Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Oktoba pp. 6-11
  • Jehobah Shi Ne ‘Tushen Farin Cikinmu’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Shi Ne ‘Tushen Farin Cikinmu’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH NE TUSHEN FARIN CIKI
  • KAR KA BAR KOME YA HANA KA FARIN CIKI
  • Farin Ciki​—Hali Ne da Muke Koya Daga Wurin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Yadda Za Ka Ƙara Jin Daɗin Yin Waꞌazi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Bayarwa Za Ta Sa Ka Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Oktoba pp. 6-11

TALIFIN NAZARI NA 40

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

Jehobah Shi Ne ‘Tushen Farin Cikinmu’

“ Zan je . . . gare ka . . . ya Allah, tushen farin cikina.”—ZAB. 43:4.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abubuwan da za su iya sa mu daina farin ciki, da kuma abubuwan da za mu iya yi da za su sake sa mu farin ciki.

1-2. (a) Wane yanayi ne mutane da yawa suke ciki a yau? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

MUTANE da yawa a yau suna yin abubuwa dabam-dabam don su yi farin ciki. Duk da haka, ba sa farin ciki. Mutane da yawa suna baƙin ciki kuma suna ganin cewa abubuwa za su daɗa taɓarɓarewa a rayuwarsu. Wasu bayin Jehobah ma suna fama da irin wannan tunanin. Da yake muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe,” za mu iya fuskantar matsalolin da za su sa mu damu ko kuma mu yi baƙin ciki sosai.—2 Tim. 3:1.

2 A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwan da za su iya sa mu daina farin ciki, da yadda za mu sake yin farin ciki idan hakan ya faru. Yanzu, bari mu ga Wanda zai iya taimaka mana mu kasance da farin ciki na gaske.

JEHOBAH NE TUSHEN FARIN CIKI

3. Mene ne halittu suke koya mana game da Jehobah? (Ka kuma duba hotunan.)

3 Jehobah, Allah ne mai farin ciki. Kuma yana son mu ma mu kasance da farin ciki a kowane lokaci. Shi ya sa ya halicci abubuwa da yawa da za su sa mu farin ciki. Alal misali, muna farin ciki idan muka ga yadda duniyarmu take cike da kaloli dabam-dabam, muna kuma jin daɗi idan muka ga dabbobi suna wasa. Ƙari ga haka, muna farin ciki idan muka sami abincin da muke so sosai. Babu shakka, Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana so mu yi farin ciki!

Hotuna: Dabbobi dabam-dabam suna wasa. Na 1. Ɗan ƙaramin giwa yana wasa a cikin ruwa. Na 2. Yaran tsuntsun penguin suna wasa a dusar ƙanƙara. Na 3. Ƙananan awaki suna wasa suna tsalle. Na 4. Kifin dolphin suna wasa kuma sun tashi sama daga cikin ruwa.

Baby elephant: Image © Romi Gamit/Shutterstock; penguin chicks: Vladimir Seliverstov/500px via Getty Images; baby goats: Rita Kochmarjova/stock.adobe.com; two dolphins: georgeclerk/E+ via Getty Images

Yadda dabbobi suke wasa ya nuna cewa Jehobah, Allah ne mai farin ciki (Ka duba sakin layi na 3)


4. (a) Me ya sa Jehobah yake farin ciki duk da cewa yana ganin irin matsalolin da muke fama da su? (b) Ta yaya Jehobah yake taimaka mana a yanzu? (Zabura 16:11)

4 Ko da yake Jehobah “Allah mai farin ciki” ne, ya san irin matsalolin da muke fama da su a duniyar nan. (1 Tim. 1:​11, NWT) Amma sanin hakan bai hana shi farin ciki ba. Ya san cewa dukan matsalolin da muke fama da su za su ƙare wata rana. Shi da kansa ne ya saka wannan ranar. Kuma yana jiran ranar ta kai ne domin ya kawo ƙarshen matsalolinmu har abada. Amma kafin wannan lokacin, yana taimaka mana yanzu idan muna fama da wata matsala. Ta yaya yake taimaka mana? Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce, ta wajen sa mu yi farin ciki. (Karanta Zabura 16:11.) Bari mu ga yadda sanin Jehobah ya sa Yesu farin ciki.

5-6. Me ya sa Yesu yake farin ciki?

5 A cikin dukan halittun Jehobah, Yesu ne ya fi farin ciki. Me ya sa muka ce hakan? Ga dalilai guda biyu: (1) Yana da hali irin na Ubansa, shi ya sa yake farin ciki sosai. (Kol. 1:15; 1 Tim. 6:15) (2) Yesu ya yi shekaru aru-aru tare da Jehobah fiye da kowa, Wanda shi ne tushen farin ciki.

6 Yesu yana farin ciki domin yana yin abin da Ubansa yake so a kowane lokaci. (K. Mag. 8:​30, 31; Yoh. 8:29) Shi ya sa Jehobah yake alfahari da shi.—Mat. 3:17.

7. Mene ne zai taimaka mana mu yi farin ciki?

7 Mu ma za mu yi farin ciki idan muka ci-gaba da kusantar Jehobah wanda shi ne Tushen farin ciki. Idan muna yawan koya game da Jehobah kuma muna bin misalinsa, za mu yi farin ciki sosai. Za mu kuma yi farin ciki idan muna yin abin da Jehobah yake so, da kuma sanin cewa ya amince da mu.a (Zab. 33:12) Gaskiyar ita ce, a wasu lokuta, za mu iya yin baƙin ciki, mai yiwuwa na ꞌyan kwanaki ko kuma na dogon lokaci. Idan hakan ya faru, bai kamata mu ɗauka cewa Jehobah bai amince da mu ba. Jehobah ya san cewa a wasu lokuta za mu yi baƙin ciki ko kuma mu ji zafi don wani abu ya same mu. (Zab. 103:14) Yanzu bari mu ga abubuwan da za su iya sa mu daina farin ciki, da kuma yadda za mu sake yin farin ciki.

Yadda Jehobah Yake Sa Mu Farin Ciki

Mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki. Ruhun Jehobah ne kawai zai iya taimaka mana mu yi farin ciki. (Gal. 5:22) Da taimakon ruhu mai tsarki, za mu iya jimre kowane yanayin da muke ciki, mu yi haƙuri, kuma mu yi farin ciki.—Kol. 1:11.

Mu sa bautar Jehobah kan gaba a rayuwarmu. Mu riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma karanta littattafanmu. Mu yi amfani da kowace damar da muka samu wajen gaya wa mutane “labari mai daɗi da zai sa dukan mutane farin ciki sosai.” (Luk. 2:10) Idan bautar Jehobah ce ta fi muhimmanci a rayuwarmu, za mu yi farin ciki.—Zab. 65:4.

Mu riƙa yin abin da Jehobah yake so a kowane lokaci. Mu tuna cewa dokokin Jehobah don amfaninmu ne. Kuma idan muka bi dokokin, ba za su hana mu jin daɗi ba. Amma za su sa mu ji daɗin rayuwa kuma mu yi farin ciki.—Luk. 11:28.

KAR KA BAR KOME YA HANA KA FARIN CIKI

8. Me zai iya faruwa idan muna fama da matsaloli?

8 Idan muna fama da matsaloli. Shin, kana fama don ana tsananta maka, ko don talauci, ko don rashin lafiya, ko don tsufa, ko kuma don wani balaꞌi? Irin waɗannan matsalolin za su iya sa mu yi baƙin ciki sosai, musamman idan babu abin da za mu iya yi. Littafi Mai Tsarki ya ce, za mu iya yin baƙin ciki har mu ga kamar ba za mu sake yin farin ciki ba. (K. Mag. 15:13) Wani dattijo mai suna Charalambos ya ji kamar ba zai sake yin farin ciki ba, domin yayansa da kuma iyayensa sun mutu a cikin shekaru huɗu. Ya ce: “Na ji kamar ba ni da kowa kuma babu wanda zai iya taimaka mini. A wasu lokuta, nakan damu sosai, domin kafin iyayena da ɗanꞌuwana suka rasu, na so in riƙa kasancewa tare da su sosai. Amma hakan bai yiwu ba.” A wasu lokuta, matsalolinmu za su iya zama da wuya sosai har su sa mu gaji ko kuma mu yi sanyin gwiwa.

9. Me zai taimaka mana mu sake yin farin ciki? (Irmiya 29:​4-7, 10)

9 Me zai taimaka mana mu sake yin farin ciki? Za mu sake yin farin ciki idan muna nuna godiya don abubuwan da muke da su, kuma muka daina damuwa don abubuwan da ba za mu iya canjawa ba. A yau, mutane suna ganin kamar wajibi ne rayuwar mutum ta kasance babu matsala don ya iya yin farin ciki. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Alal misali, Jehobah ya gaya wa Yahudawan da aka kai bauta a Babila cewa su yi iya ƙoƙarinsu su ji daɗin rayuwa a wurin. (Karanta Irmiya 29:4-7, 10.) Me hakan ya koya mana? Mu yi ƙoƙari mu yi laꞌakari da abubuwa masu kyau da muke da su, kuma mu ji daɗin su. Mu kuma tuna cewa Jehobah zai taimaka mana, ba zai taɓa barin mu ba. (Zab. 63:7; 146:5) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Effie da ta yi hatsari kuma ba ta iya tafiya, ta ce: “Jehobah da iyalina da kuma ꞌyanꞌuwa maza da mata a ikilisiyarmu ne suka taimaka mini kuma suka ƙarfafa ni. Don in nuna musu cewa ina godiya, na yi iya ƙoƙarina in kasance da farin ciki.”

10. Me ya sa za mu iya yin farin ciki ko da muna fama da matsaloli?

10 Ko da muna fama da matsaloli, ko wani mummunan abu ya same mu ko danginmu, za mu iya ci-gaba da yin farin ciki.b (Zab. 126:5) Me ya sa? Domin ba yanayin da muke ciki ne ainihin abin da yake sa mu farin ciki ba. Wata majagaba mai suna Maria ta ce: “Idan muna fama da matsaloli, kuma muna farin ciki, hakan ba ya nufin cewa ba za mu yi kuka ko mu faɗi abin da ke zuciyarmu ba. Amma yin farin ciki zai nuna cewa ba mu manta da alkawuran Jehobah ba. Kuma Jehobah zai sa mu ci-gaba da yin hakan a duk yanayin da muka sami kanmu.” Ka tuna cewa, komin wuyan yanayin da kake ciki yanzu, ba zai dawwama ba. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai cire duk wani abin da yake sa mu wahala ko baƙin ciki.

11. Ta yaya labarin manzo Bulus ya ƙarfafa ka?

11 A wasu lokuta, za mu iya ganin kamar muna fama da matsaloli ne domin Jehobah ba ya son abin da muke yi. Idan haka muke ji, zai dace mu yi laꞌakari da labaran bayin Jehobah da suka yi fama da matsaloli. Alal misali, Yesu ne da kansa ya zaɓi manzo Bulus ya je ya yi wa “alꞌummai, da sarakuna, da kuma ꞌyaꞌyan Israꞌila” waꞌazi. (A. M. 9:15) Wannan aiki ne mai muhimmanci! Duk da haka, Bulus ya yi fama da matsaloli da yawa. (2 Kor. 11:​23-27) Shin, matsalolin da Bulus ya yi fama da su sun nuna cewa Jehobah ba ya jin daɗin abin da yake yi ne? Aꞌa! Jehobah ne ya taimaka masa ya iya jimre matsalolin. (Rom. 5:​3-5) Yanzu, ka yi tunani game da naka matsalolin. Duk da matsalolin nan, ka ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Saboda haka, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana taimaka maka kuma ya amince da kai.

12. Me zai iya faruwa idan ba mu sami damar yin wata hidimar da muke so ba?

12 Idan ba ka sami damar yin abin da kake so ba. (K. Mag. 13:12) Muna ƙaunar Jehobah kuma muna godiya don kome da yake mana. Hakan yakan sa mu nemi hanyoyin faɗaɗa hidimarmu. Sai dai, idan muna so mu yi wani abu amma ya fi ƙarfinmu don yanayin da muke ciki, hakan zai iya sa mu karaya. (K. Mag. 17:22) Wata majagaba mai suna Holly ta ce: “Na so in je Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki, in yi hidima a ƙasar waje, ko in yi aikin gine-gine a Ramapo. Amma yanayina ya canja kuma na gagara yin waɗannan abubuwan. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai.” Bayin Jehobah da yawa ma suna fama da irin wannan yanayin.

13. Ko da a wane irin yanayi ne muke ciki, waɗanne abubuwa ne za mu iya yi?

13 Abin da zai taimaka mana mu sake yin farin ciki. Ka tuna cewa Jehobah ba zai so ka yi abin da ba za ka iya ba. Jehobah yana daraja mu ko da ba za mu iya yin abin da wasu suke yi ba. Yana so mu san abin da za mu iya yi kuma mu yi hakan da aminci. (Mik. 6:8; 1 Kor. 4:2) Jehobah yana farin ciki idan muna da halayen kirki, muna tunani da kuma yin abubuwan da yake so. Saboda haka, ba zai dace mu so yin abin da ba za mu iya yi ba.c Idan yanayinka ya rage abubuwan da za ka iya yi a hidimar Jehobah, ka mai da hankali a kan waɗanda za ka iya. Alal misali, za ka iya taimaka wa matasa su ƙware, ko kuma ka riƙa ƙarfafa ꞌyanꞌuwan da suka tsufa. Ƙari ga haka, za ka iya ziyartar wani ɗanꞌuwa don ka ƙarfafa shi ko ka kira shi ta waya, ko kuma ka tura masa saƙo. Jehobah zai sa ka yi farin ciki yayin da kake yin iya ƙoƙarinka wajen yin abin da za ka iya yi! Kuma ka tuna cewa nan ba da daɗewa ba, za mu sami damar yi wa Jehobah hidima a hanyoyin da ba mu taɓa tsammani ba! ꞌYarꞌuwa Holly da aka ambata ɗazu ta kammala da cewa: “Idan na soma yin sanyin gwiwa, nakan dakata kuma in tuna cewa zan yi rayuwa har abada. Da taimakon Jehobah, a sabuwar duniya, zan iya yin abubuwan da nake so in yi a hidimarsa.”

14. Mene ne kuma zai iya hana mu yin farin ciki?

14 Idan kuɗi ko wasu abubuwa ne suke sa mu farin ciki. A dandalin sada zumunta, za mu iya gani kamar wasu suna farin ciki domin suna jin daɗi a kowane lokaci. Mu ma za mu iya soma ganin kamar idan muna yin abubuwan da muke so, mu sayi abubuwan da muke so, kuma mu je wurare dabam-dabam, za mu yi farin ciki. Yin waɗannan abubuwan ba laifi ba ne. Jehobah ya halicce mu yadda za mu ji daɗin abubuwan da ya halitta. Amma mutane da yawa da suke ƙoƙarin jin daɗi kawai, sun gano cewa abubuwan da suke tsammanin za su sa su farin ciki, ba su sa su farin ciki ba. Wata majagaba mai suna Eva ta ce, “Idan abin da kake so kawai shi ne, ka yi ta jin daɗi, ba zai taɓa isan ka ba.” Idan jin daɗi ne kawai muke so mu riƙa yi kowane lokaci, ba za mu taɓa gamsuwa ba, kuma za mu yi baƙin ciki.

15. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Sarki Sulemanu?

15 Labarin Sarki Sulemanu ya koya mana mummunan sakamakon da son jin daɗi kawai yake jawowa. Alal misali, ya samu ya ci abinci kala-kala masu daɗin gaske, ya saurari waƙoƙi masu daɗi, kuma ya sayi abubuwa masu tsada. Amma dukan abubuwan nan ba su sa shi farin ciki ba. Ya ce: “Idanu ba sa ƙoshi da gani, kunnuwa ma ba sa ƙoshi da ji.” (M. Wa. 1:8; 2:​1-11) Raꞌayin mutanen duniya game da yin farin ciki yana kama da jebun kuɗi. Jebun kuɗi yana kama da kuɗi mai kyau, amma ba za mu iya yin kome da shi ba.

16. Mene ne zai taimaka mana mu sake yin farin ciki? (Ka kuma duba hotunan.)

16 Mene ne zai taimaka mana mu sake yin farin ciki? Yesu ya koya mana cewa, “bayarwa tana sa farin ciki fiye da karɓa.” (A. M. 20:35) Wani dattijo mai suna Alekos ya ce: “Ina yi wa mutane ƙananan abubuwa don in taimaka musu. Saꞌad da nake taimaka musu, ina mai da hankali ga nasu matsalolin maimakon nawa, kuma hakan na sa ni farin ciki.” Waɗanne abubuwa ne za ka iya yi don ka taimaka wa mutane? Alal misali, idan ka ga wani yana baƙin ciki, ka ƙarfafa shi. Wataƙila ba za ka iya magance matsalarsa ba, amma za ka iya ƙarfafa shi idan ka saurare shi da kyau, ka tausaya masa kuma ka tuna masa cewa Jehobah zai taimaka masa. (Zab. 55:22; 68:19) Za ka kuma iya tuna masa cewa Jehobah bai yashe shi ba. (Zab. 37:28; Isha. 59:1) Ƙari ga haka, za ka iya yin wasu abubuwa don ka taimaka masa kamar dafa abinci da dai sauransu. Za ku kuma iya fita waꞌazi tare, domin yin waꞌazi yana sa mu farin ciki. Ka bar Jehobah ya yi amfani da kai wajen ƙarfafa mutane. Idan muna taimaka wa mutane, za mu yi farin ciki ƙwarai!—K. Mag. 11:25.

Hotuna: Na 1. Wata ꞌyarꞌuwa tana zaune ita kaɗai a wurin shan shayi tana danna waya. Na 2. Ta ziyarci wata ꞌyarꞌuwa da ta tsufa kuma ta ba ta damin fulawa.

Maimakon ka mai da hankali a kan abin da kake so, ka mai da hankali wajen taimaka wa wasu (Ka duba sakin layi na 16)d


17. Mene ne za mu yi idan muna so mu yi farin ciki? (Zabura 43:4)

17 Za mu yi farin ciki idan muka ci-gaba da kusantar Jehobah kuma muna yin abubuwan da yake so. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Jehobah shi ne ‘Tushen farin cikinmu.’ (Karanta Zabura 43:4.) Saboda haka, ko da mene ne muke fama da shi a rayuwa, bai kamata mu damu ko mu ji tsoro ba. Idan mu aminan Jehobah ne, zai taimaka mana mu yi farin ciki har abada!—Zab. 144:15.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa Jehobah da Yesu suke farin ciki?

  • Waɗanne abubuwa ne za su iya sa mu daina farin ciki?

  • Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu sake yin farin ciki?

WAƘA TA 155 Jehobah ne Ke Sa Mu Farin Ciki

a Ka duba akwatin nan “Yadda Jehobah Yake Sa Mu Farin Ciki.”

b Alal misali, ka duba ganawar da aka yi da Ɗanꞌuwa da ꞌYarꞌuwa Christensen a 2023 Karin Bayani na 5 Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu a jw.org/ha.

c Don samun ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Ka Kafa Makasudai da za su Yiwu Kuma ka Yi Farin Ciki” a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Yuli, 2008.

d BAYANI A KAN HOTO: Wata ꞌyarꞌuwa ta saya wa kanta abubuwa dabam-dabam. Amma ta fi yin farin ciki da ta saya wa wata tsohuwa fulawa don ta ƙarfafa ta.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba