Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wcg babi na 46 pp. 208-211
  • “Na Ga Ubangiji!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Na Ga Ubangiji!”
  • Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Bincike Sosai
  • Ka Yi Tunani a kan Darussan
  • Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
  • Ƙarin Darussa
  • Ta Karɓi Aikin da Ƙarfin Zuciya
    Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
  • “Ta Yi Abin da Za Ta Iya Yi”
    Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
  • Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
wcg babi na 46 pp. 208-211

46 MARYAMU MAGDALIN

“Na Ga Ubangiji!”

Hoto
Hoto

MARYAMU MAGDALIN ta sha wahala sosai. Miyagun ruhohi sun shiga jikinta kuma sun yi ta wulaƙanta ta. Amma rayuwarta ta canja saꞌad da ta haɗu da Yesu. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya fitar da “aljanu bakwai” daga jikinta. Ta yi godiya sosai ga Yesu har ta zama mabiyinsa, kuma ta yi iya ƙoƙarinta don ta taimaka masa.

Tana ƙaunar Yesu sosai kuma tana kiran sa Rabboni, wanda ke nufin “Malami.” Hakan ya nuna cewa tana daraja Yesu sosai. Yesu da almajiransa 12 sun zagaya dukan yankin suna waꞌazi game da Mulkin Allah. Maryamu ta lura cewa mutanen nan sun bar ayyukansu kuma suna amfani da lokacinsu da ƙarfinsu gabaki-ɗaya don su yi wannan aiki mai muhimmanci. Mene ne Maryamu ta yi don ta taimaka musu?

Maryamu Magdalin ta yi fama sosai, amma da ta haɗu da Yesu, ta mai da hankali ga taimaka masa da mabiyansa

Maryamu tana cikin mata da yawa da suke yi wa Yesu da almajiransa “hidima.” Matan nan sun yi amfani da kuɗinsu don biyan bukatun Yesu da almajiransa. Mai yiwuwa adadin almajiran Yesu da suke bin sa yin waꞌazi a “garuruwa da ƙauyuka” sun kai 20. Wataƙila mutane sun yi mamaki sosai saꞌad da suka ga matan nan suna bin Yesu, domin a lokacin mata ba sa tafiya tare da malamin addini, kuma wataƙila mutane sun yi wa matan nan baƙar magana. Amma a wurin Maryamu da sauran matan, babu abin da ya fi muhimmanci kamar kula da Yesu da almajiransa. Domin suna da ƙarfin zuciya, sun kula da Yesu duk da cewa mutane sun yi maganganu marasa kyau game da su.

Babu shakka, Maryamu ta yi baƙin ciki sosai saꞌad da aka kama Yesu a daren Bikin Ƙetarewa a Urushalima, aka yanke masa hukunci cewa ya yi saɓo, kuma aka kashe shi a kan gungumen azaba. Amma ba ta daina nuna ƙarfin zuciya ba. Ta raka mamar Yesu da wasu mata masu aminci zuwa wurin da aka kashe Yesu. Kuma ko a lokacin da Yesu yake shan wahala a kan gungumen azaba, ya ga cewa matan ba su bar shi ba kuma suna ƙaunar sa sosai. Sun shaida yadda Yesu ya riƙe amincinsa har mutuwa, da kuma yadda ya kammala dukan abubuwan da Ubansa ya aiko shi ya yi. Maryamu tana wurin a lokacin da ya yi numfashinsa na ƙarshe.

Maryamu Magdalin tana taimaka wa mamar Yesu yayin da su biyun suke kallon Yesu yana shan wahala a kan gungumen azaba. Shugabannin addinan Yahudawa suna hararar su, sojojin Roma suna tsaye kusa, kuma akwai wasu a bayansu da suke makoki.

Maryamu da sauran matan sun nuna ƙarfin zuciya wajen yin kuka a gaban sojojin Roma da shugabannin Yahudawa, waɗanda suka kashe Yesu. Ko da yake Maryamu tana baƙin ciki sosai, har ila akwai wani abu da take so ta yi don ta nuna cewa tana ƙaunar Yesu. A yankin Yahudiya, ana zafi sosai, kuma hakan na sa gawa ta yi saurin ruɓewa. Don kada warin ya dami masu makoki, akan shafa wa gawar māi da turare mai ƙamshi kafin a binne gawar. Abin da Maryamu take so ta ƙara yi ke nan bayan an binne Yesu. Da sassafe bayan Ranar Assabaci, sai Maryamu da wasu mata suka sayi kayan ƙamshi kuma suka je kabarin Yesu don su shafa wa gawarsa.

Mai yiwuwa Maryamu ce ta fara isa kabarin, kuma ta yi mamaki da ta sami kabarin a buɗe kuma babu kome a ciki! Sai ta gudu zuwa wurin Bitrus da Yohanna don ta gaya musu abin da ta gani. Saꞌad da ta dawo, ba ta sami sauran matan ba. Maryamu ta matso kusa kuma ta leƙa cikin kabarin, sai ta ga “malaꞌiku biyu sanye da fararen riguna, suna zaune a wurin da gawar Yesu take a dā.” Bayan ta ɗan yi magana da su, sai ta juya baya kuma ta ga wani mutum wanda ta ɗauka cewa shi mai kula da lambu ne. Sai mutumin ya tambaye ta: “Me ya sa kike kuka?” Sai ta ce: “Maigida, idan kai ne ka ɗauke shi, ka gaya mini inda ka kwantar da shi, domin in je in ɗauke shi.” Maryamu ba ta yi tunanin ko za ta iya ɗaukan gawar mutumin da ya manyanta ba. Ta dai san cewa za ta yi iya ƙoƙarinta don ta nuna ƙaunarta ga Yesu.

Da ta juya za ta koma cike da baƙin ciki, sai mutumin ya ce mata: “Maryamu!” Nan da nan ta gane muryar. Sai ta yi ihu ta ce: “Rabboni!” kuma ta rungume shi. Yesu bai bar ta ta ci-gaba ta riƙe shi ba. Yana so ta yi wani aiki mai muhimmanci, sai ya ce mata: “Ki je wurin ꞌyanꞌuwana.” Yana so ta je ta gaya wa manzanninsa labari mafi daɗi da suka taɓa ji, wato an ta da Ubangijinsu! Kuma ta tafi nan take. Da farko, manzannin ba su yarda da abin da ta faɗa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce sun ɗauki maganar kamar “zancen banza ne kawai.” Amma shakkar da suka yi ba ta hana Maryamu Magdalin gaya wa mutane cewa an ta da Yesu ba. Kuma har bayan lokacin, ta ci-gaba da gaya wa mutane cewa an ta da Yesu. Yin hakan na bukatar ƙarfin zuciya sosai.

Ka karanta labarin a:

  • Matiyu 27:​55, 56

  • Markus 16:​1, 2

  • Luka 8:​1-3; 24:​1-11

  • Yohanna 19:25; 20:​1, 2, 11-18

Mene ne raꞌayinka?

A waɗanne hanyoyi ne Maryamu Magdalin ta nuna ƙarfin zuciya?

Ka Yi Bincike Sosai

  1. 1. A waɗanne hanyoyi ne mai yiwuwa Maryamu Magdalin da wasu mata suka taimaka wa Yesu da almajiransa? (ijwia talifi na 6 sakin layi na 5-6-wcgr) Ka duba hoto na 1

    Maryamu Magdalin tana gai da Yesu da manzanninsa biyu yayin da suke shigowa gidanta. Akwai wasu mata kuma da suke farin ciki yayin da suke yin burodi da saƙa riga.

    Hoto na 1

  2. 2. Da farko, me ya sa ya yi wa Maryamu wuya ta gane Yesu bayan da aka ta da shi daga mutuwa? (ijwia talifi na 6 sakin layi na 16-wcgr)

  3. 3. Me ya sa Yesu ya ce wa Maryamu Magdalin ta daina riƙe shi? (w08 4/15 32 sakin layi na 6)

  4. 4. Da Maryamu Magdalin ta gaya wa manzannin Yesu cewa an ta da Yesu daga mutuwa, sun ɗauka cewa “zancen banza ne kawai” take yi. Wane irin raꞌayi ne suke da shi game da mata da ya sa suka faɗi hakan? (Luk. 24:11; w12 10/1 10 sakin layi na 1-2)

Ka Yi Tunani a kan Darussan

  • Maryamu Magdalin ta yi abubuwa dabam-dabam don ta taimaka ma wasu. Ta yaya za mu yi koyi da ita? Ka duba hoto na 2

    Wasu ꞌyanꞌuwa mata uku suna farin ciki yayin da suke raba abinci a wani wurin da ake aikin gini.

    Hoto na 2

  • Ta yaya za mu yi koyi da Maryamu Magdalin saꞌad da wasu suka ƙi amincewa da waꞌazi da muke yi musu, ko kuma ba su daraja shi ba? (Luk. 24:​10, 11)

  • Ta yaya za ka yi koyi da irin ƙarfin zuciya da Maryamu Magdalin ta nuna?

Ka Ƙara Yin Tunani Sosai

  • Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?

  • Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?

  • Me ya sa kake godiya domin da alama an zaɓi Maryamu Magdalin ta yi mulki tare da Kristi a sama?

Ƙarin Darussa

Ka karanta talifin nan don ka ga wasu abubuwa da mutane suke faɗa game da Maryamu Magdalin da kuma gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

“Wace ce Maryamu Magdalin?” (ijwbq talifi na 172-wcgr)

Ta yaya yadda Yesu ya bi da Maryamu Magdalin da wasu mata, ya kafa mana misali na yadda ya kamata mu bi da mata? Ka karanta talifin nan don ka ga amsar.

“Mata Kirista Sun Cancanci Ban-girma da Ladabi” (w95 8/1 14-16 sakin layi na 3-8)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba