31 WATA ƘARAMAR YARINYA ꞌYAR ISRAꞌILA
Ta Yi Magana Game da Allahnta da Ƙarfin Zuciya
BA MU san sunanta ba, amma mun san wani abu mai muhimmanci game da ita. Ta yi rayuwa a lokacin da Sarki Jehoram yake mulki. A lokacin, Sarki Jehoram da alʹummar Israꞌila suna yi wa Jehobah rashin biyayya. Hakan ya sa Jehobah ya ƙyale Suriyawa su yi ta kawo musu hari. Wata rana, sojojin Suriya sun kama wata ƙaramar yarinya kuma suka kai ta ƙasarsu.
Babu shakka, ta ji tsoro kuma danginta sun yi baƙin ciki sosai. A wurin, ta zama baiwar matar Naꞌaman, shugaban sojojin Suriya. Da alama cewa yarinyar ta yi iya ƙoƙarinta wajen sabawa da sabon wuri da aka kawo ta. Kuma wataƙila ta lura cewa Naꞌaman da iyalinsa suna cikin baƙin ciki domin yana fama da kuturta. Cutar tana da tsanani, tana jawo ciwo-ciwo a jikin mutum kuma ƙila ba za ta warke ba.
Duk da cewa tana zama da mutanen da suke bauta wa allolin ƙarya, ta tausaya musu kuma ta nuna ƙarfin zuciya
ꞌYar ƙaramar yariyar tana da hankali sosai. Duk da cewa ta san Naꞌaman maƙiyin mutanen Israꞌila ne, ta tausaya wa shi da matarsa kuma ta san cewa zai iya warkewa. Wataƙila iyayenta sun gaya mata labaran abubuwa masu ban mamaki da Jehobah ya sa annabi Elisha ya yi. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa Elisha ya taɓa warkar da mai fama da kuturta ba, yarinyar ta tabbata cewa Allahnta Jehobah zai iya taimaka wa annabinsa ya yi duk abin da yake so.
Ba mamaki ta yi ta tunani ko ta gaya musu game da Jehobah ko ta yi shiru. Ta san cewa hakan zai iya jefa ta cikin matsala. Naꞌaman yana bauta wa allahn Suriyawa mai suna Rimmon kuma yana yawan kai sarkin Suriyawa ibada a haikalin Rimmon. Mutanen Suriya sun yi imani cewa allahnsu na da ƙarfi sosai, har yana iya kawo ruwan sama mai ƙarfi da tsawa. Don haka, ba ta san abin da Naꞌaman zai yi ba idan ta gaya masa game da Allahnta Jehobah. Ƙila ta ga kamar zai yi fushi idan ta gaya masa cewa Jehobah zai iya warkar da shi. Abin da allahnsa ya gagara yi ke nan. Babu shakka, yarinyar ta yi adduꞌa cewa Jehobah ya ba ta ƙarfin zuciya. Sai ta gaya wa matar Naꞌaman cewa: “Da a ce maigida zai tafi wurin annabin da yake a birnin Samariya da zai warke.”
Abin da ta faɗa da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki ke nan. Ba dogon bayani ta yi ba. Amma sakamakon abin da ta faɗa na da ban mamaki. Bayan da ta gaya wa matar Naꞌaman, sai Naꞌaman ya gaya wa Sarki Ben-hadad abin da yarinyar ta faɗa. Bayan haka, sai sarkin Suriya ya ce wa Naꞌaman ya je Israꞌila. Kuma ya ba shi wasiƙa ya kai wa sarkin Israꞌila Jehoram. A cikin wasiƙar ya roƙa cewa a warkar da Naꞌaman.
Da Naꞌaman ya tafi ƙasar Israꞌila, sai dukan gidansa suka jira don su ga abin da zai faru. Babu shakka, ꞌyar ƙaramar yarinyar nan ta yi ta adduꞌa tana roƙon Jehobah ya warkar da Naꞌaman don ya nuna cewa shi ne Allah na gaskiya. Wataƙila ya yi kwanaki ko makonni kafin ya dawo. Ka yi tunanin irin farin ciki da mutanen da ke gidansa suka yi da suka gan shi yana dawowa. Sun ga yadda aka warkar da shi, kuma jikinsa ya yi sumul kamar na ɗan yaro!
Ka yi tunanin yadda yarinyar take saurara da kyau saꞌad da ake ba da labarin abin da ya faru. Yadda Elisha ya marabci Naꞌaman kuma ya ba shi wasu umurnan da suka ɓata masa rai. Yadda bayin Naꞌaman suka roƙe shi ya bi umurnin. Yadda Naꞌaman ya gane cewa yana bukatar ya ƙasƙantar da kansa. Da kuma yadda ya nitsar da kansa sau bakwai a Kogin Jodan kuma ya warke. Babu shakka, abin da ya fi sa ta farin ciki shi ne abin da ya faru bayan da aka warkar da Naꞌaman. Tun daga lokacin, Naꞌaman ya soma bauta wa Jehobah kamar yadda take yi!
Dukan abubuwan ban mamakin nan sun faru ne domin wata ƙaramar yarinya ta nuna ƙarfin zuciya kuma ta yi magana game da Allah da kuma annabinsa. Ko da yake ba mu san sunanta ba, Jehobah ya sani. Idan mu ma mun kasance da ƙarfin zuciya kamar yarinyar nan, za mu haɗu da ita a aljanna a lokacin da Jehobah zai ta da ita daga mutuwa. Ka yi tunanin lokacin da za mu haɗu da ita, mu san sunanta kuma mu ji sauran abubuwan da suka faru a rayuwarta!
Ka karanta labarin a:
2 Sarakuna 5:1-19
Mene ne raꞌayinka?
A waɗanne hanyoyi ne ƙaramar yarinya ꞌyar Israꞌila ta nuna ƙarfin zuciya?
Ka Yi Bincike Sosai
1. Mene ne Suriyawa suke yi da wataƙila ya sa ꞌyar yarinyar nan ta ji tsoro? (w96 5/15 8 sakin layi na 3-wcgr) Ka duba hoto na 1
Courtesy of Musée du Louvre, Paris
Hoto na 1: Gunkin mutanen Suriya na dā, wataƙila shi ne Rimmon
2. Ka kwatanta abin da ke faruwa da mutumin da yake fama da kuturta. (it “Kuturta” sakin layi na 3-5-wcgr)
3. Me ya sa Elisha ya ƙi karɓan kyautar da Naꞌaman ya ba shi? (w05 8/1 28 sakin layi na 2)
4. Me ya sa Elisha ya tabbata cewa Jehobah zai gafarta wa Naꞌaman don ya rusuna a gaban Rimmon? (2 Sar. 5:18, 19; w05 8/1 28 sakin layi na 3) Ka duba hoto na 2
Hoto na 2
Ka Yi Tunani a kan Darussan
Naꞌaman shugaban sojojin Suriya ne da ya kawo wa Israꞌila hari. Duk da haka, Jehobah ya warkar da shi. Mene ne hakan ya koya maka game da jinƙai da kuma rashin nuna bambanci da Jehobah yake yi? Ka duba hoto na 3
Hoto na 3
Ta yaya labarin ƙaramar yarinyar nan ya ƙarfafa ka ka yi waꞌazi ko da kana jin tsoro?
A waɗanne hanyoyi ne kuma za ka iya yin koyi da irin ƙarfin zuciya da ƙaramar yarinyar nan ta nuna?
Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?
Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?
Mene ne zan so in tambayi ƙaramar yarinyar idan muka haɗu a aljanna?a
Ƙarin Darussa
Da yake ba a ambata sunan ƙaramar yarinyar a Littafi Mai Tsarki ba, hakan yana nufin ba ta da muhimmanci ga Jehobah ne? Ka karanta talifin nan don ka ga amsar.
“Me Ya Sa Ba a Ambata Sunayen Wasu Mutane a Littafi Mai Tsarki Ba?” (w13 8/1 10-wcgr)
Ka kalli bidiyon nan don ka ga yadda matasa za su iya nuna ƙarfin zuciya kamar ƙaramar yarinya ꞌyar Israꞌila.
a Idan yarinyar ta yi girma kafin ta mutu, haka za a ta da ita a nan gaba.