Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/15 p. 32
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Dalilin da Ya Sa Yesu Bai Hanzarta Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Yesu Ya Tayar da Li’azaru Daga Matattu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Menene Zai Faru Idan Muka Mutu?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/15 p. 32

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Me ya sa Yesu ya yi kuka kafin ya ta da Li’azaru daga mutuwa, kamar yadda aka rubuta a Yohanna 11:35?

Mukan yi kuka sa’ad da wani wanda muke ƙauna ya rasu don za mu riƙa kewar sa. Yesu bai yi kuka don mutuwar Li’azaru ba, ko da yake yana ƙaunarsa. Kamar yadda mahallin labarin Yohanna ya nuna, ya yi kuka ne domin yana ƙaunar iyalin Li’azaru da kuma abokansa.—Yoh. 11:36.

Sa’ad da Yesu ya sami labari cewa Li’azaru yana ciwo, bai hanzarta don ya je ya warkar da shi ba. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’ad da [Yesu] fa ya ji labari [cewa Li’azaru] yana ciwo, ya kwana biyu a wurin da yake a loton nan.” (Yoh. 11:6) Me ya sa Yesu bai hanzarta ba? Yana da dalilin yin hakan. Ya ce: “Wannan cuta ba ta mutuwa ba ce, amma domin girmar Allah ne, domin a girmama Ɗan Allah ta wurinta.” (Yoh. 11:4) Saboda haka, Yesu yana so a ga “girmar Allah” ta mutuwar Li’azaru. Ta yaya zai yi hakan? Yana so ya yi wata mu’ujiza ta musamman, wato ya ta da abokinsa daga mutuwa.

A tattaunawar da Yesu ya yi da almajiransa a wannan lokacin, ya kwatanta mutuwa da barci. Shi ya sa ya gaya musu cewa, “zan tafi, domin in tashe [Li’azaru] daga barci.” (Yoh. 11:11) Kamar yadda iyaye suke ta da ’ya’yansu daga barcin rana, haka Yesu zai ta da Li’azaru daga mutuwa. Saboda haka, bai kamata ya yi baƙin ciki don Li’azaru ya mutu ba.

To, idan haka ne, me ya sa Yesu ya yi kuka? Har ila mahallin labarin ya ba mu amsar. Sa’ad da Yesu ya ga Maryamu ’yar’uwar Li’azaru da kuma waɗanda suka zo musu ta’aziya suna kuka, sai “ya ji haushi cikin ruhunsa.” Baƙin cikin da suke yi ne ya sa Yesu “ya ji haushi cikin ruhunsa.” Wannan dalilin ne ya sa “Yesu ya yi kuka.” Babu shakka, baƙin cikin da abokan Yesu suka yi ya ɓata masa rai sosai.—Yoh. 11:33, 35.

Wannan labarin ya nuna cewa Yesu yana da ikon ta da abokanmu da ’yan’uwanmu daga matattu don su yi rayuwa cikin ƙoshin lafiya a sabuwar duniya a nan gaba. Hakan kuma ya nuna mana cewa Yesu yana juyayi ga waɗanda ɗan’uwansu ya rasu. Wani darasi kuma da za mu koya daga wannan labarin shi ne, ya kamata mu ta’azantar da waɗanda suke makoki don ɗan’uwansu ƙaunatacce ya rasu.

Ƙauna da kuma tausayin da Yesu yake ji ga abokansa ne suka sa ya yi kuka, duk da cewa ya san zai ta da Li’azaru daga mutuwa. Hakazalika, tausayi ne ya kamata ya sa mu “yi kuka tare da masu-kuka.” (Rom. 12:15) Shin yin kuka sa’ad da wani ya mutu ya nuna cewa ba mu yi imani ga tashin matattu ba ne? A’a. Babu shakka, kukan da Yesu ya yi sa’ad da Li’azaru ya rasu ko da ya san zai ta da shi ya nuna cewa yana juyayi kuma hakan misali ne mai kyau a gare mu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba