47 MARYAMU, ꞌYARꞌUWAR LIꞌAZARU
“Ta Yi Abin da Za Ta Iya Yi”
MARYAMU ta nuna godiya sosai domin alherin da Yesu Kristi ya yi musu. Ya yi mata da ꞌyarꞌuwata Marta da kuma ɗanꞌuwansu Liꞌazaru alheri sosai. Sau da yawa Yesu ya sauka a gidansu da ke Betani, kuma ya koyar da su sosai game da Jehobah da kuma kansa. Sun zama aminansa sosai. Kuma saꞌad da Liꞌazaru ya mutu, Yesu ya ta da shi daga mutuwa!
Maryamu ta so ta nuna ma Yesu cewa tana godiya. Sai ta yanke shawarar ba shi kyauta mai daraja, wato “rabin litan mān ƙamshi mai tsada sosai, wanda aka yi da nad zalla,” a cikin kwalbar alabasta. A zamaninsu, lebura zai yi aiki na kusan shekara guda kafin ya sami isasshen kuɗi da zai saya ƙaramar kwalbar mān ƙamshin. Littafi Mai Tsarki bai faɗa lokacin da Maryamu ta sayi wannan mān ƙamshi ko yadda ta saye shi ba, amma wataƙila shi ne abu mafi tsada da take da shi.
Tana so ta ba wa Yesu kyauta mafi daraja, kuma ta san cewa hakan zai iya sa wasu mutane su yi mata baƙar magana
Wata rana, saꞌad da Yesu yake cin abinci a gidan wani mutum a Betani, sai Maryamu ta yanke shawarar ba shi kyautar. Ta zo wurin Yesu kuma ta buɗe kwalbar, a hankali ta zuba mān ƙamshin nan mai daraja a kansa da ƙafafunsa. Yayin da mān yake ɗiga a ƙasa, sai ta cire ɗankwalinta kuma ta share ƙafafunsa da gashinta. Wasu za su iya ganin cewa bai dace da ta cire ɗankwalinta ba bisa alꞌadarsu. Amma a wannan lokacin, Maryamu ta damu ne kawai da abin da zai mutunta Ubangijinta. Ta ƙaskantar da kanta don ta daraja shi sosai.
Jim kaɗan, sai ƙamshin ya cika gidan gabaki-ɗaya. Amma ba kowa ba ne ya ji daɗin hakan. Yahuda Iskariyoti ya yi fushi sosai kuma da alama ya sa wasu manzannin suka goyi bayansa, cewa abin da Maryamu ta yi ba daidai ba ne. Yahuda ya yi tambaya cewa: “Me ya sa ba a sayar da mān ƙamshin nan dinari ɗari uku ba, kuma a ba wa talakawa kuɗin?” Ka yi tunanin yadda Maryamu ta ji. Tana ƙaunar Yesu kuma ta so ta daraja shi da wannan kyauta ta musamman. Maimakon manzannin Yesu su yaba mata, sai suka yi fushi da ita. Babu shakka ta ji kunya sosai. Amma Yesu bai yi fushi kamar manzanninsa ba, ya yaba mata.
Yesu ya gaya wa mazajen cewa: “Ku bar ta.” Babu shakka, da suka ji abin da ya faɗa, dukansu sun yi shuru. Ya ce: “Abu mai kyau ne ta yi mini.” Yesu ya gaya musu cewa Maryamu ta yi hakan ne don ta nuna masa cewa tana ƙaunar sa. Abin da Maryamu ta yi yana da kyau sosai domin Yesu ya kusan mutuwa. Ko da yake ita da kanta ba ta san da hakan ba. Yesu ya ce ta zuba mān ne domin jikinsa da aka kusan binne. Yesu ya fahimci dalilin da ya sa Maryamu ta zuba masa mān ƙamshin, kuma ya ce: “Ta yi abin da za ta iya yi.” A ƙarshe, ya ƙara da cewa: “A gaskiya ina gaya muku, a duk inda za a yi shelar labari mai daɗi a dukan duniya, za a riƙa faɗin abin da matar nan ta yi don tunawa da ita.” Yesu ya san cewa Maryamu tana ƙaunar sa kuma abin da ta yi ya nuna cewa tana da ƙarfin zuciya. Don haka, ya kamata a yaba mata don yadda ta bayar hannu sake.
Bayan da Yesu ya gama magana, ba wanda ya sake ce wa Maryamu kome. Yahuda ya bar wurin, kuma bayan hakan, ya shirya yadda zai ci amanar Yesu. Ba shakka, Maryamu ta yi farin ciki domin abin da Yesu ya faɗa. Kuma da alama ta yi tunani sosai a kan hakan. ꞌYan kwanaki bayan haka, abin da Yesu ya faɗa cewa za a binne shi ya faru, kuma a lokacin ne Maryamu ta fahimci abin da ya faɗa. An kama Yesu, an yi masa sharri, an yanke masa hukunci, an kashe shi kuma aka binne shi. Babu shakka, wannan mata mai tausayi da kuma alheri ta yi baƙin ciki sosai don abin da ya faru. Abin da Yesu ya gaya mata ya taꞌazantar da ita a wannan mawuyacin lokaci.
Kwana uku bayan mutuwar Yesu, wani abin ban mamaki ya faru, an ta da Ubangiji Yesu! Ba da daɗewa ba, ya bayyana ga almajiransa fiye da 500. Mai yiwuwa a wannan lokaci ne Yesu ya umurce su su yi waꞌazin labari mai daɗi ga “mutanen dukan alꞌummai.” (Mat. 28:19, 20) Yesu ya ce a duk inda aka ba da ‘labari mai daɗin,’ za a kuma gaya wa mutane yadda Maryamu ta nuna masa ƙauna da kuma sauƙin kai! Babu shakka, Maryamu ba ta taɓa yin da na sani don yadda ta ba wa Ubangijinta abu mafi daraja da take da shi ba. Har iya rayuwarta, ba ta manta da yadda Yesu ya yaba mata domin bangaskiyarta da ƙarfin zuciyarta ba, saꞌad da ya ce: “Ta yi abin da za ta iya yi.”
Ka karanta labarin a:
Mene ne raꞌayinka?
A waɗanne hanyoyi ne Maryamu ꞌYarꞌuwar Liꞌazaru ta nuna ƙarfin zuciya?
Ka Yi Bincike Sosai
1. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da halayen Maryamu da ꞌyarꞌuwarta Marta? (Luk. 10:39, 40; Yoh. 11:20; ia 173 sakin layi na 5-6 da 176 sakin layi na 17) Ka duba hoto na 1
Hoto na 1
2. Ta yaya Yesu ya yi dabam da wasu malaman addinai a zamaninsa? (w99-E 9/1 30 sakin layi na 1-4-wcgr)
3. Me ya sa mān da Maryamu ta zuba a kan Yesu yake da tsada sosai? (“mān ƙamshi mai tsada sosai” Mat. 26:7, nwtsty-wcgr) Ka duba hoto na 2
Indian nard: © Haijie Lu, licensed under CC BY-NC 4.0. Source; dried jatamansi: wasanajai/stock.adobe.com; alabaster jar: © The Trustees of the British Museum. Licensed under CC BY-NC-SA 4.0. Source
Hoto na 2: Fure da kuma jijiyar itacen Nardostachys jatamansi. Da alama, da su ne aka yi mān da Maryamu ta zuba ma Yesu. Akwai kuma hoton kwalbar alabasta
4. A zamanin dā, idan mutum ya zuba māi a kai da ƙafafun mutum, me hakan yake nufi? (w11 1/1 6 sakin layi na 4, da ƙarin bayani)
Ka Yi Tunani a kan Darussan
Yesu ya ce Maryamu “ta zaɓi abu mai kyau”—domin ta sa Jehobah farko a rayuwarta. (Luk. 10:42) Ta yaya za mu yi koyi da ita a yau? Ka duba hoto na 3
Hoto na 3
Yesu ya yaba wa Maryamu domin “ta yi abin da za ta iya yi.” Bisa ga hakan, mene ne ya fi muhimmanci a wurin Jehobah yayin da muke bauta masa? (Mar. 12:29, 30; 14:8)
A waɗanne hanyoyi ne za ka iya yin koyi da irin ƙarfin zuciya da Maryamu ta nuna?
Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?
Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?
Me ya sa kake godiya domin da alama an zaɓi Maryamu ꞌyarꞌuwar Liꞌazaru ta yi mulki tare da Kristi a sama?
Ƙarin Darussa
Mene ne yara za su iya koya daga wurin Maryamu da Marta da kuma Yesu game da yin abota? Ka kalli bidiyon nan don ka ga amsar.
Ka karanta talifin nan don ka ga yadda Yesu ya daraja kyauta mai tsada da Maryamu ta ba shi da kuma kyautar ƙananan saɓar kuɗi da wata gwauruwa ta bayar.