Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 52
  • Rayuwa Tana da Ma’ana Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Rayuwa Tana da Ma’ana Kuwa?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da
  • Me Ya Sa Allah Ya Halicce Mu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Za Ka Iya Zama Aminin Jehobah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Biɗar Rayuwa Mai Ma’ana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Allah Shi Ne Amini Na Ƙwarai Da Za Ka Taɓa Samu
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
Dubi Ƙari
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 52

Rayuwa Tana da Ma’ana Kuwa?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

Tambayoyi game da ma’anar rayuwa suna zuwa a fasaloli dabam-dabam kamar su, Me ya sa aka halicce mu? ko kuma Rayuwata tana da ma’ana kuwa? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dalilin da ya sa aka halicce mu shi ne mu kulla dangantaka da Allah. Ka lura da wasu abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki da suka tabbatar da hakan.

  • Allah ne Mahaliccinmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Allah] ne ya yi mu” ba mu muka halicci kanmu ba.—Zabura 100:3; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

  • Allah yana da dalilin da ya sa ya halicci kowane abu, har da mu ma.—Ishaya 45:18.

  • Allah ya halicce mu da “bukatar kulla dangantaka da” shi. (Matta 5:3, fassarar New World Translation) Yana so mu biya wa kanmu wannan bukatar.—Zabura 145:16.

  • Za mu iya biya wa kanmu wannan bukatar ta wajen kulla abokantaka da Allah. Wasu suna iya ganin kamar ba zai taba yiwuwa mu zama abokan Allah ba, amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.”—Yakub 4:8; 2:23.

  • Kafin mu zama abokan Allah, wajibi ne mu yi rayuwar da ta jitu da nufinsa. Littafi Mai Tsarki ya bayyana wannan nufin a Mai-Wa’azi 12:13 cewa: “Ka ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kadai ne wajibin mutum.”

  • A nan gaba, za mu ga ainihi yadda Allah ya so rayuwarmu ta kasance. A lokacin, Allah zai kawar da wahala kuma ya ba da rai madawwami ga abokansa, wato wadanda suka bauta masa.—Zabura 37:10, 11.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba