Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wcg babi na 29 pp. 134-137
  • Jehobah Ne Allahna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ne Allahna
  • Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Bincike Sosai
  • Ka Yi Tunani a kan Darussan
  • Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
  • Ƙarin Darussa
  • Allahnsa Ya Ƙarfafa Shi
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Sami Ƙarfafawa Daga Wajen Allahnsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ya Lura, Kuma Ya Jira
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ka Taba Jin Kadaici da Tsoro?
    Ku Koyar da Yaranku
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah da Ƙarfin Zuciya
wcg babi na 29 pp. 134-137

29 ILIYA

Jehobah Ne Allahna

Hoto
Hoto

KAMAR tsawar da aka yi a lokacin da babu hadari, haka labarin Iliya ya ɓullo a Littafi Mai Tsarki. Ƙaro na farko da muka ji game da shi, shi ne lokacin da ya kawo wa wani sarki saƙo mai nauyi. Sarakuna shida na farko da suka yi mulki a kan ƙabilu goma na Israꞌila mugaye ne sosai. Ahab ne sarki na bakwai, kuma a gun Jehobah halinsa ne ya fi muni. Ahab ya auri wata muguwar mata. Ita ꞌyar sarkin Sidon ne. Ahab yana bauta wa gumaka. Amma abin da matarsa take yi ya fi muni. Tana bauta wa allahn ƙarya mai suna Baal, kuma wataƙila hakan ya ƙunshi yin hadaya da yara. Ƙari ga haka, ta ƙarfafa maigidanta da kuma dukan mutanen Israꞌila su riƙa bauta wa Baal. Ana nan wata rana, sai Iliya ya zo wurin Ahab. Jehobah ne ya turo shi wurin sa. Iliya ya gaya wa Ahab cewa abin da yake yi mugun abu ne. Ya kuma gaya masa matakin da Jehobah zai ɗauka.

Don Iliya ya samu ya idar da wannan saƙon, yana bukatar ya taka daga Gilead zuwa Samariya. Wannan ba tafiya mai sauƙi ba ce domin akwai tuddai da yawa a wurin. Kuma idan ya isa Samariya, zai bukaci ya shiga babban fadar Sarki Ahab. Ana kiran fadar nan “gidan haƙoran giwa.” Wataƙila ana yin hakan ne don yadda aka yi wa gidan ado da haƙoran giwa. (1 Sar. 22:39) Ka yi tunanin yadda annabi Iliya sanye da rigar da aka yi da gashin dabba kuma ya yi ɗamara da fata, ya shiga babban fadar don ya gaya wa sarki cewa allahnsa Baal ba kome ba ne! Idan Jezebel tana tare da Ahab lokacin da Iliya ya idar da wannan saƙon, babu shakka za ta yi fushi sosai. Ahab da Jezebel sun yi imani cewa allahnsu Baal yana da ikon sa a yi ruwan sama. Amma Iliya ya nuna ƙarfin zuciya, kuma ya gaya musu cewa allahnsu ba zai taimaka musu ba. Jehobah ya ce ba za a yi ruwan sama a ƙasar ba, kuma za a yi shekaru ana fama da rashin ruwa har sai bawan Jehobah ya sanar cewa za a sake yin ruwan!

Iliya yana yi wa sarki Ahab magana a fadarsa. Ahab yana zaune yana saurarar Iliya. Jezebel tana tsaye tana ƙoƙarin ƙaryata shi. Wasu kuma suna kallon sa suna shakka.

Me ya taimaka wa Iliya ya yi magana da ƙarfin zuciya haka? Ɗaya daga cikin abin da ya taimaka masa shi ne, abin da ya faɗa game da Jehobah. Da ya fara magana, ya ce: “Na rantse da Yahweh Allah Mai Rai na Israꞌila, wanda nake bauta masa.” Furucin nan “wanda nake bauta masa” a Ibrananci tana nufin “wanda nake tsaye a gabansa.” Ko da yake Iliya ya tsaya a gaban sarki mai iko sosai saꞌad da yake idar da saƙon da Jehobah ya ba shi, ya san cewa a matsayinsa na bawan Jehobah, yana nan a gaban Jehobah. Duk da cewa Ahab da Jezebel suna da iko sosai kuma su abin tsoro ne, su ba kome ba ne idan aka gwada su da Jehobah. Babu shakka, sanin hakan ya sa Iliya ya kasance da ƙarfin zuciya!

Iliya ya yi wa mugun sarki da sarauniyarsa da kuma alꞌummar Israꞌila da suka yi tawaye magana da ƙarfin zuciya. Kuma ya dogara ga Jehobah saꞌad da ya ji tsoro

Iliya ya ci-gaba da bauta wa Jehobah da ƙarfin zuciya. Ya nuna hakan ta wajen ɓuya a wani kogo a lokacin da ake yunwa kuma ba a ruwan sama kamar yadda Jehobah ya gaya masa. A wurin, wani tsuntsu ne yake kawo masa abinci, kuma yana samun ruwan sha daga wani ɗan rafi. Ya kuma nuna ƙarfin zuciya saꞌad da Jehobah ya ce masa ya je Sidon ya taimaka wa wata gwauruwa da ta nuna bangaskiya. Ya bukaci ƙarfin zuciya domin mahaifin Jezebel ne sarki a wannan ƙasar. Ƙari ga haka, Iliya ya nuna ƙarfin zuciya a lokacin da ya tinkari annabawa 450, kuma ya nuna musu cewa Jehobah ne Allah na gaskiya. A dukan rayuwarsa, Iliya ya dogara ga Jehobah, kuma ya nuna cewa Jehobah ne Allahnsa. Hakan ya jitu da maꞌanar sunansa wato, Jehobah ne Allahna.

Amma, “Iliya mutum ne kamar mu.” (Yak. 5:17) A wasu lokuta ya ji tsoro. Duk da abin mamakin da Jehobah ya yi a Babban Tudun Karmel, Ahab ya ƙi ya tuba kuma Jezebel ta ba da umurni cewa a kashe Iliya. Hakan ya sa tsoro ya kama shi. Sai ya gudu ya ɓuya. Iliya ya karaya sosai, har ma ya gaya wa Jehobah cewa ya fi son ya mutu. Ya ji kamar bai da wani amfani, kuma ya ce bai fi kakaninsa waɗanda suka mutu ba. Duk da haka, Jehobah ya yi haƙuri ya saurare shi. Iliya ya kuma gaya wa Jehobah sau biyu cewa yana ganin kamar shi kaɗai ne ya rage, kuma yana jin tsoro. Ban da haka ma, yana ganin aikin da ya yi a matsayin annabi aikin banza ne. Amma Jehobah ya gaya wa annabinsa cewa, akwai mutane da yawa da suka riƙe amincinsu kamar yadda ya yi. Kuma ya gaya masa cewa yana da daraja a wurinsa. Ƙari ga haka, Jehobah ya ce zai ba shi mataimaki, kuma ya sa Iliya ya koyar da shi don shi ma ya zama annabi.

Jim kaɗan bayan hakan, sai Iliya ya je ya nemi Elisha. Su biyu sun ci-gaba da bauta wa Jehobah, da idar da saƙonninsa a lokaci mai wuya. Elisha ya taimaka wa Iliya kuma ya koyi abubuwa da yawa daga wurinsa. Da taimakon Jehobah, Iliya ya sake zama mai ƙarfin zuciya kuma ya ci-gaba da hakan har ƙarshen rayuwarsa.

Ka karanta labarin a:

  • 1 Sarukuna 16:​29-33; 17:​1-10a; 18:1–19:21

  • 2 Sarukuna 3:11

Mene ne raꞌayinka?

A waɗanne hanyoyi ne Iliya ya nuna ƙarfin zuciya?

Ka Yi Bincike Sosai

  1. 1. Jehobah ya zaɓi tsuntsu ya riƙa kai wa Iliya abinci. Me ya sa hakan ya dace? (it “Hankaka” sakin layi na 5-wcgr) Ka duba hoto na 1

    Hankaka.

    Lior Kislev

    Hoto na 1

  2. 2. Waɗanne muꞌujizai ne Iliya ya yi? (it “Iliya” Na 1 sakin layi na 11-wcgr)

  3. 3. A Babban Tudun Karmel, Iliya ya tona babban rami kewaye da bagadin, sai ya ce a cika ramin da ruwa. Da yake ana rashin ruwa sosai a lokacin, a ina ne aka samo ruwa da yawa haka? (ba 17 sakin layi na 4) Ka duba hoto na 2

    Todd Bolen/BiblePlaces.com

    Hoto na 2: Babban Tudun Karmel da Tekun Meditereniya

  4. 4. Mene ne rigar Iliya take wakilta, kuma me ya sa ya wurga wa Elisha rigar a kafaɗarsa? (w14 2/1 12 sakin layi na 3-wcgr)

Ka Yi Tunani a kan Darussan

  • Ta yaya Jehobah ya bi da Iliya, kuma ta yaya hakan zai taimaka mana mu sa ya yi wa ꞌyanꞌuwanmu sauƙi su gaya mana matsalolin da suke ciki? (1 Sar. 19:​1-18) Ka duba hoto na 3

    Hotuna: Wani ɗanꞌuwa da ya manyanta yana ƙarfafa wani ɗanꞌuwa da ya yi sanyin gwiwa. An maimaita hotunan ɗaɗɗaya a gaba. Hotuna: Na 1. Ɗanꞌuwan da ya manyanta ya kira ɗanꞌuwan da ya yi sanyin gwiwa a waya. Na 2. Ɗanꞌuwan da ya yi sanyin gwiwa ya amsa wayar saꞌad da yake kwance a gadonsa. Daga baya a ranar, su biyun sun je wurin shan shayi. Ɗanꞌuwan da ya manyanta yana sauraron ɗanꞌuwan da ya yi sanyin gwiwa.

    Hoto na 3

  • Iliya ya koya wa Elisha aikin da yake yi da farin ciki. Ta yaya za mu bi misalinsa saꞌad da muke koyar da wasu kuma muka bar musu wasu ayyukan da muke yi?

  • A waɗanne hanyoyi kuma za ka iya yin koyi da irin ƙarfin zuciya da Iliya ya nuna?

Ka Ƙara Yin Tunani Sosai

  • Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?

  • Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?

  • Mene ne zan so in tambayi Iliya idan muka haɗu a aljanna?

Ƙarin Darussa

Ka kalli bidiyon nan don ka ga abin da Jehobah ya yi don ya ƙarfafa Iliya.

Za Mu Iya Kasancewa da Haƙuri Kamar Annabawa—Iliya (1:19)

Mene ne matasa za su iya koya daga yadda Iliya ya nuna ƙarfin zuciya a Babban Tudun Karmel? Ka karanta talifin nan don ka ga amsar.

“Ka Kāre Bauta ta Gaskiya!” (Jerin talifofin jw.org “Ayyuka don Nazarin Littafi Mai Tsarki”)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba