20-26 GA YULI, 2026
WAƘA TA 133 Mu Bauta wa Jehobah da Kuruciyarmu
Ka Tsai da Shawara Mai Kyau Game da Samun Ƙarin Ilimi
“Mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.”—K. MAG. 14:15.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abubuwa masu muhimmanci da muke bukatar mu yi tunani a kai saꞌad da muke so mu yanke shawara game da samun ƙarin ilimin, da kuma wasu ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau.
1-2. (a) Wace shawara ce matasa suke bukata su yanke? (b) Mene ne ake nufi da furucin nan “ƙarin ilimi”? (Ka duba “Maꞌanar Wasu Kalmomi.”)
“WANE irin aiki ne za ka so ka yi idan ka yi girma?” Idan kai matashi ne, babu shakka an sha yi maka irin tambayar nan. Gaskiyar ita ce, abin da zai fi amfanar ka shi ne yin hidima ta cikkaken lokaci. Duk da haka, kana bukatar ka samu kuɗin biyan bukatunka. (2 Tas. 3:10) Mai yiwuwa ka riga ka zaɓi irin aikin da za ka yi idan ka yi girma.
2 Don su iya samun aikin da suke so, wasu matasa sukan tattauna da iyayensu kuma su yanke shawara cewa za su samu ƙarin ilimin bayan sun gama makarantar sakandare.a Mai yiwuwa, kai ma ka taɓa tunanin ko kana bukatar samun ƙarin ilimi. Idan haka ne, a ina ne za ka iya yin hakan? A wannan talifin, za mu tattauna ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka ka yanke shawarwarin da suka dace game da yawan karatun da za ka yi. Ko da yake an shirya wannan talifin don matasa ne, shawarwarin da ke ciki za su taimaka wa dukan waɗanda suke so su samu ƙarin ilimin. Shawarwarin kuma za su taimaka wa iyaye su iya taimaka wa yaransu su san abin da ya dace su yi.
SHIN KANA BUKATAR ƘARIN ILIMIN?
3. Me ya sa wasu ꞌyanꞌuwa suke so su samu ƙarin ilimin?
3 A wasu wurare, idan mutum ya gama makarantar sakandare kawai, zai iya samun aiki. Amma a wasu wurare kuma, in ba ka samu ƙarin ilimi ba, ba za ka iya samun aikin da za a biya ka wani abin kirki ba. Samun ƙarin ilimi zai iya ba wa Krista lokacin yin waꞌazi ko kuma yin wasu ayyukan ibada. Amma neman ƙarin ilimin yakan ci lokaci da kuɗi, kuma yakan jawo wasu matsaloli.
4. Waye ne yake da hakkin yanke shawara a kan yawan karatun da mutum zai yi? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
4 Littafi Mai Tsarki ya ce, kowane mutum ne zai ɗauki hakkin shawarar da ya yanke. (Gal. 6:5) Saboda haka, kowane mutum ne zai yanke shawara ko zai samu ƙarin ilimin ko aꞌa.b Iyaye kuma suna da hakkin yanke shawara a kan yawan karatun da yaransu za su yi. (Afis. 6:1) Za su kuma iya taimaka wa yaransu su iya yanke shawarwari masu kyau game da yawan karatun da za su yi idan suka yi girma.—K. Mag. 22:6.
5. A wane lokaci ne zai dace mutum ya yanke shawara ko zai samu ƙarin ilimin, kuma me ya sa? (Ka kuma duba hoton.)
5 Matasa suna bukatar su yanke shawara ko za su samu ƙarin ilimi kafin su gama makarantar sakandare. Zai dace su tattauna da iyayensu game da wannan batun kafin su yanke shawara. Hakan zai ba wa su da iyayensu damar yin bincike don su san shawarar da za su yanke. Hakan kuma zai taimaka musu su zaɓi fannin karatu ko wata sanaꞌa da za ta taimaka musu idan sun yanke shawarar samun ƙarin ilimi ko kuma aikin da za su yi a nan gaba. Shin, dole ne iyaye da yaransu su yanke wannan shawarar kafin yaransu su gama makarantar sakandare? Ba lallai ba. (K. Mag. 21:5) Wasu matasa sun yanke shawara cewa, idan suka gama makarantar sakandare za su nemi aiki, su soma hidimar majagaba, kafin su yanke shawara ko za su samu ƙarin ilimin. Mutum zai iya yanke shawarar samun ƙarin ilimi daga baya a rayuwarsa.
Iyaye suna da hakkin taimaka wa yaransu su yanke shawarwarin da suka dace game da samun ƙarin ilimi (Ka duba sakin layi na 5)
6. Me zai taimaka wa mutum ya yanke shawarar da ta dace a batun samun ƙarin ilimi?
6 Me zai taimake ka ka yanke shawarar da ta dace a batun samun ƙarin ilimi? Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yanke shawarar da ta dace. (Yak. 1:5) Ban da haka, zai dace ka yi tunani game da abubuwa biyun nan. Na ɗaya, ka tambayi kanka, me ya sa nake so in samu ƙarin ilimin? (Zab. 26:2) Na biyu, ka bincika illoli da amfanin da za ka samu idan ka je samun ƙarin ilimi. (K. Mag. 14:15) Bari mu tattauna batutuwa biyun nan ɗaya bayan ɗaya.
ME YA SA KAKE SO KA SAMU ƘARIN ILIMI?
7. Me ya kamata mu tambayi kanmu idan muna so mu samu ƙarin ilimi?
7 Idan kana so ka samu ƙarin ilimi, yana da muhimmanci sosai ka tambayi kanka, ‘Me ya sa nake so in samu ƙarin ilimin?’ Mutane da yawa suna zuwa samun ƙarin ilimi don su iya samun irin aikin da suke so, ko kuma don su iya samun aikin da za a biya su kuɗin kirki. Yin hakan ba laifi ba ne. (1 Tim. 5:8) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi hankali da yawan son kuɗi, kuma kada mu soma dogara ga kuɗi maimakon Jehobah. (K. Mag. 23:4, 5; 1 Tim. 6:8-10; 1 Yoh. 2:17) Idan burinka shi ne ka yi kuɗi ko kuma ka burge mutane, ba za ka yi farin ciki na ƙwarai ba, za ka iya ma daina bauta wa Jehobah.
8-9. (a) Wane raꞌayi ne ya kamata mu kasance da shi game da samun ƙarin ilimi? (Matiyu 6:33) (b) Mene ne ka koya daga labarin Josefina, da Morine, da kuma Iris?
8 Wane raꞌayi ne ya kamata mu kasance da shi game da samun ƙarin ilimi? Babu abin da ya kai bauta wa Jehobah muhimmanci a rayuwarmu. (Mat. 22:37, 38; Filib. 3:8) Saboda haka, idan za ka so ka samu ƙarin ilimi ya kamata ya zama don ka iya samun abin da zai taimaka maka ka iya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka.—Karanta Matiyu 6:33.
9 Bari mu ga abin da ya taimaka ma wasu Kristoci su kasance da raꞌayin da ya dace game da samun ƙarin ilimi. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Josefina daga ƙasar Chile ta ce: “Na nemi samun ƙarin ilimi don in samu aikin da zai ba ni damar bauta wa Jehobah sosai. A rayuwata, bauta wa Jehobah ne ya fi muhimmanci ba samun ƙarin ilimin ba.” Wata ꞌyarꞌuwa kuma mai suna Morine ta zaɓi ta koyi yin kitso na tsawon shekara ɗaya. Me ya sa? Ta ce: “Burina shi ne yin hidima a inda ake bukatar masu shela. Saboda haka, na nemi sanaꞌar da za ta taimaka mini in cim ma burina. Bayan na koyi sanaꞌar, na ɗan yi aiki don in tara kuɗin yin tafiyar. Ƙari ga haka, sanaꞌar kuma ta taimaka mini in samu aiki a wurin da na je yin hidima.” Wata ꞌyarꞌuwa kuma mai suna Iris da samun ƙarin iliminta ya ɗan ci lokaci don a ɓangaren gyaran haƙora ne ta ce: “Samun ƙarin ilimi zai iya taimakon ka, amma ba zai iya sa ka samu ainihin farin ciki da gamsuwa ba. In kana so ka yi farin ciki, to ka tabbata cewa ka riƙe Jehobah sosai. Idan har duk abin da kake yi don Jehobah ne, to an gama.” Gaskiyar ita ce, idan dangantakarmu da Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu, zaɓin da za mu riƙa yi za su sa mu yi farin ciki na ƙwarai.
KA BINCIKA ILLOLI DA AMFANIN DA ZA KA SAMU
10. Ta yaya abin da ke Maimaitawar Shariꞌa 32:29 zai taimaka maka ka yanke shawara ko za ka samu ƙarin ilimi ko aꞌa?
10 Mai yiwuwa kana da wani fannin karatu da kake so ka yi, ko kuma wata sanaꞌa da kake so ka koya. Hakan yana da kyau. Amma zai dace ka yi tunani ko akwai wasu dabam da za ka iya zaɓa. (Ka duba Karin Magana 18:17.) A yau, akwai hanyoyin samun ƙarin ilimi da babu su a dā. Alal misali, mutum zai iya samun ƙarin ilimi daga gidansa ta intane. Ban da haka, zai dace ka yi tunani ko za ka iya biyan bukatunka ba tare da ka nemi ƙarin ilimi ba. Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Johanna daga Finland da ba ta nemi ƙarin ilimi ba ta ce: “Da na gama makarantar sakandare sai na soma yin aiki na ꞌyan kwanaki a mako, kuma ina hidimar majagaba. Yanzu na yi ayyuka dabam-dabam, kuma kullum Jehobah yana biyan bukatuna kamar yadda ya yi mana alkawari.” Ka tuna cewa, duk shawarar da ka yanke game da samun ƙarin ilimi da kuma irin ƙarin ilimin da kake so ka samu, yana da illolinsa da kuma amfaninsa. Saboda haka, ka tambayi kanka: ‘Amfanin da zan samu ya fi sadaukarwar da zan yi?’ (Karanta Maimaitawar Shariꞌa 32:29; 1 Kor. 10:23) Bari mu ga wasu abubuwan da za su taimaka maka ka iya amsa tambayar nan.
11. Me ya sa zai dace mutum ya yi tunani a kan lokacin da zai kashe kowane mako wajen samu ƙarin ilimi ko kuma koyan wata sanaꞌa? (Ka kuma duba hotunan.)
11 Lokacin da zai ci kowane mako. Ka yi tunani a kan lokacin da za ka kashe kowane mako kana zuwa aji, ko koyan sanaꞌar, da kuma yin ayyukan da ake ba wa ɗalibi a makaranta ya yi a gida. Shin, za ka samu lokacin yin ayyukan ibada da kuma cika hakkinka a iyali kuwa? (Filib. 1:10) Shin, samun ƙarin ilimin nan zai gajiyar da kai sosai har ka kasa yin shiri don taro da kuma yin nazari na kanka? Abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna Jeroz daga Indiya ke nan. Ya ce: “Fita waꞌazi ya yi min wuya sosai, kuma ba na iya mai da hankali a taro. A wasu lokuta, ba na ma halartan taro kwata-kwata. A yanzu ina da na sani domin karatun ya ci lokacina sosai kuma na sha wuya.” Amma, akwai fannin karatun da ba sa cin lokaci da yawa, ba a bukatar mutum ya riƙa zuwa kowace rana, kuma ba su da aikin da ɗalibi zai riƙa yin a gida da yawa. Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Rabeca daga Mozambik da ta ji daɗin zaɓin karatun da ta yi ta ce: “Awa biyu ne kawai ake koyar da mu kowace rana. Hakan ya ba ni dama in ci-gaba da yin hidimar majagaba na kullum.”
Idan kana son ka samu ƙarin ilimi, ka tabbata cewa za ka samu lokacin yin abubuwa masu muhimmanci da kake bukatar ka yi (Ka duba sakin layi na 11)
12. Wace tambaya ce zai dace ka yi wa kanka don ka iya yin amfani da lokacinka da kyau? (Mai-Waꞌazi 12:1)
12 Watanni ko shekaru nawa ne zai ɗauka? Wani abu kuma da zai dace ka yi tunani a kai shi ne watanni ko shekaru nawa ne samun ilimin zai ɗauka. Shin, samun ilimin zai nuna cewa kana amfani da lokacinka a hanyar da ta dace? (Afis. 5:15-17) Idan kai matashi ne, shin samun ƙarin ilimin zai ba ka damar yin iya ƙoƙarinka a bautar Jehobah ko yin hidima ta cikkaken lokaci yanzun da kake matashi? (Karanta Mai-Waꞌazi 12:1.) Shin, akwai wasu hanyoyin koyan sanaꞌar da kake so ba tare da ɓata lokaci da yawa ba? Alal misali, wasu makarantu da wuraren koyan sanaꞌa za su koyar da kai a cikin ƙanƙanin lokaci, kuma ba ka bukatar ka kashe kuɗi da yawa kamar yadda ake yi a jamiꞌa. Wani ɗanꞌuwa mai suna Mario daga ƙasar Chile ya ce: “Na halarci makarantar koyan sanaꞌa na shekara biyu, kuma kuɗin makarantar bai kai wanda ake biya a jamiꞌa ba. Ana koyar da mu sau huɗu kawai a mako. Hakan ya sa na ci-gaba da yin hidimar majagaba yayin da nake makarantar.”
13. Ta yaya wurin da mutum yake zama saꞌad da yake samun ƙarin ilimi zai iya shafan sa?
13 Wurin da za ka je ka samu ƙarin ilimin. Za ka iya samun ƙarin ilimi a wani wuri da ke kusa da inda kake zama. Amma a wasu lokuta, wurin da kake so ka samu ƙarin ilimin zai iya zama a wani gari, ko kuma kana bukatar ka koma zama a makarantar. A irin yanayoyin nan zai dace ka sani cewa barin gida zai iya sa dangantakarka da Jehobah da kuma iyalinka ta yi tsami musamman idan za ka koma zama da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. (K. Mag. 22:3; 1 Kor. 15:33) Wani ɗanꞌuwa mai suna Matias daga Mozambik ya je wani wuri da kuɗin makarantar bai da tsada don samun ƙarin ilimi na shekara ɗaya. Amma ya yi da na sanin yin hakan. Me ya sa? Ya ce: “Na yi shekara ɗaya ina zama a makarantar. Kowace rana, ina fama da jarabar yin abin da bai dace ba. Shawarata ita ce, duk wanda yake son ya samu ƙarin ilimi, kada ya yi hakan a wuri da ke da nisa da iyalinsa.” Wata ꞌyarꞌuwa kuma daga ƙasar Rasha ta ce: “Da yake ina zama da iyaye na a lokacin da nake samun ƙarin ilimi, hakan ya sa na iya guje wa matsaloli da jarabobi.” Bugu da ƙari, mutum zai iya samun ƙarin ilimi ta intane.
14. Ta yaya ƙaꞌidar da ke Luka 14:28 za ta taimaka maka ka yanke shawara mai kyau?
14 Kuɗin da za ka kashe. Wasu fannin karatu ba su da tsada, wasu kuma gwamnati tana iya biya wa mutum. A irin yanayoyin nan, mutum zai iya yin karatu ko ya koyi wata sanaꞌa da za ta taimaka masa ya samu aikin da yake so ba tare da kashe kuɗi da yawa ba. Amma a wasu wurare kuma, samun ƙarin ilimi na da tsada sosai. Ban da ainihin kuɗin da za ka kashe wajen samun ƙarin ilimin, za ka bukaci ka samu malamin da zai riƙa koyar da kai a gida don ka samu karɓuwa a makarantar. Wasu ƙarin ilimin za su iya ƙure aljihun mutum har su jefa shi cikin bashi na shekaru da yawa. Wani ɗanꞌuwa mai suna Adilson daga Mozambik, ya yi da na sanin irin karatun da ya yi. Ya ce: “Na yi girma a wurin kakannina. A wasu lokuta ba sa iya sayan abinci ko wasu abubuwan da suke so don su iya biya mini kuɗin makaranta, kuma sun yi shekara huɗu suna hakan.” Yayin da kake son ka samu ƙarin ilimi ko kuma koyan wata sanaꞌa, ka tambayi kanka: ‘Nawa ne zan kashe? Zai yi wa ni ko iyalina sauƙi mu biya wannan kuɗin?’ ‘Akwai wani fannin karatu ko sanaꞌar da zan iya koya da bai da tsada sosai?’ (Karanta Luka 14:28.) ‘Idan na karɓi bashi, tsawon wane lokaci ne zai ɗauke ni in biya? Aikin da zan samu a nan gaba zai iya biyan bukatuna kuma ya taimaka mini in iya biyan wannan bashin?’—K. Mag. 22:7.
15. Me ya sa zai dace ka yi ƙoƙari ka san irin aikin da ake samuwa a inda kake kafin ka yanke shawarar koyan wata sanaꞌa ko kuma irin karatun da za ka yi?
15 Ka yi tunani a kan irin ayyukan da ake samuwa a wurin da kake, ko a wurin da kake so ka ƙaura. Shin, ƙarin ilimin nan zai taimaka maka ka samu aiki kuwa? A wasu ɓangarorin karatu, akan mai da hankali a kan karatu ne kawai ko kuma koyar da raꞌayoyi dabam-dabam maimakon koya wa mutum takamaiman abin da zai taimaka masa ya samu aiki. (Kol. 2:8) Wata ꞌyarꞌuwa daga Indiya ta ce: “Karatun da na yi bai taimaka mini in kasance da ƙwarewar da ake bukata maꞌaikaci ya kasance da su ba. Hakan ya sa na gagara samun aiki a fannin karatun da na yi.” A wasu ɓangarorin karatu kuma, akan koya wa mutum ainihin abin da aikin ya ƙunsa da kyau, amma ba a yawan samun irin aikin. Wani ɗanꞌuwa mai suna Sublime daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya koyi yadda ake gyaran iyakwandishan, wato AC. Amma ya ce: “A wurinmu yawancin mutane suna gyaran abubuwa da kansu. Saboda haka, samun aiki ya yi mini wuya sosai.”
16. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka maka ka san irin aikin da za ka yi bayan ka samu ƙarin ilimi?
16 Wasu abubuwa kuma da za ka iya yin tunani a kai su ne: bayan ka gama samun ƙarin ilimin, za ka ji daɗin aikin da za ka samu kuwa? (M. Wa. 3:12, 13) Yaya wurin aikin zai kasance, kuma da wane irin mutane ne za ka riƙa yin aiki? Aiki ne da ke tattare da haɗarurruka da yawa? Za ka bukaci ka yi aiki da mutane ko kamfanin da suke so su zama a kan gaba a kowane lokaci? Aikin yana gajiyar da mutum sosai? Nawa ne ake biya a irin aikin? Kuɗin da za ka samu zai iya biyan bukatunka kuwa? Za ka bukaci ka riƙa samun ƙarin ilimi a kai a kai don ka ci-gaba da yin aikin? Mafi muhimmanci ma, aikin zai ba ka damar sa Mulkin Allah farko a rayuwarka? (M. Wa. 12:13) Gaskiyar ita ce, idan ana ƙarancin aiki, mutum yakan yi ƙoƙarin damƙe duk wanda ya samu. Amma irin ƙarin ilimin da ka zaɓa zai iya shafan irin aikin da za ka samu a nan gaba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tabitha daga Indiya ta zaɓi ta koyi yin ɗinki na wata shida. Ta ce: “Abin da ya sa na zaɓi wannan aikin shi ne don zai ba ni damar yin hidimar majagaba. Aiki ne da ake bukatarsa a kowane lokaci. Zan iya yin aikin a duk lokacin da na ga dama kuma ba na bukatar jari da yawa don in soma yin aikin.” Wannan aikin ya taimaka wa Tabitha ta ci-gaba da yin hidimar majagaba.
17. (a) Waɗanne abubuwa ne Krista yake bukatar ya yi da za su taimaka masa ya yanke shawarar da ta dace a batun samun ƙarin ilimi? (b) Waɗanne ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka yanke shawarar da ta dace? (Ka duba akwatin nan “Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da Za Su Taimaka.”)
17 A wannan talifin, mun tattauna abubuwa masu muhimmanci da ya kamata mutum ya yi tunani a kai game da samun ƙarin ilimi. To, waɗanne abubuwa ne Krista yake bukatar ya yi don ya iya yanke shawarar da ta dace? Idan kana so ka samu ƙarin ilimi a wani fanni, ka yi bincike ta wurin zuwa makarantar ko kuma ka shiga dandalin intane na makarantar. Ka yi ƙoƙari ka san ko ana samun aiki sosai a fannin da kake so ka karanta. Za ka kuma iya tambayar mutanen da suka sauke karatu a wannan fannin, ko kuma waɗanda suke yin irin aikin da kake so ka yi. (K. Mag. 13:10) Za ka iya tambayar su amfani da kuma illolin karatu ko kuma aikin da kake so ka yi. Ƙari ga haka, za ka iya neman raꞌayin ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka manyanta, kuma suna jin daɗin bauta wa Jehobah. (K. Mag. 15:22) Za ka iya ce su gaya maka irin ƙarin ilimin da suke ganin zai dace mutum ya samu, da kuma irin aikin da zai nema. Mai yiwuwa za su iya ambata wani irin aikin da ba ka taɓa yin tunaninsa ba.
18. Me ya kamata mu tuna?
18 Kamar yadda muka gani, samun ƙarin ilimi yana da amfaninsa da kuma illolinsa. Saboda haka, ka yi adduꞌa kafin ka yanke wata shawara. Ka tuna cewa samun ƙarin ilimi zai iya sa ka samu kuɗin biyan bukatunka, amma kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah shi ne kawai zai sa ka yi farin ciki na gaske. (Zab. 16:9, 11) Jehobah zai ci-gaba da kula da bayinsa ko da sun samu ƙarin ilimi ko aꞌa. (Ibran. 13:5) Amma, idan mutum ya yanke shawarar samun ƙarin ilimi kuma fa? Mene ne zai taimaka masa ya ci-gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah? Abin da za mu tattauna ke nan a talifi na gaba.
WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai
a MAꞌANAR WASU KALMOMI: A wannan talifin da kuma na gaba, furucin nan “ƙarin ilimi” yana nufin duk wani tsarin karatu ko koyo da mutum yakan yi bayan ya gama makarantar sakandare. Hakan ya haɗa da ƙarin ilimin da ake samuwa a jamiꞌa, ko kwaleji, ko makarantar koyan sanaꞌa ko kuma wasu wuraren koyan sanaꞌa.
b Littattafanmu a dā sun ce ba zai dace Krista ya nemi samun wasu irin ƙarin ilimin boko ba. Alal misali, talifin nan mai jigo “Iyaye, Wace Irin Rayuwa Ce Kuke Son Yaranku Su Yi A Nan Gaba?” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2005, ya ambata wasu haɗarurruka da mutum zai iya shiga idan ya halarci jamiꞌa. Duk da cewa haɗarurrukan nan suna nan har wa yau, kowane mutum ne yake da hakkin yanke shawara ko zai samu irin ƙarin ilimin nan ko aꞌa. Iyaye suna da hakkin yanke shawarar nan idan suna da yaran da ke ƙarƙashinsu. Kowane Krista yana bukatar ya yi adduꞌa, ya bincika ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, kuma ya yi ƙoƙari ya san irin sadaukarwar da zai yi wajen samun ƙarin ilimin kafin ya yanke shawara. Kada kowa, har da dattawa ma su shariꞌanta mutum a kan shawarar da ya yanke game da wannan batun.—Yak. 4:12.