30 GWAURUWAR ZAREFAT
Ta Nuna Ƙarfin Zuciya a Lokaci Mai Wuya Sosai
AKAWAI wata mata da mijinta ya mutu, kuma ita da yaronta suna zama a Zarefat. An daɗe ba a yi ruwan sama a Zarefat ba, don haka koꞌina ya bushe. Ba a yi noma ba, kuma mutane suna fama da rashin abinci. Allah ya ba wa Israꞌilawa doka a kan yadda za a tanada wa gauraye da marayu abubuwan da suke bukata. Amma da yake tana zama a Zarefat, ba za ta amfana daga tanadin ba. Zarefat wani ɓangare ne a Sidon, kuma sunan sarkin da ke mulki a warin shi ne Ethbaal. Yana bauta wa wata allahiya da ake kira Ashtoret. Kuma mai yiwuwa ya yi aiki a matsayin firist na allahiyar. Mutanen da suke bauta mata suna yin munanan abubuwa don su burge ta. Babu shakka, ya yi wa gwauruwar wuya ta zauna a tsakanin irin mutanen nan. Mai yiwuwa ta yi wa kanta tambaya cewa: Me zai faru da ni da ɗana? Akwai wanda ya san cewa ina bukatar taimako kuwa? Shin, akwai wanda ya damu da mu?
Ta ci-gaba da yin iya ƙoƙarinta wajen samun abin da ita da yaronta za su ci. Amma, yanayin sai ƙara muni yake yi. Kuma ba da daɗewa ba, turi zai kai bango.
Amma Jehobah yana ƙaunar ta, kuma ya ga cewa halinta ya fita dabam da na sauran mutanen. Ko da yake tana zama a wurin da mutane suke bauta wa allolin ƙarya, ta ba da gaskiya ga Jehobah. Wataƙila ta ji game da Jehobah da abubuwan da ya yi wa mutanensa, kuma sun burge ta sosai. Hakan ya sa ta kasance da tabbaci cewa shi ne Allah na gaskiya. Kusan shekaru 1,000 bayan hakan, Yesu ya yi magana game da ita kuma ya ce Jehobah ya taimaka mata. Ta yaya Jehobah ya yi hakan?
Jehobah ya tura annabi Iliya zuwa Zarefat, kuma ya gaya masa cewa zai haɗu da wata gaurawa da za ta riƙa ba shi abinci a wurin. Da ya isa wurin, ya ga wata mata da take tattara itace. Ya yi mata magana cikin alheri, kuma ya roƙe ta ta ba shi ruwa. Ko da yake ba ta taɓa ganin Iliya ba, ta tashi ta je ta kawo masa ruwan. Mai yiwuwa ta gane cewa shi annabin Jehobah ne ta wurin rigar da ya saka, da kuma yadda ya yi mata magana cikin alheri. Wataƙila a wannan lokacin, Iliya yana tunanin ko ita ce matar da Jehobah ya turo sa wurinta. Don ya tabbatar da hakan, sai ya ce mata, ki kuma kowa mini ɗan burodi in ci.
Da ta ji hakan, sai ta gaya masa ainihin yanayin da suke ciki. Ta soma da cewa, “Na rantse da Yahweh Allahnka mai rai.” Hakan ya nuna ta gaskata cewa Jehobah ne Allah na gaskiya kuma “Shi ne Allah Mai Rai.” (Irm. 10:10) Sai ta gaya wa Iliya cewa ba ta da burodi, sai dai ɗan garin fulawa da kuma ɗan māi. Ta kuma ƙara da cewa, “Ina neman itacen dafuwa da zan kai gida in yi abinci da shi, ni da yarona mu ci mu mutu.”
Duk da cewa ita da ɗanta suna fama da yunwa, ta ba wa annabin Jehobah raguwar abincin da take da shi
Sai Iliya ya gaya mata cewa: “Kada ki ji tsoro.” Mai yiwuwa hakan ya ba ta mamaki. Ta yi mamakin yadda ya gaya mata cewa kada ta ji tsoro domin a ganinta yunwa zai kashe ta da yaronta. Duk da cewa ba ta fahimci abin da yake nufi ba, ba ta yi gardama ba. Sai Iliya ya gaya mata abin da Jehobah ya ce zai yi mata. Ya gaya mata cewa, ba za su taɓa rasa garin fulawa da māi da suke bukata ba, da zai kai su har lokacin da za a soma ruwan sama!
A nan ne gizo ke saƙa. Shin, za ta nuna bangaskiya kuma ta yi abin da Iliya ya gaya mata ta yi? Za ta ba wa Iliya ɗan abincin da ya rage mata? Mai yiwuwa ta ji labarin abubuwan ban mamakin da Jehobah ya yi wa mutanensa. Hakan ya sa ta gaskata cewa wannan ma ba zai gagari Jehobah ba. Duk da haka, tana bukatar ƙarfin zuciya don ta dogara ga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta je ta yi dukan abin da Iliya ya faɗa mata.”
Jehobah ya cika alkawarin da ya yi mata, kuma ya albarkace ta don bangaskiyar da ta nuna. Jehobah ya tabbata cewa ba su rasa garin fulawa da māi da suke bukata ba. Ƙari ga haka, Jehobah ya yi mata wani abu kuma mai ban mamaki. Ya yi amfani da Iliya wajen ta da ɗanta da ya mutu. Wannan shi ne ƙaro na farko da aka ta da wani daga mutuwa a Littafi Mai Tsarki. Babu shakka, hakan ya ƙarfafa bangaskiyar wannan gwauruwar. Tun daga lokacin, labarinta ya ƙarfafa mutane da yawa su riƙa nuna irin wannan bangaskiyar.
Ka karanta labarin a:
1 Sarakuna 17:8-24
Mene ne raꞌayinka?
A waɗanne hanyoyi ne gwauruwar Zarefat ta nuna ƙarfin zuciya?
Ka Yi Bincike Sosai
1. Mene ne mutanen Sidon suke bauta wa, kuma mene ne suke yi a bautarsu? Ta yaya bautar ta shafi Israꞌilawa? (it “Sidon” sakin layi na 6-wcgr) Ka duba hoto na 1
Penta Springs Limited/Alamy Stock Photo
Hoto na 1: Gunkin Ashtoret, daga wajen shekara ta 1500 K.H.Y.
2. Wace alaƙa ce ke tsakanin Sarki Ethbaal da Sarki Ahab? (it “Ethbaal”-wcgr)
3. Mutanen Finikiya suna bauta wa allahiyar nan Ashtoret. Waɗanne abubuwa ne ake yi a yau da suke da alaƙa da wannan addinin? (g93 11/22 13 sakin layi na 1-4-wcgr)
4. Saꞌad da ɗanta ya mutu, me ya sa gwauruwar ta tambayi Iliya cewa: “Ka zo ne domin ka sa Yahweh ya tuna da zunubaina, ka kuma jawo mutuwar yarona?” (1 Ki. 17:18; w14 2/15 15 sakin layi na 4-5) Ka duba hoto na 2
Hoto na 2
Ka Yi Tunani a kan Darussan
Duk da cewa gwauruwar Zarefat tana zama a garin da ake bauta wa gumaka, Jehobah ya san da zaman ta. Mene ne hakan ya koya mana game da Jehobah da kuma raꞌayinsa game da mutanen da ke yankinmu? (A. M. 10:35)
Mene ne Kiristocin da suke fama da rashin kuɗi za su iya koya daga bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya da gwauruwar Zarefat ta nuna? Ka duba hoto na 3
Hoto na 3
A waɗanne hanyoyi kuma za ka iya yin koyi da irin ƙarfin zuciya da gwauruwar Zarefat ta nuna?
Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?
Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?
Mene ne zan so in tambayi gwauruwar Zarefat idan muka haɗu a aljanna?
Ƙarin Darussa
Ta yaya za mu nuna cewa dangantakarmu da Jehobah ce ta fi kuɗi ko dukiya muhimmanci kamar yadda gwauruwar Zarefat ta yi? Ka karanta talifin nan don ka ga amsar.
“Samun Tagomashin Allah Yana Kai Ga Samun Rai Na Har Abada” (w11 2/15 13-17)
Me ya tabbatar mana cewa Jehobah yana ganin duk abin da muka yi don mu nuna cewa mun ba da gaskiya gare shi? Ka karanta talifin nan don ka ga amsar.
“Shin, Jehobah Yana Ganin Abin da Kake Yi?” (w03-E 5/1 28-31-wcgr)