Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Nuwamba p. 31
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Ce Zai Faru da Maƙiyan Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Kada Ku Ji Tsoron Dabbobin Nan Masu Ban Tsoro
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Jehobah Ya Bayyana Al’amura Da Lallai “Za Su Faru Ba Da Daɗewa Ba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Nuwamba p. 31

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Wane irin “tunani” ne Jehobah zai sa a zukatan gwamnatoci nan ba da daɗewa ba?

Ga abin da aka ce za a fara gani a lokacin ƙunci mai girma a Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​16, 17. Ayoyin sun ce: “Ƙahoni goma da ka gani, su da dabbar za su ƙi ganin wannan ƙaruwa. Za su ƙwace kome da take da shi su kuma bar ta tsirara, za su cinye naman jikinta, su kuma ƙone ta da wuta. Gama Allah ya nufe su su aikata nufinsa, su zama da tunani ɗaya, su ba wannan dabba ikonsu domin ta yi mulki.” A dā, an rubuta a littattafanmu cewa tunanin da Jehobah ya sa a zukatan gwamnatocin nan, na hallaka addinin ƙarya ne.

Amma ana bukatar gyara. ‘Tunanin’ da Jehobah zai sa a zukatan gwamnatocin shi ne su ba wa wata “dabba ikonsu domin ta yi mulki.” Don mu fahimci yadda hakan zai cika, bari mu tattauna waɗannan tambayoyin.

Su waye ne aka ambata a cikin annabcin? Na ɗaya ita ce “ƙaruwa” wadda ake kiran ta “Babila Babba.” Ita ce take waƙiltar daular addinin ƙarya. Na biyu ita ce “jar dabba.” Ita ce take waƙiltar Majalisar Ɗinkin Duniya. An kafa wannan ƙungiyar a shekara ta 1919 don ta kawo zaman lafiya a duniya. Kuma ita ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta dā. (R. Yar. 17:​3-5) Na uku kuma shi ne “ƙahoni goma.” Su ne suke waƙiltar dukan gwamnatocin da suke goyon bayan dabbar.

Wace irin dangantaka ce ke tsakanin ƙaruwar da jar dabbar? Ƙaruwar ta daɗe “tana zaune” a kan dabbar kuma hakan ya nuna cewa tana goyon bayan ta, kuma tana ƙoƙarin sa ta ta yi dukan abin da ta faɗa.

Mene ne zai faru da ƙaruwar? Ƙahoni goma da kuma dabbar da suke goyon bayan “ƙaruwar” za su ƙi jininta. Za su tsane ta sosai har su ƙwace kome da kome da take da shi, kuma su nuna wa kowa cewa ita muguwa ce. A ƙarshe, za su hallaka ta kuma shi ne abin da Jehobah ya ce zai faru da ita. (R. Yar. 17:1; 18:8) Hakan zai kawo ƙarshen addinan ƙarya. Amma kafin hakan ya faru, Jehobah zai sa gwamnatocin su yi wani abin da ba a taɓa gani ba.

Mene ne Jehobah zai sa gwamnatocin su yi? Zai sa su aikata “nufinsa.” Za su ba wa wannan jar dabbar “ikonsu” wato Majalisar Ɗinkin Duniya. (R. Yar. 17:13) Hakan yana nufin cewa ba da son ransu ne za su ba wa dabbar ikonsu ba. Annabcin ya nuna cewa Allah ne da kansa zai sa su yi hakan. (K. Mag. 21:1; ka kuma duba Isha. 44:28.) Hakan zai faru a hankali a hankali ne? Aꞌa! Hakan zai faru farat ɗaya ne. Wannan zai sa dabbar ta hallaka dukan addinan ƙarya.

Mene ne muke ganin zai faru nan ba da daɗewa ba? Kada mu ɗauka za mu ji cewa gwamnatoci sun soma ba wa Majalisar Ɗinkin Duniya goyon baya a sanu a hankali. Abin da zai faru shi ne: A lokaci guda, Jehobah zai sa dukan gwamnatocin duniya su ba wa Majalisar Ɗinkin Duniya ikonsu ɗari bisa ɗari. Idan hakan ya faru, za mu san cewa lokacin ƙunci mai girma ya yi kusa. Saboda haka, ya kamata “mu yi zaman tsaro da shiri,” domin za mu ga canje-canje nan ba da daɗewa ba.—1 Tas. 5:6.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba