suka ƙi su yi biyayya da gargaɗinsa. Saboda sun yi zunubi ga Allah, za su yi tafiya kamar makafi babu taimako, ba za su iya samun ceto ba. A ranar hukunci na Jehovah, “za a zubar da jininsu kamar ƙura,” kamar abin da ba shi da amfani. Hakika ƙarshensu zai zama da kunya, domin Allah zai watsar da jikunan—har ma da kayan ciki—na waɗannan miyagu a duniya, “kamar taroso.”

23. Ko da miyagu ba za su tsira ba a “ranar hasalar Ubangiji,” wane bege annabcin Zafaniya ya miƙa?

23 Babu wanda zai iya cetan masu yaƙi da Allah da mutanensa. Ko azurfa ko zinariya ba su iya cetan miyagu na Yahuza ba, yadda tsabar arziki da cin hanci ba za su tsare ko tsirar da wani ba “a ranar hasalar Ubangiji” a kan Kiristendam da sauran wannan tsarin abubuwa. A wannan rana ta ƙarshe, “dukan duniya za ta halaka” ta zafin kishin Allah yayin da ya halaka miyagu. Domin muna da bangaskiya cikin kalmomin annabci na Allah, mun tabbata cewa mun yi nisa cikin “ƙarshen lokaci.” (Daniyel 12:4) Ranan hukunci na Jehovah ta gabato, jim kaɗan zai zartar da ramakonsa a kan magabtansa. Duk da haka, annabcin Zafaniya ya ba da begen ceto. To, menene ake bukata a gare mu don a ɓoye mu a ranar hasalar Jehovah?

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya annabcin Zafaniya ya cika a bisa Yahuza da Urushalima?

• Menene yake jiran Kiristendam da dukan miyagu a zamaninmu?

• Me ya sa bai kamata mu yi tunani cewa ranar hukunci na Jehovah zai zo a can gaba da nesa ba?

[Hoto a shafi na 5]

Zafaniya da gaba gaɗi ya yi shelar cewa ranar hukunci na Jehovah ta gabato

[Inda aka Dauko]

Daga Self-Pronouncing Edition of the Holy Bible, yana ɗauke da juyin King James da na Revised

[Hoto a shafi na 7]

Ranar Jehovah ta zo bisa Yahuza da Urushalima ta hannun Babiloniyawa a shekara ta 607 K.Z.

[Hoto a shafi na 8]

Kana da begen za ka tsira lokacin da Jehovah zai halaka miyagu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba