Ta Yaya ‘Za Ka Sa Hanyarka ta Yi Nasara’?
“NASARA” kalma ce da take jan hankali! Wasu mutane sun samu matsayi mai girma kuma sun yi nasara sosai wajen samun arziki da kuma yi wa kansu suna. Wasu mutane sun yi mafarkin yin nasara amma hakan bai faru ba.
Hakika, yin nasara ya dangana ne ga abin da ka mai da wa hankali a rayuwarka. Abubuwa biyu masu muhimmanci su ne yadda ka yi amfani da lokacinka da kuzarinka da kuma ko za ka yanki shawarar yin hakan.
Kiristoci da yawa sun ga cewa shagalawa a hidima ya sa sun samu gamsuwa sosai. Yin hidima ta cikakken lokaci ya taimaki matasa da manya su yi nasara. Duk da haka, wasu za su ji cewa hidima tana cin rai kuma ba za su saka ta farko a rayuwarsu ba yayin da suke biɗan wasu maƙasudai. Mene ne zai iya sa hakan ya faru? Mene ne ya kamata ka yi don ka guji yin watsi da abin da ya fi muhimmanci da gaske? Kuma ta yaya ‘za ka sa hanyarka ta yi nasara’?—Josh. 1:8.
Ayyuka da Ake Yi Bayan An Tashi daga Makaranta da Kuma Wasanni
Matasa Kiristoci suna bukatar su kasance da daidaita tsakanin zuwa makaranta da kuma bauta wa Allah na gaskiya. Waɗanda suke yin hakan za su yi nasara a rayuwa kuma sun cancanci a yaba musu sosai.
Amma wasu matasa Kiristoci suna shagalawa sosai a ayyuka da ake yi idan aka tashi daga makaranta da kuma wasanni. Yin irin waɗannan ayyukan ba laifi ba ne. Amma, ya kamata matasa Kiristoci su tambayi kansu: ‘Sa’o’i nawa ne zan bukaci yin amfani da su don yin hakan? Cuɗanya kuma fa? Waɗanne irin mutane ne nake tarayya da su sa’ad da nake yin waɗannan ayyukan? Kuma mene ne zan mai da wa hankali a rayuwa?’ Mai yiwuwa ka fahimci cewa mutum yana iya shaƙu a irin waɗannan ayyuka har ba zai samu isashen lokaci ko kuma kuzari na ci gaba da dangantaka da Allah ba. Shi ya sa, yake da kyau a kafa abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwa.—Afis. 5:15-17.
Ka yi la’akari da labarin Wiktor.a Ya ce: “Sa’ad da nake ɗan shekara 12, na shiga kulob ɗin wasan kwallon raga. Da shigewar lokaci, na ci gasa masu yawa kuma na samu lada. Na samu zarafin zama fitaccen ɗan wasa.” Amma, Wiktor ya damu game da yadda yin wasan yake shafan ruhaniyarsa. Wata rana, barci ya kwashe shi sa’ad da yake ƙoƙarin karanta Littafi Mai Tsarki. Sai kuma ya fahimci cewa ba ya farin ciki sosai idan ya fita hidimar fage. “Wasan yana sa ba ni da ƙarfi, kuma ba da daɗewa ba na fahimci cewa yana hana ni kasancewa da ƙwazo a ruhaniya. Na san cewa ba na iya ƙoƙari na.”
Makaranta Gaba da Sakandare
Kirista yana da hakki na Nassi ya kula da iyalinsa, kuma wannan ya haɗa da tanadar da bukatu na zahiri. (1 Tim. 5:8) Har ila, shin hakan yana bukatar zuwa wata kwaleji ko kuma samun digiri a jami’a?
Zai zama da kyau a yi la’akari da yadda neman ƙarin ilimi zai iya shafan dangantakar mutum da Jehobah. Bari mu bayyana wannan ta wurin yin la’akari da wani misali na Nassi.
Baruch sakataren annabi Irmiya ne. A wani lokaci, Baruch ya zama mai dogon buri, maimakon ya mai da hankali ga gatan da yake da shi a hidimarsa ga Jehobah. Jehobah ya lura da hakan kuma ta wurin Irmiya ya gargaɗar da shi: “Kana fa biɗa wa kanka manyan abu? kada ka biɗe su.”—Irm. 45:5.
Waɗanne ‘manyan abubuwa’ ne Baruch ya ci gaba da biɗansu? Wataƙila ya so ya yi wa kansa suna a zamanin Yahudawa. Ko kuma manyan abubuwan da ya biɗa su ne abubuwan mallaka. Ko yaya dai, bai saka abubuwa masu muhimmanci da farko a rayuwarsa ba, wato, abubuwa da za su sa ya ci gaba da kasancewa kusa da Jehobah. (Filib. 1:10) Har ila, Baruch ya saurari gargaɗin Jehobah ta wurin Irmiya da hakan aka ceci ransa.—Irm. 43:6.
Me za mu iya koya daga wannan labarin? Gargaɗin da aka yi wa Baruch ya nuna cewa akwai abin da bai yi daidai ba. Ya nemi wa kansa manyan abubuwa. Idan kana da abin biyan bukata, shin kana bukatar ka ɓata lokaci da kuɗi da kuma ƙoƙari wajen samun ƙarin ilimi don ka cim ma burinka ko kuma na iyayenka ko na wasu dangogi?
Ka yi la’akari da Grzegorz, mai tsara ayyukan kwamfuta. Da abokan aikinsa suka rinjaye shi, sai ya soma ƙarin ilimi na musamman. Ba da daɗewa ba, ba shi da lokacin biɗan abubuwa na ruhaniya. Ya tuna: “A koyaushe ina ji na taƙure sosai. Lamiri na ya dame ne domin ban cim ma maƙasudai na ruhaniya da na kafa wa kaina ba.”
Shagalawa a Aiki
Kalmar Allah ta ƙarfafa Kiristoci na gaskiya su zama masu aiki tuƙuru kuma su zama shugabannin aiki masu kyau da kuma ma’aikata masu kan gado. Manzo Bulus ya rubuta: “Iyakar abin da ku ke yi, ku aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji, ba ga mutane ba.” (Kol. 3:22, 23) Amma, ko da yake aiki tuƙuru yana da kyau, muna bukatar mu kasance da dangantaka mai kyau da Mahaliccinmu. (M. Wa. 12:13) Idan Kirista ya shagala a aikinsa, zai iya kasancewa da sauƙi ya ƙi saka biɗe-biɗe na ruhaniya farko a rayuwarsa.
Shagalawa a aikinsa zai iya sa Kirista ya ji ya gaji ainun ya ci gaba da kula da ruhaniyarsa kuma ya taimaka wa iyalinsa. Sarki Sulemanu ya lura cewa “hannu biyu cike, tare da wahala” sau da yawa “cin iska kawai” ne. Idan Kirista ya fi shagalawa a aikinsa, a ƙarshe zai iya samun matsi na dogon lokaci. Irin wannan mutum zai iya zama bawa ga aikinsa har ya soma ciwo. Idan haka ne, shin zai iya “yi murna, . . . shi ji daɗi cikin dukan aikinsa”? (M. Wa. 3:12, 13; 4:6) Mafi muhimmanci, shin zai iya samun isashen ƙarfi na zahiri da na motsin rai don ya cika ayyukansa a cikin iyali kuma ya saka hannu cikin ayyuka na ruhaniya?
Janusz, wanda yake da zama a Gabashin Turai ya shagala a sana’arsa na aikin lambu. Ya tuna: “Mutanen duniya suna so na domin ina iya yin abu ba tare da neman taimakon kowa ba kuma ina iya kammala kowanne aikin da aka ba ni. Amma na soma sanyi a ruhaniya, kuma na daina fita hidimar fage. Ba da daɗewa ba na daina halartar taro. Na zama mai fahariya har ba na karɓan gargaɗi daga dattawa kuma na bijire daga ikilisiya.”
Za Ka Iya Yin Nasara a Rayuwa
Mun tattauna abubuwa uku da Kirista zai iya yi da za su sa shi sanyi a ruhaniya. Shin kana yin ɗaya cikin waɗannan ayyukan? Idan haka ne, tambayoyi na gaba da nassosi da kuma kalamai za su iya taimaka maka ka san ko kana kan hanyar samun nasara.
Makaranta da ayyuka da ake yi bayan an tashi daga makaranta: Yaya yawan yadda kake shaƙu a irin waɗannan ayyuka? Shin Waɗannan suna cin lokacin da ka keɓe a dā don ayyuka na ruhaniya? Shin ka lura cewa ba ka jin daɗin cuɗanya da ’yan’uwanka masu bi kuma? Idan haka ne, ka yi koyi da Sarki Dauda, wanda ya roƙi Jehobah: “Ka sa in san tafarkin da zan bi.”—Zab. 143:8.
Wani mai kula mai ziyara ya taimaki Wiktor, da aka ambata ɗazu. Mai kula mai ziyarar ya gaya masa: “Ka yi magana da alfahari game da sana’arka na wasan kwallon raga.” “Hakan ya taɓa ni sosai,” in ji Wiktor. “Sai na fahimci cewa na yi nisa sosai. Ba da daɗewa ba na daina tarayya da abokai na na duniya a kulob ɗin kuma na nemi abokai a cikin ikilisiya.” A yau, Wiktor yana bauta wa Jehobah da himma a cikin ikilisiyarsu. Ya ba da shawara: Ka tambayi abokanka da iyayenka, ko kuma dattawan ikilisiya ko sun lura cewa ayyukanka na makaranta suna sa ka kusaci Jehobah ko kuma suna nisanta ka daga wurinsa.”
Zai dace ka gaya wa dattawa da ke ikilisiyarku cewa za ka so ka biɗi ƙarin gata wajen bauta wa Allah. Shin za ka iya tallafa wa tsofaffi da suke bukatar cuɗanya ko taimako, wataƙila ka taimake su da yin sayayya ko kuma aikace-aikace a gidansu? Ko da mene ne shekarunka, kana iya saka hannu a hidima ta cikakken lokaci, kana gaya wa mutane dalilin da ya sa kake farin ciki.
Makarantar jami’a: Yesu ya yi kashedi game da ‘neman darajar kanka.’ (Yoh. 7:18) Ko da wace shawara ka tsai da game da yawan makaranta da za ka yi, shin ka “gwada mafifitan al’amura”?—Filib. 1:9, 10.
Grzegorz, mai tsara ayyukan kwamfuta da muka ambata ɗazun ya yi wasu gyare-gyare a rayuwarsa. Ya ce: “Da yake na saurari shawarar dattawa, sai na sauƙaƙa rayuwata. Kuma na fahimci cewa ba na bukatar ƙarin makaranta. Hakan zai cinye lokacin na da kuma kuzari na.” Grzegorz ya saka hannu sosai a ayyukan ikilisiya. Da shigewar lokaci, ya sauke karatu daga Makarantar Koyar da Masu Hidima da yanzu ake kira Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure. Hakika ya “rifta zarafi” don ya ƙara iliminsa game da Allah.—Afis. 5:16.
Aikin albashi: Shin ka shagala ainun a cikin aikinka har ka sa al’amura na ruhaniya a gefe ɗaya? Shin kana amfani da isashen lokaci don ka tattauna da iyalinka? Shin kana kyautata jawabanka a cikin ikilisiya? Kana taɗi mai ƙarfafa mutane kuwa? “Ka ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa” kuma za ka samu albarkar Jehobah kuma ‘ka ji wa ranka daɗi cikin aikinka.’—M. Wa. 2:24; 12:13.
Janusz, da aka ambata ɗazun, bai yi nasara ba a sana’arsa na aikin lambu; maimakon haka ya yi hasara. Da yake ba ya samun kuɗi kuma ya ci bashi, sai ya komo ga Jehobah. Janusz ya daidaita al’amuransa kuma yanzu yana hidima a matsayin majagaba na kullum da kuma dattijo a cikin ikilisiya. Ya ce: “Yayin da na gamsu da abubuwa masu muhimmanci, kuma na yi amfani da ƙarfi na don abubuwa na ruhaniya, sai na samu kwanciyar rai da kuma lumana.”—Filib. 4:6, 7.
Ka ɗauki lokaci don ka bincika muradinka da abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwarka. Bauta wa Jehobah ce za ta sa mutum ya samu nasara na dindindin. Ka sa wannan ya zama abin da ya fi muhimmanci a rayuwarka.
Wataƙila za ka bukaci ka yi wasu gyare-gyare har da kawar da abubuwa da ba su da muhimmanci domin ka tabbatar wa kanka “nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.” (Rom. 12:2) Amma ‘za ka iya yin nasara’ ta wajen bauta masa da dukan ranka.
[Hasiya]
a An canja wasu sunayen.
[Akwati/Hoto a shafi na 31]
Ta Yaya Za Ka Sa Hanyarka ta Yi Nasara?
Da yake akwai abubuwa da yawa da suke janye hankali, ta yaya za ka iya mai da hankali ga abubuwan da suke da muhimmanci sosai? Ka keɓe lokaci don ka bincika muradinka da abubuwan da suke fi maka muhimmanci ta yin tunani a kan waɗannan tambayoyin:
AYYUKA DA AKE YI BAYAN AN TASHI DAGA MAKARANTA DA KUMA WASANNI
▪ Waɗanne irin cuɗanya ne kake yi idan ka saka hannu a waɗannan ayyukan?
▪ Yawan wane lokaci ne yin hakan zai bukaci?
▪ Shin wannan zai zama abin da ya fi muhimmanci a rayuwarka?
▪ Shin wannan yana cin lokacin da kake amfani da shi don ayyuka na ruhaniya?
▪ Da waɗanne irin mutane ne zan riƙa abokantaka?
▪ Shin kana jin daɗin yin tarayya da su fiye da ’yan’uwanka masu bi?
ƘARIN ILIMI
▪ Idan kana da aikin da kake tallafa wa kanka da shi, shin kana bukatar yin amfani da lokaci da kuɗi da kuma kuzari don samun ƙarin ilimi?
▪ Shin sai ka samu ilimin kwaleji ko kuma digiri na jami’a don ka tallafa wa kanka?
▪ Yaya hakan zai shafi halartar tarurruka?
▪ Shin ka ‘tabbata da abubuwan da suka fi muhimmanci’?
▪ Shin kana bukatar ka ƙarfafa tabbacinka cewa Jehobah zai iya yi maka tanadi?
AIKI
▪ Shin zaɓin da ka yi yana ƙyale ka ka ji daɗin rayuwarka?
▪ Shin aikinka yana sa ka samu ƙarfi na zahiri da na motsin rai don ka cika hakkokinka a cikin iyali kuma ka saka hannu a ayyuka na ruhaniya?
▪ Kana samun isashen lokaci don ka tattauna da iyalinka?
▪ Shin ka shagala sosai a ayyuka har ka ajiye ayyuka na ruhaniya a gefe ɗaya?
▪ Shin hakan ya shafi jawabanka a cikin ikilisiya?
[Hoto a shafi na 30]
Jehobah ya yi wa Baruch gargaɗi game da dogon buri