Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 26
  • Shin Allah Zai Taimake Ni Idan Na Yi Addu’a?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin Allah Zai Taimake Ni Idan Na Yi Addu’a?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da
  • Jehobah Yana Saurarar Mu Kuwa?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Allah Yana Jin Addu’o’inmu Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Jawowa Kurkusa da Allah Cikin Addu’a
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 26

Shin Allah Zai Taimake Ni Idan Na Yi Addu’a?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

E, Allah yana taimakon wadanda suke rokon shi da gaske kuma bisa nufinsa. Ko da ba ka taba yin addu’a ba, za ka sami karfafa daga misalai na wadanda suka yi addu’a cewa, “Allah ka taimake ni” da ke Littafi Mai Tsarki. Ga wasu misalai:

  • “Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; Ka cece ni bisa ga jinƙanka.”—Zabura 109:26.

  • “Ni matalauci ne, mai-talauci; Duk da haka Ubangiji ... kai ne taimakona.”—Zabura 40:17.

Babu shakka, marubucin wadannan kalmomi ya yi imani da Allah sosai. Duk da haka, Allah yana sauraron duk wadanda suka yi addu’a da kyakkyawar aniya, kamar “masu karyayyar zuciya” ko kuma wadanda suke da “ruhu mai-tuba.”—Zabura 34:18.

Kada ka ji tsoro cewa Allah yana da nisa kuma cewa bai damu da matsalolinka ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ko da shi ke Ubangiji madaukaki ne, ya kan lura da masu tawali’u: Amma masu-girman kai daga nesa ya fishe su.” (Zabura 138:6) Hakika, Yesu ya taba gaya wa almajiransa: “Har da gasussuwan kanku dukansu an kididdige su.” (Matta 10:30) Allah yana ganin abubuwa da yawa game kai da ba ka sani ba. Saboda haka, zai saurare ka sosai idan ka yi masa addu’a ya taimake ka ka jure matsalolinka!—1 Bitrus 5:7.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba