Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 61
  • Labaran Wadanda Suka Tsallake Rijiya da Baya, Mene ne Yake Nufi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Labaran Wadanda Suka Tsallake Rijiya da Baya, Mene ne Yake Nufi?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Menene Zai Faru Idan Muka Mutu?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Dalilin da Ya Sa Yesu Bai Hanzarta Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 61

Labaran Wadanda Suka Tsallake Rijiya da Baya, Mene ne Yake Nufi?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Mutane da yawa da suka tsallake rijiya da baya suka ce sun rabu da jikinsu kuma suka shiga cikin wani wuri mai kyaun gaske. Littafin nan Recollections of Death ya ce: ‘Wadansun su suna daukan wannan wata gata ce ta musamman su yi rayuwa a wata duniya.” Littafi Mai Tsarki bai ambata irin wannan aukuwa ba, amma ya fadi gaskiya cewa hakan ba wahayin wata rayuwa ba ce.

Matattu ba su san kome ba.

Littafi Mai Tsarki ya ce matattu “ba su san kome ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Idan mutum ya mutu ba ya zuwan wani waje ko soma wani tunani ba. Koyarwar cewa kurwa marar mutuwa ce ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne. (Ezekiel 18:4) Saboda haka, babu wani labari na tsallake rijiya da baya da ya nuna cewa ya faru a sama, ko hell, ko kuma a wani wajen rayuwa bayan mutuwa ba.

Li’azaru ya fadi wani abu ne cewa ya rayu bayan da ya mutu?

Labarin Littafi Mai Tsarki game da Li’azaru ya kwatanta mutuwa sarai: Yesu ya ta da shi bayan kwana hudu da mutuwa. (Yohanna 11:38-​44) Da a ce Li’azaru yana more rayuwa a wani wuri dabam ne da zai zama mugunta ne Yesu ya tashe shi ya sake rayuwa a duniya. Amma, babu wani labari daga Li’azaru game da wata rayuwa bayan mutuwa ba. Da hakan ya faru, babu shakka da Li’azaru ya yi tadin rayuwar da ya yi sa’ad da ya mutu. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda Yesu ya kwatanta mutuwar Li’azaru da barci, yana nuna cewa sa’ad da ya mutu, bai san kome ba sam.​—Yohanna 11:11-​14.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba