Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Nuwamba pp. 16-21
  • Yesu Babban Firist Namu Ne Mai Tausayi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Babban Firist Namu Ne Mai Tausayi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YESU YA ZO DUNIYA
  • YESU YA TAUSAYA WA MUTANE
  • YADDA MUKE KOYI DA YESU A YAU
  • YESU ZAI IYA TAIMAKA MAKA
  • Mene ne Fansar Yesu Ta Nuna Mana?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Darussa Daga Kwanaki 40 na Ƙarshe da Yesu Ya Yi a Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Jehobah “Yakan Warkar da Masu Fid da Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Nuwamba pp. 16-21

TALIFIN NAZARI NA 46

WAƘA TA 17 “ Na Yarda”

Yesu Babban Firist Namu Ne Mai Tausayi

“ Gama Babban Firist nan namu ba wani ne wanda bai damu da kāsawarmu ba.”—IBRAN. 4:15.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga dalilin da ya sa za mu iya ce Yesu ne Babban Firist da ya fi dacewa da kuma hanyoyi dabam-dabam da yake taimaka mana a yau.

1-2. (a) Me ya sa Jehobah ya turo Ɗansa zuwa duniya? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin? (Ibraniyawa 5:​7-9)

WAJEN shekaru 2,000 da suka shige, Jehobah ya turo Ɗansa da yake ƙauna zuwa duniya. Me ya sa? Dalili ɗaya shi ne, domin ya ꞌyantar da mutane daga zunubi da mutuwa, kuma ya cire dukan wahalolin da Shaiɗan ya jawo. (Yoh. 3:16; 1 Yoh. 3:8) Jehobah ya san cewa idan Yesu ya zo duniya a matsayin mutum, hakan zai sa ya ƙara zama Babban Firist mai tausayi. Yesu ya zama Babban Firist ne bayan ya yi baftisma a shekara ta 29 bayan haifuwa Yesu.a

2 A wannan talifin, za mu ga yadda yin rayuwa a matsayin mutum ya taimaka wa Yesu ya ƙara zama Babban Firist mai tausayi sosai. Sanin hakan zai sa ya yi mana sauƙi mu yi adduꞌa kuma mu kusaci Jehobah musamman a lokacin da muke baƙin ciki don zunubi ko kuskuren da muka yi.—Karanta Ibraniyawa 5:​7-9.

YESU YA ZO DUNIYA

3-4. Mene ne Yesu ya sadaukar kafin ya zo duniya, kuma yaya rayuwarsa ta kasance a duniya?

3 Da yawa daga cikinmu mun yi wasu canje-canje a rayuwa. Alal misali, mai yiwuwa mun ƙaura daga inda muke, kuma mun bar danginmu da abokanmu. Irin waɗannan canje-canjen ba su da sauƙi. Amma babu wani a cikinmu da ya taɓa yin canje-canje a rayuwa kamar yadda Yesu ya yi. A sama, shi ne na farko kuma mafi ɗaukaka a cikin malaꞌiku. Jehobah yana ƙaunar sa sosai kuma yana farin ciki domin yana aiki tare da Ubansa. (Zab. 16:11; K. Mag. 8:30) Duk da haka, Filibiyawa 2:7 ta ce, “ya mai da kansa kamar ba kome ba,” ya sadaukar da kome da kome da yake da shi a sama don ya yi rayuwa da ꞌyanꞌadam ajizai a duniya.

4 Ka yi laꞌakari da yanayin da Yesu ya sami kansa saꞌad da aka haife shi a duniya. Iyayensa talakawa ne. Mun san hakan domin saꞌad da aka haife shi, iyayensa sun yi hadaya da ƙananan tsuntsaye biyu ne. (Fir. 12:8; Luk. 2:24) Saꞌad da mugun Sarki Hiridus ya ji cewa an haifi Yesu, ya yi ƙoƙarin kashe shi. Don su ceci ran yaron, iyayensa sun yi gudun hijira zuwa ƙasar Masar na ɗan lokaci. (Mat. 2:​13, 15) Rayuwar Yesu a duniya ta yi dabam sosai da yadda rayuwarsa take saꞌad da yake sama.

5. Mene ne Yesu ya gani saꞌad da yake duniya, kuma ta yaya hakan ya taimaka masa ya zama Babban Firist mai tausayi? (Ka kuma duba hoton.)

5 Yayin da Yesu yake duniya, ya ga yadda mutane suke shan wahala. Yesu ya san yadda mutum yake ji idan wani nashi ya rasu, kuma ba shakka ya ga yadda mutane da dama suka rasu har da babansa na duniya, wato Yusufu. Saꞌad da yake waꞌazi, Yesu ya haɗu da kutare, da makafi, da mutanen da wani bangaren jikin su ya shanye, da iyayen da yaransu suka rasu, kuma ya tausaya masu. (Mat. 9:​2, 6; 15:30; 20:34; Mar. 1:​40, 41; Luk. 7:13) Ko da yake, ya ga yadda mutane suke shan wahala a lokacin da yake sama, zuwa duniya ya taimaka masa ya ƙara fahimtar yadda mutane suke ji idan suna shan wahala. (Isha. 53:4) Ya ƙara fahimtar yadda mutane suke ji a yanayoyi dabam-dabam, da yadda suke fama don matsalolin da suke ciki. Shi da kansa ma ya yi fama da gajiya, da baƙin ciki, da kuma damuwa.

Mutane da yawa sun kewaye Yesu suna roƙon sa ya warkar da su. Ya tausaya wa wani mutum da ya tsufa kuma bai da lafiya, sai ya riƙe hannunsa.

Yesu ya tausaya wa mutane kuma ya damu da yadda suke shan wahala (Ka duba sakin layi na 5)


YESU YA TAUSAYA WA MUTANE

6. Mene ne muka koya daga annabcin da Ishaya ya yi game da yadda Yesu zai tausaya wa mutane? (Ishaya 42:3)

6 Saꞌad da Yesu yake waꞌazi a duniya, ya tausaya wa mutanen da ba su da lafiya, da waɗanda ake wulaƙantawa. Ta yin hakan, ya cika annabcin da Jehobah ya yi ta wurin annabi Ishaya. A wasu lokuta a Nassosin Ibrananci, akan kwatanta masu karfi da kuma arziki da lambu mai kyau da ke samun isasshen ruwa, ko bishiya mai tsayi da kuma ƙarfi. (Zab. 92:12; Isha. 61:3; Irm. 31:12) Amma akan kwatanta talakawa da waɗanda ake wulaƙantawa da karan da bai da ƙarfi, ko kuma fitilar da wutarta ta kusan mutuwa. (Karanta Ishaya 42:3; Mat. 12:20) Jehobah ya yi amfani da waɗannan kwatancin don ya bayyana irin ƙauna da kuma tausayin da Yesu zai nuna wa waɗanda ake wulaƙantawa.

7-8. Ta yaya Yesu ya cika annabcin da Ishaya ya yi?

7 Matiyu ya rubuta cewa Yesu ya cika annabcin da Ishaya ya yi. Ya ce: “Ba zai ƙarya karan da ya kusan karyewa ba, ba zai kashe fitilar da ta kusan mutuwa ba.” Yesu ya yi muꞌujizai da yawa da ya amfane waɗanda ake ganin cewa su ba kome ba ne, kamar karan da ya kusan karyewa da kuma waɗanda ba su da bege da suna nan kamar fitilar da ta kusan mutuwa. Alal misali, Yesu ya haɗu da wani mutum da ke da cutar kuturta mai tsanani sosai. Mai yiwuwa mutumin nan ya ga kamar ba zai taɓa warkewa ba, ko kuma ba zai taɓa kasancewa tare da iyalinsa da abokansa ba. (Luk. 5:​12, 13) Akwai wani mutum da shi kurma ne kuma ba ya iya magana. Ka yi laꞌakari da yadda mutumin nan zai ji yayin da yake ganin mutane suna magana da juna amma ba ya jin abin da suke faɗa. (Mar. 7:​32, 33) Amma ba shi ke nan ba.

8 A Lokacin da Yesu yake duniya, Yahudawa da yawa sun yi imani cewa idan mutum yana fama da rashin lafiya ko naƙasa, laifinsa ne ko na iyayensa. (Yoh. 9:2) A sakamakon haka, mutane suna yawan wulaƙanta su kuma hakan yana sa su baƙin ciki. Amma Yesu ya warkar da su kuma ya taimaka musu su san cewa Allah ya damu da su. Wane tabbaci ne hakan yake ba mu?

9. Ta yaya Ibraniyawa 4:​15, 16 suka nuna cewa Yesu yana tausaya wa ꞌyanꞌadam?

9 Karanta Ibraniyawa 4:​15, 16. Muna da tabbaci cewa Yesu zai riƙa tausaya mana. Me ya sa muka ce haka? Mutum mai tausayi yana damuwa sosai idan ya ga cewa wasu suna cikin matsala. Kalmar Girkanci da aka fassara zuwa “tausayi” tana nufin nuna damuwa kan abin da ya sami wani na rashin jin daɗi. (Ka kuma duba Ibraniyawa 10:34.) Idan muka karanta labaran da suka nuna yadda Yesu ya taimaka wa mutane a Littafi Mai Tsarki, za mu ga cewa ya tausaya masu sosai. Bai warkar da mutane kawai don yana ganin ya zama masa dole ba. Ya damu da su da gaske ne, kuma yana so ya taimaka musu. Alal misali, saꞌad da ya warkar da kuturun, ya taɓa shi. Yesu zai iya warkar da shi daga nesa, amma bai yi hakan ba. Kuma mai yiwuwa mutumin nan ya yi shekaru da yawa ba wanda ya taɓa shi! Ƙari ga haka, lokacin da Yesu zai warkar da kurman, ya kai shi gefe wurin da ba kowa kuma ba hayaniya. Kuma saꞌad da wani Bafarisi ya so ya wulaƙanta wata mata da ta tuba daga zunubanta, ta wanke ƙafafun Yesu da hawayenta, kuma ta share shi da gashin kanta, Yesu ya kāre ta. (Mat. 8:3; Mar. 7:33; Luk. 7:44) Yesu bai guji waɗanda suke rashin lafiya ko waɗanda suka yi zunubi masu tsanani ba. A maimakon haka, yana so su zo kusa da shi, kuma ya nuna masu cewa yana ƙaunar su. Muna da tabbaci cewa mu ma zai tausaya mana.

YADDA MUKE KOYI DA YESU A YAU

10. Waɗanne abubuwa ne za mu iya amfani da su don mu taimaka wa kurame da makafi? (Ka kuma duba hotunan.)

10 A matsayinmu na mabiyan Yesu masu aminci, muna iya ƙoƙarinmu mu yi koyi da shi, ta wajen ƙaunar mutane, da kuma tausaya musu. (1 Bit. 2:21; 3:8) Ko da yake ba mu da ikon warkar da makafi ko kurame, za mu iya taimaka musu su koyi abubuwa game da Jehobah kuma su kusaci shi. Alal misali, akwai littattafanmu a yarukan kurame fiye da 100. Kuma don a taimaka wa makafi da waɗanda ba sa gani sosai, an shirya littattafai na makafi a yaruka fiye da 60, kuma akwai bidiyoyi masu ƙarin bayani a yaruka fiye da 100. Abubuwan nan suna taimaka wa kurame da makafi su kusaci Jehobah da Ɗansa.

Hotuna: Na 1. ꞌYanꞌuwa suna waƙa a yaren kurame a taron ikilisiyar kurame. Na 2. Wata ꞌyarꞌuwa makauniya tana karatun Littafi Mai Tsarki na makafi.

Akwai littattafanmu a yaruka fiye da 1,000

Hagu: Yarukan kurame fiye da 100

Dama: Yarukan makafi fiye da 60

(Ka duba sakin layi na 10)


11. Ta yaya ƙungiyar Jehobah take nuna ta damu da dukan mutane kamar yadda Yesu ya yi? (Ayyukan Manzanni 2:​5-7, 33) (Ka kuma duba hotuna.)

11 Ƙungiyar Jehobah tana ƙoƙari wajen taimaka wa mutane daga wurare dabam-dabam su zo su bauta wa Jehobah. Ka tuna cewa bayan da Yesu ya tashi daga mutuwa, ya ba wa mabiyansa ruhu mai tsarki domin duk waɗanda suka halarci bikin Fentikos su ji waꞌazin labari mai daɗin nan a “yarensu.” (Karanta Ayyukan Manzanni 2:​5-7, 33.) A ƙarƙashin ja-gorancin Yesu, ƙungiyarmu ta tanadar da littattafai a yaruka fiye da 1,000. Wasu yarukan mutane kaɗan ne suke yin sa. Alal misali, mutane kaɗan ne suke yin wasu yaruka da ake yi a wasu wurare a Kudanci da kuma Arewancin Amurka. Duk da haka, an shirya littattafanmu a irin yarukan nan fiye da 160 don a tabbata cewa mutane da yawa sun ji waꞌazin labarin nan mai daɗi. Ƙari ga haka, akwai littattafanmu a yarukan Romany fiye da 20. Dubban mutane da suke irin waɗannan yarukan sun soma bauta wa Jehobah.

Hotuna: Na 1. Wata ꞌyarꞌuwa da take yin ɗaya daga cikin ƙananan yarukan da ake yi a Kudanci da Arewacin Amurka, ta riƙe Littafi Mai Tsarki na yarensu tana murmushi. Na 2. Wata ꞌyarꞌuwa da ꞌyarta da suke yin yaren Romany suna jin daɗin jawabai a yarensu a wani babban taro.

Hagu: Ƙananan yarukan da ake yi a Kudanci da Arewacin Amurka fiye da 160

Dama: Yarukan Romany fiye da 20

(Ka duba sakin layi na 11)


12. Waɗanne abubuwa ne kuma ƙungiyar Jehobah take tanadar wa mutane?

12 Ban da taimaka wa mutane su ji waꞌazin labari mai daɗi, ƙungiyar Jehobah tana taimaka wa waɗanda balaꞌi ya shafa. Saboda haka, dubban ꞌyanꞌuwa suna a shirye don su taimaka wa ꞌyanꞌuwansu maza da mata da suke da bukata. Ƙungiyar Jehobah tana kuma tanadar mana da wuraren da muke ibada da kuma koyan abubuwa game da yadda Jehobah yake ƙaunar mu.

YESU ZAI IYA TAIMAKA MAKA

13. A Waɗanne hanyoyi ne Yesu yake taimaka mana?

13 Da yake Yesu makiyayi ne mai kyau, yana tabbata cewa muna da abin da muke bukata don mu kusaci Jehobah. (Yoh. 10:14; Afis. 4:7) A wasu lokuta mukan yi sanyi gwiwa sosai har mu ji kamar mu kara ne mara ƙarfi ko fitila da ta kusan mutuwa. Wataƙila mukan ji hakan ne don wata rashin lafiya mai tsanani da muke fama da ita, ko mun yi kuskure, ko kuma mu sami saɓani da wani ɗanꞌuwa a ikilisiya. A irin wannan yanayin, za mu iya mai da hankali a kan matsalolin da muke fama da su maimakon begen da muke da shi na nan gaba. Ka tuna cewa Yesu ya san yanayin da kake ciki kuma ya fahimci yadda kake ji. Da yake Yesu mai tausayi ne yana so ya taimaka maka. Alal misali, Yesu zai iya amfani da ruhu mai tsarki ya ƙarfafa ka a lokacin da ka yi sanyi gwiwa. (Yoh. 16:7; Tit. 3:6) Ƙari ga haka, zai iya amfani da dattawa, ko ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya su ƙarfafa ka da kuma taimaka maka.—Afis. 4:8.

14. Mene ne za mu iya yi idan mun yi sanyin gwiwa?

14 Idan wani abu yana ci maka tuwo a ƙwarya, ka tuna cewa Yesu ne Babban Firist ɗinmu, kuma ka yi tunani a kan abin da hakan yake nufi. Ka tuna cewa Jehobah ya turo shi duniya ba kawai don ya ba da ransa ba, amma don ya ƙara fahimtar irin matsalolin da ꞌyanꞌadam ajizai suke fama da su. Idan mun yi sanyi gwiwa don zunubai ko kurakuren da muka yi, Yesu yana shirye ya taimaka mana a daidai lokacin da muke bukata.—Ibran. 4:​15, 16.

15. Mene ne ya taimaka wa wani ɗanꞌuwa ya dawo cikin ikilisiya?

15 Yesu yana sa mabiyansa su taimaka wa waɗanda suka bar Jehobah su sake dawowa. (Mat. 18:​12, 13) Ka yi laꞌakari da labarin Stefano.b Bayan shekaru 12 da aka cire shi daga ikilisiya, ya yanke shawarar sake halartan taro. Ya ce: “Hakan bai min sauƙi ba, amma ina so in sake kasance a cikin iyalin Jehobah. Dattawan da suka tattauna da ni sun kwantar mini da hankali. A wasu lokuta nakan ga kamar na ɓata wa Jehobah rai sosai har in ji kamar ba zai ƙara amincewa da ni ba. Amma dattawan sun tuna mini cewa Jehobah da Yesu ba sa so in karaya. A lokacin da aka mai da ni cikin ikilisiya dukan ꞌyanꞌuwa a ikilisiya sun marabce ni sosai. Daga baya matata ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Yanzu muna bauta wa Jehobah tare.” Babu shakka Babban Firist ɗinmu yana farin ciki sosai idan ya ga dukan ꞌyanꞌuwa suna taimaka wa wanda ya yi zunubi ya dawo cikin ikilisiya.

16. Me ya sa muke godiya don muna da Babban Firist mai tausayi?

16 Saꞌad da Yesu yake duniya ya taimaka wa mutane da yawa a lokacin da suke da bukata. A yau muna da tabbaci cewa zai taimaka mana. Kuma a sabuwar duniya zai taimaka wajen ꞌyantar da ꞌyanꞌadam daga zunubi da kuma ajizanci. Muna godiya sosai ga Jehobah, don yadda yake ƙaunar mu kuma ya ba mu Ɗansa mai tausayi ya zama Babban firist ɗinmu!

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya rayuwa a matsayin ɗanꞌadam ya taimaka wa Yesu ya zama Babban Firist mai tausayi?

  • Ta yaya Yesu ya cika annabcin da ke Ishaya 42:3?

  • Ta yaya Babban Firist ɗinmu yake taimaka mana a yau?

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misalin Yesu

a Don ƙarin bayani game da yadda Yesu ya maye gurbin babban firist na Yahudawa, ka duba talifin nan “Kar Ka Yi Wasa da Gatan Bauta wa Jehobah a Haikalinsa Na Alama” a Hasumiyar Tsaro na Oktoba 2023 shafi na 26, sakin layi na 7-9.

b An canja sunan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba