Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wcg babi na 45 pp. 204-207
  • “Ni Mai Zunubi Ne”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ni Mai Zunubi Ne”
  • Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Bincike Sosai
  • Ka Yi Tunani a kan Darussan
  • Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
  • Ƙarin Darussa
  • Ya Zama Dutse
    Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
  • Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah da Yesu Suke Tunani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
wcg babi na 45 pp. 204-207

45 BITRUS

“Ni Mai Zunubi Ne”

Hoto
Hoto

BITRUS mutum ne da ke aiki da ƙwazo a matsayinsa na mai kamun kifi, kuma yana yin aikin tare da wasu membobin iyalinsa. Shi mai ƙarfin zuciya ne, kuma ba ya tsoron faɗan abin da ke zuciyarsa ko ya yi abin da yake ganin ya dace. Wata rana, ɗanꞌuwansa Andarawus ya zo wurinsa a guje kuma ya gaya masa cewa: “Mun samo Almasihu.” Nan take Bitrus ya je wurin Yesu kuma ya zama mabiyinsa.

Bayan ꞌyan watanni, Yesu ya je Kafarnahum inda Bitrus yake zama kuma yake aikin kamun kifi. A lokacin da Yesu ya haɗu da Bitrus, Bitrus ya gaji sosai domin tun da dare yana ta ƙoƙarin kama kifi amma bai kama ko ɗaya ba. Sai Yesu ya gaya masa ya je inda ruwan yake da zurfi kuma ya sake jefa ragarsa. Bitrus ya yi shakka domin ba a yawan kama kifi da rana. Sai Bitrus ya ce: “Mun yi fama dukan dare, ba mu kama kome ba.” Duk da haka, ya yi abin da Yesu ya gaya masa. Jim kaɗan sai suka kama kifaye da yawa, har suka cika jiragen ruwa guda biyu kuma jiragen suka soma nitsewa! Abin da Yesu ya yi ya ba ma Bitrus mamaki sosai kuma tsoro ya kama shi. Sai ya durƙusa a gaban Yesu kuma ya ce: “Ka rabu da ni Ubangiji, domin ni mai zunubi ne.” Bitrus ya ji kamar bai cancanci ya kasance tare da Ɗan Allah wanda yake da ikon yin abin ban mamaki kamar haka ba. Sai Yesu ya kwantar masa da hankali ta wurin gaya masa cewa: “Ka daina jin tsoro, daga yanzu, za ka soma jawo mutane kamar yadda ake kama kifi.”

Bitrus yana durƙusawa a gaban Yesu, Yesu kuma yana zaune a gaban jirgin ruwa. Masu kamun kifi suna ƙoƙarin jan ragarsu, yayin da jirgin ruwansu ya cika da kifi.

Yesu ya ga halaye masu kyau da Bitrus yake da su, kuma daga baya ya zaɓe shi ya zama ɗaya daga cikin manzanninsa 12. Bitrus ya nuna ƙarfin zuciya a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, idan Yesu ya faɗi abin da manzanninsa ba su gane ba, Bitrus yakan gaya masa ya sake bayyana musu. Saꞌad da Yesu ya yi tafiya a kan ruwa, Bitrus kaɗai ne ya yi ƙoƙarin yin abin da Yesu ya yi.

Bitrus yana yawan faɗan abin da bai kamata ya faɗa ba. Don haka, saꞌad da aka yi masa gyara, ya bukaci ƙarfin zuciya don ya karɓi gyarar kuma ya yi canji

Bitrus ya nuna ƙarfin zuciya a wata hanya dabam. Idan aka yi wa mutum gyara, zai bukaci ƙarfin zuciya domin ya iya bincika kansa da kyau, ya gane kuskurensa kuma ya yi canje-canje. Saꞌad da Yesu ya gaya musu cewa za a kashe shi, Bitrus ya tsawata masa cikin kuskure, cewa: “Ubangiji, kada ka yi wa kanka irin wannan fatan.” Sai Yesu ya tsawata masa sosai domin abin da ya faɗa bai yi daidai da nufin Allah ba, kuma irin abin da Shaiɗan zai so ya faɗa ke nan. Akwai kuma lokuta da yawa da Yesu ya yi wa Bitrus gyara. Amma da yake Bitrus mai sauƙin kai ne, ya saurari Yesu kuma ya yi abin da Yesu ya gaya masa.

A dare na ƙarshe kafin ya mutu, Yesu yana so ya koya wa Manzanninsa yadda za su nuna sauƙin kai, sai ya soma wanke ƙafafunsu kamar yadda bawa yake yi wa maigidansa. Sai Bitrus ya ce wa Yesu: “Ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Da Yesu ya yi masa gyara, sai Bitrus ya faɗi abin da ya yi dabam da wanda ya faɗa da farko. Ya gaya ma Yesu ya wanke har ma da hannayensa da kuma kansa ba ƙafafunsa kawai ba. Yesu ya sake yi masa gyara. Daga baya, Yesu ya ce dukan manzanninsa za su gudu su bar shi. Amma Bitrus ya ce ba zai taɓa barin Yesu ba ko da sauran sun bar shi! Yesu ya ce Bitrus zai yi mūsun sanin sa sau uku a daren.

Bayan ꞌyan awoyi, sai sojoji suka zo suka kama Yesu. Bitrus ya yi ƙarfin zuciya ya bi su daga nesa don ya ga inda za su kai Yesu. Sun kai Yesu gidan shugaban firistoci, suka ci zalin sa kuma suka yanka masa hukunci a kan abin da bai yi ba. A daidai lokacin, Bitrus yana cikin farfajiyar gidan. Wasu mutane da ke wurin sun ga Bitrus kuma sun gane cewa shi mabiyin Yesu ne. Sau uku Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu, kamar yadda Yesu ya faɗa.

Nan take Yesu ya fito daga gidan kuma ya haɗa ido da Bitrus. Bitrus ya yi baƙin ciki sosai don abin da ya yi. Ya bar farfajiyar, “ya fita waje, ya yi kuka sosai.” Bayan wasu awoyi, aka kashe abokinsa Yesu, kuma Bitrus ya yi baƙin ciki sosai irin wanda bai taɓa yi ba. Duk da cewa Bitrus ya yi babban kuskure, bai karaya ba. Ya ci-gaba da bauta ma Jehobah tare da sauran manzannin. Da aka ta da Yesu, ya bayyana ga Bitrus saꞌad da yake nan shi kaɗai. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abin da Yesu ya faɗa masa ba, amma mun san cewa yadda Yesu ya gafarta masa, ya ƙarfafa shi kuma ya sa hankalinsa ya kwanta.

Bayan ꞌyan makonni, Yesu ya haɗu da manzanninsa a Tekun Galili, kuma ya yi wa Bitrus alheri. Kamar yadda ya yi mūsun sanin Yesu sau uku, Yesu ya ba Bitrus damar nuna masa cewa yana ƙaunar sa har sau uku. Sai Yesu ya ba ma Bitrus wani aiki mai muhimmanci, ya ce masa: “Ka ciyar da ꞌyan tumakina.” A Babi na 49, za mu ga yadda Bitrus ya yi abin da Yesu ya ce masa ya yi, da kuma yadda ya nuna ƙarfin zuciya har ƙarshen rayuwarsa.

Ka karanta labarin a:

  • Matiyu 14:​23-29; 15:15; 16:​21-23; 18:21; 19:​27-29; 26:​69-75

  • Markus 14:​27-31, 53, 54; 16:7

  • Luka 5:​1-11; 12:41; 22:​61, 62; 24:​33, 34

  • Yohanna 1:​40-42; 13:​3-10, 36-38; 21:​15-17

Mene ne raꞌayinka?

A waɗanne hanyoyi ne Bitrus ya nuna ƙarfin zuciya?

Ka Yi Bincike Sosai

  1. 1. Ta yaya masu kamun kifi suke yin aikinsu a zamanin Litafi Mai Tsarki? (it “Farauta da Kamun Kifi” sakin layi na 6-7-wcgr) Ka duba hoto na 1

    Wani mai kamun kifi a ƙarni na farko yana ɗinka ragar kamun kifi.

    Hoto na 1

  2. 2. Me ya sa Yesu ya ba wa Siman suna Kefas (Bitrus)? (w24.06 28 sakin layi na 11)

  3. 3. Mene ne Yesu yake nufi saꞌad da ya ce ma Bitrus da Andarawus su zama “masu jawo mutane kamar yadda ake kama kifi”? (Mat. 4:​18-20; w16.05 9 sakin layi na 3-4) Ka duba hoto na 2

    Masu kamun kifi guda huɗu a ƙarni na farko suna jan ragar da ta cika da kifaye zuwa cikin jirgin ruwa.

    Hoto na 2

  4. 4. Jim kaɗan kafin Yesu ya koma sama, ya tambayi Bitrus cewa: “Kana ƙauna ta fiye da abubuwan nan?” Mene ne wataƙila Yesu yake nufi da wannan tambayar? (w17.05 22 sakin layi na 2)

Ka Yi Tunani a kan Darussan

  • Mene ne za mu iya koya daga labarin Bitrus game da bauta ma Jehobah ko da muna fama da wata kasawa? Ka duba hoto na 3

    Hotuna: Wani matashi yana fama da kasawarsa. Hotuna uku na gaba sun nuna abubuwan da suka faru ɗaya bayan ɗaya. Matashin yana kallon kansa a madubi yayin da yake tunani a kan kasawarsa. ꞌYanꞌuwa guda biyu suna ƙarfafa matashin da Littafi Mai Tsarki. Matashin yana karanta Littafi Mai Tsarki daga dakalin magana a taro.

    Hoto na 3

  • Ta yaya yin tunani a kan yadda Jehobah da Yesu suka gafarta ma Bitrus zai taimaka maka?

  • Ta yaya za ka yi koyi da irin ƙarfin zuciya da Bitrus ya nuna?

Ka Ƙara Yin Tunani Sosai

  • Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?

  • Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?

  • Me ya sa kake farin ciki cewa Bitrus yana cikin waɗanda za su yi sarauta da Yesu a sama?

Ƙarin Darussa

Ta yaya iyaye za su iya yin amfani da misalin Bitrus don su koya ma yaransu game da yadda Jehobah yake nuna jinƙai? Ka kalli bidiyon nan don ka ga amsar.

Jehobah Yana Gafartawa (9:40)

Ka karanta labarin nan don ka ga dalilin da ya sa Bitrus bai bar Yesu ba duk da cewa sauran sun bar Yesu.

“Ya Kasance da Aminci a Lokacin Gwaji” (ia 188-195)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba