Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Yuni pp. 26-31
  • Mun Koyi Darussa da Dama Daga Malamin da Babu Kamar Sa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mun Koyi Darussa da Dama Daga Malamin da Babu Kamar Sa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • IYAYENMU SUN ƘAFA MINI MISALI MAI KYAU
  • MUN SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI
  • HIDIMARMU A ƘASASHEN WAJE
  • HIDIMA A TURAI DA KUMA AFIRKA
  • HIDIMA A GABAS TA TSAKIYA
  • MUN SAKE DAWOWA AFIRKA
  • Na Kudurta Cewa Ba Zan Karaya Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Jehobah Ya Albarkace Ni Fiye da Yadda Na Yi Tsammani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Jehobah Ya ‘Daidaita Hanyoyina’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Albarkun da Muka Samu da Kuma Darussan da Muka Koya a Hidimarmu ga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Yuni pp. 26-31
Franco Dagostini.

TARIHI

Mun Koyi Darussa da Dama Daga Malamin da Babu Kamar Sa

FRANCO DAGOSTINI NE YA BA DA LABARIN

SAꞌAD DA muke hidimar majagaba da kuma waꞌazi a kasashen waje, ni da matata mun yi fama da abubuwa dabam-dabam. Wasu daga cikinsu su ne, yaƙin basasa, da ƙone-ƙone, da mahaukaciyar guguwa, da guduwa daga gidajenmu. A wasu wuraren kuma, mun haɗu da sojoji ɗauke da mayan makamai, ga kuma wuraren bincika ababan hawa da suke koꞌina. Duk da matsalolin nan, muna farin ciki cewa mun zaɓi mu yi hidima ta cikakken lokaci! A dukan rayuwarmu, Jehobah ya taimaka mana kuma ya ci gaba da yi mana albarka. A matsayinsa na malami da babu kamar sa, ya koya mana darussa masu muhimmanci.—Ayu. 36:22; Isha. 30:20.

IYAYENMU SUN ƘAFA MINI MISALI MAI KYAU

A 1957, iyayenmu sun ƙaura daga Italiya zuwa Kindersley, da ke Saskatchewan, a ƙasar Kanada. Ba da daɗewa ba bayan hakan, sun koyi gaskiya kuma ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Na tuna lokacin da nake ɗan yaro, iyalinmu suna daɗewa sosai a waꞌazi har ma a wasu lokuta nakan yi wasa cewa na yi “majagaba na ɗan lokaci” saꞌad da nake shekara takwas!

Franco tare da iyayensa da ꞌyanꞌuwansa lokacin da yake ƙarami.

Tare da iyayenmu da ꞌyanꞌuwana, a wajen 1966

Iyayenmu talakawa ne, duk da haka, sun ƙafa mana misali mai kyau wajen yin sadaukarwa a bautar Jehobah. Alal misali, a 1963 sun sayar da kayansu da yawa don su sami isashen kuɗin halartan taron ƙasa da ƙasa da aka yi a Pasadena, Kalifoniya, da ke Amurka. A 1972, mun ƙaura zuwa Trail da ke British Columbia a Kanada don mu taimaka wajen yi wa mutanen da ke yaren Italiya waꞌazi, kuma wurin na da nisa daga inda muke. Babana yana kula da kuma share wani babban shago. Sau da yawa, ya ƙi karɓan ƙarin matsayi don ya iya mai da hankali ga bautar Jehobah.

Ina godiya don misali mai kyau da iyayenmu suka ƙafa wa ni da ꞌyanꞌuwana uku. Misalinsu ya taimaka mini sosai a hidimata ga Jehobah, kuma sun koya mini wani abin da ba zan taɓa mantawa ba: Cewa idan na sa Mulkin Allah farko a rayuwata, Jehobah zai kula da ni.—Mat. 6:33.

MUN SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI

A 1980, na auri wata kyakkyawar ꞌyarꞌuwa mai suna Debbie da take bauta wa Jehobah da dukan zuciyarta. Mun so mu soma hidima ta cikakken lokaci, don haka, Debbie ta soma hidimar majagaba wata uku bayan aurenmu. Da aurenmu ya kai shekara ɗaya, mun ƙaura zuwa wata ikilisiya inda ake bukatar masu shela. A wurin ne na soma hidimar majagaba tare da matata.

Franco da Debbie a ranar auren su.

Ranar aurenmu a 1980

Da shigewar lokaci, mun yi sanyin gwiwa kuma muka yanke shawara cewa za mu bar wurin. Amma kafin mu yi hakan, mun tattauna da mai kula da daꞌirarmu. Ya nuna mana ƙauna, amma ya gaya mana gaskiya babu ɓoye-ɓoye. Ya ce: “Ku ne kuke sa yanayinku yake ƙara yin wuya. Kuna mai da hankali ne a kan abubuwan da kuke fama da su. Idan kuka mai da hankali a kan albarkun da kuke samuwa, za ku gan su.” Wannan abin da ya gaya mana abu ne da muke bukata a lokacin. (Zab. 141:5) Ba tare da ɓata lokaci ba, mun bi shawarar da ya ba mu, kuma nan da nan, mun ga cewa akwai albarku da yawa da muke samuwa. Mun ga cewa mutane da yawa a ikilisiya suna so su faɗaɗa hidimarsu ga Jehobah, a cikin su akwai yara maza da mata da kuma wasu mata da mazajensu ba Shaidu ba. Hakan ya koya mana darasi mai muhimmanci. Mun koyi cewa mu riƙa mai da hankali ga albarkun da muke samuwa da kuma dogara ga Jehobah, da tabbaci cewa zai taimaka mana mu jimre kowane yanayi da muke ciki. (Mik. 7:7) Mun sake soma farin ciki kuma abubuwa suka soma gyaruwa.

Malaman da suka koyar da mu a makarantar hidimar majagaba na farko da muka halarta, sun taɓa hidima a ƙasashen waje. Sun nuna mana hotuna kuma sun gaya mana game da kalubale da albarkun da suka samu yayin da suke hidima a wasu ƙasashe. Hakan ya sa muka soma tunanin yin hidima a ƙasashen waje, kuma ni da matata mun yarda cewa za mu yi hakan.

Wurin faka motoci a wani Majami’ar Mulki da dusar ƙanƙara ta mamaye kuma an tuttura su gefe-gefe don a iya wucewa.

A Majamiꞌar Mulki da ke British Columbia, a 1983

Don mu cim ma maƙasudinmu, a 1984 mun ƙaura zuwa Quebec, inda ake Faransanci. Wurin na da nisan kilomita 4,000 daga British Columbia. A wurin, mun bukaci mu koyi sabon alꞌada da yare. Wata matsala kuma da muka yi fama da ita, ita ce ƙarancin kuɗi. Akwai lokacin da ba mu da wani abin da za mu ci, sai dai dankali da wani manomi ya bar mu mu yi kale a gonarsa. Matata ta zo ta ƙware a dafa dankali a hanyoyi dabam-dabam! Duk da matsalolin nan, mun ci gaba da jimrewa da farin ciki kuma mun ga cewa Jehobah yana kula da mu.—Zab. 64:10.

Wata rana ba zato ba tsammani, aka kira mu a waya. An gayyace mu zuwa ofishinmu da ke Kanada, mu yi hidima a wurin. Ba mu san ko mu yi kuka ne ko mu yi farin ciki ba, domin kafin wannan lokacin mun cika fom na zuwa Makarantar Gilead. A ƙarshe dai, mun yanke shawara za mu je. Da muka isa, mun haɗu da Ɗanꞌuwa Kenneth Little, wanda shi memban Kwamitin da Ke Kula da Reshen Ofishinmu ne. Sai muka tambaye shi cewa, “Me za mu yi ke nan idan aka gayyace mu Makarantar Gilead?” Sai ya ce, “Kar ku damu, za mu san abin da za mu yi a lokacin.”

Maƙo ɗaya bayan hakan, sai lokacin ya yi, domin an gayyace mu zuwa Makarantar Gilead. Hakan ya raɓa hankalinmu, muka soma tunanin wanda za mu zaɓa. Amma Ɗanꞌuwa Little ya gaya mana cewa: “Duk wanda kuka zaɓa, a kwana a tashi za ku gwammaci da kun zaɓi ɗayan. Ba wanda ya fi wani, Jehobah zai albarkace ku ko da wanne ne kuka zaɓa.” Mun karɓi gayyatar zuwa Makarantar Gilead, kuma da shigewar lokaci mun ga cewa abin da Ɗanꞌuwa Little ya faɗa gaskiya ne. Mun sha gaya wa mutanen da suka sami damar yin hidima a wurare guda biyu kuma suna bukatar su zaɓi ɗaya wannan abin da ya gaya mana.

HIDIMARMU A ƘASASHEN WAJE

(Hagu) Ulysses Glass

(Dama) Jack Redford

Mun yi farin cikin kasancewa cikin ɗalibai 24 da suka halarci aji na 83 na Makarantar Gilead. An soma makarantar a Afrilu 1987 ne, a Brooklyn, birnin New York. Ɗanꞌuwa Ulysses Glass da Ɗanꞌuwa Jack Redford, su ne ainihin malamanmu. Kafin mu ce kobo, wata biyar ya zo ya wuce, kuma mun sauƙe karatu a ranar 6 ga Satumba, 1987. Sai aka tura mu Haiti, tare da Ɗanꞌuwa John Goode da matarsa Marie.

Franco da Debbie suna waꞌazi a wani bakin teku a Haiti.

A Haiti a 1988

Tun daga 1962 aka kori masu waꞌazi a ƙasashen waje daga ƙasar Haiti, kuma tun daga lokacin, ba a sake tura wasu ba sai mu. Ni da matata mun soma hidima a wata ikilisiya da ke da masu shela 35 a wani ƙauye. A lokacin mu matasa ne, kuma muna da abubuwa da yawa da muke bukatar mu koya. Ban da haka ma, mu kaɗai ne muke zama a gidan masu waꞌazi a ƙasashen waje. Mutanen ƙauyen talakawa ne sosai, kuma yawancinsu ba su iya karatu ba. Ana nan sai matsalolin siyasa suka sa aka soma tashin hankali kuma aka yi ƙoƙarin juyin mulki, ana ta zanga-zanga, ga kuma mahaukaciyar guguwa.

Mun koyi abubuwa da yawa daga ꞌyanꞌuwa maza da mata da ke Haiti. Duk da cewa suna fama da matsaloli da yawa, sun ci gaba da kasancewa da ƙarfin zuciya da farin ciki. Suna ƙaunar Jehobah kuma suna son yin waꞌazi. Wata ꞌyarꞌuwa gwauruwa da ta tsufa da ba ta iya karatu ba, ta haddace ayoyi wajen 150. Matsalolin da ake fuskanta a wurin sun sa mun ƙara ƙwazo wajen gaya wa mutane cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai iya magance matsalolin ꞌyanꞌadam. Mun yi farin cikin ganin yadda wasu ɗalibanmu na farko-farko suka zama majagaba na kullum, da majagaba na musamman, da kuma dattawa.

Saꞌad da muke Haiti, na haɗu da wani matashi mai suna Trevor. Shi dan addinin Mormon ne kuma yana waꞌazi a ƙasar waje. Ni da shi mun tattauna wasu batutuwa daga Littafi Mai Tsarki. Bayan wasu shekaru, na samu wasiƙa daga wurinsa ba zato. A wasiƙar ya ce: “Za a yi min baftisma a taron daꞌira mai zuwa! Zan so in dawo Haiti in yi hidimar majagaba na musamman a inda dā nake aikin waꞌazi na addinin Mormon.” Kuma abin da ya yi ke nan, ya yi shekaru da yawa yana hidima tare da matarsa.

HIDIMA A TURAI DA KUMA AFIRKA

Franco a wurin aikinsa.

A wurin aiki a Slovenia, a 1994

An tura mu wani wuri a Turai, kuma a lokacin an soma cire takunkumin da aka sa a aikinmu. A 1992 ne muka isa Ljubljana, da ke Slovenia, kusa da wurin da iyayenmu suka yi girma kafin suka ƙaura zuwa Italiya. A lokacin ana kan yaƙi a yankunan da ke ƙarƙashin Yugoslavia ta dā. ꞌYanꞌuwan da ke Vienna, a Ostiriya, da waɗanda suke Zagreb, a Kuroshiya, da kuma Belgrade, a Sabiya, ne suke kula da aikin waꞌazi da ake yi a yankunan Yugoslavia ta dā. Amma yanzu, kowannensu na bukatar nasa reshen ofishi domin sun sami ꞌyanci.

Hakan yana nufin muna bukatar mu sake koyan wani sabon yare da kuma alꞌada. Yawancin mutane sukan ce: “Yaren yana da wuya.” Kuma hakan gaskiya ne! Amma yadda ꞌyanꞌuwan da suke wurin suka karɓi canje-canjen da ƙungiyarmu ta yi, da yadda Jehobah ya albarkace su ya burge mu sosai. A wannan ƙaron kuma, mun ga yadda Jehobah yake sa abubuwa su gyaru a lokacin da ya kamata. Mun koyi darussa da yawa a zamanmu a Slovenia kuma darussan da muka koya a dā sun taimaka mana mu jimre matsalolin da muka yi fama da su.

Amma da sauran rina a kaba. A shekara ta 2000, an tura mu Kwat Dibuwa, da ke yammancin Afirka. Da aka soma yaƙin basasa a wurin, a Nuwamba 2002, an ƙaurar da mu zuwa Saliyo, inda aka yi shekaru 11 ana yaƙin basasa. Kuma ba a daɗe da gama yaƙin lokacin da muka zo ba. Ya yi mana wuya mu bar Kwat Dibuwa ba tare da shiri ba. Amma darussan da muka koya sun taimaka mana mu ci gaba da yin farin ciki.

Mun mai da hankali a kan ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka yi shekaru suna fama da yaƙi, da kuma mutane da yawa da suke so su koyi gaskiya game da Allah. Duk da cewa yawancinsu talakawa ne, suna da halin bayarwa hannu sake. Wata ꞌyarꞌuwa ta ba wa matata kayan sawa. Da farko, matata ta ƙi ta karɓa, amma ꞌyarꞌuwar ta nace ta ce: “Yanzu ya kamata mu taimaka muku, domin a lokacin yaƙin, ꞌyanꞌuwa daga wasu ƙasashe sun taimaka mana.” A gaskiya, mu ma mun yi ƙoƙari mu yi koyi da irin halin nan.

Daga baya mun koma Kwat Dibuwa, amma an sake tashin hankali a wurin. Hakan ya sa a Nuwamba 2004, an kwashe mu a jirgin sama mai sauƙar angulu, aka kai mu masaukin sojoji kuma an ce kowannenmu jaka ɗaya ne kawai zai ɗauka. A wurin muka kwana a ƙasa, kuma washegari aka ɗauke mu a jirgin sama zuwa Suwizalan. Mun isa reshen ofishinmu da ke Suwizalan da tsakar dare. ꞌYanꞌuwa da ke Kwamitin da Ke Kula da Reshen Ofishinmu, da malaman Makarantar Koyar da Masu Hidima, tare da matansu, sun marabce mu sosai. Sun ba mu abinci kuma sun ba mu cakuleti da yawa. Mun yi farin ciki sosai saboda ƙaunar da suka nuna mana.

Franco yana ba da jawabi a Majami’ar Mulki da ke Kwat Dibuwa.

Yana ƙarfafa ꞌyanꞌuwan da suka yi gudun hijira a Kwat Dibuwa a 2005

Da farko an tura mu Ghana na ɗan lokaci. Daga baya muka koma Kwat Dibuwa bayan tashin hankalin ya lafa. Alherin da ꞌyanꞌuwanmu suka nuna mana ya taimaka mana mu iya jimre yanayoyin nan masu wuya. Ni da matata mun amince cewa, ko da yake nuna ƙauna irin wannan hali ne da aka san mu da shi a ƙungiyar Jehobah, ba za mu yi wasa da shi ba. Daga baya mun gano cewa matsalolin nan da muka fuskanta sun koya mana darussa da dama.

HIDIMA A GABAS TA TSAKIYA

Franco da Debbie sun ziyarci wani wurin da aka taɓa zama a dā a Gabas ta Tsakiya.

A Gabas ta Tsakiya, a 2007

A 2006, mun sami wasiƙa daga hedkwatarmu. A wasiƙar, an gaya mana cewa za mu soma hidima a Gabas ta Tsakiya. A nan, mun sake sabon lalle kuma, domin mun bukaci mu sake koya sabon yare da sabon alꞌadu. Kuma mun fuskanci wasu kalubale da ba waɗanda muka saba da su ba. Muna da abubuwa da yawa da za mu koya a wurin nan da mutane da yawa suna da tsattsaurar raꞌayi game da addini da kuma siyasa. Sai dai mun so yadda ꞌyanꞌuwanmu suke kasancewa da haɗin kai kuma suna bin ja-gorancin da ƙungiyarmu ke bayarwa, duk da cewa sun fito daga wurare dabam-dabam kuma suna yare dabam-dabam. ꞌYanꞌuwan suna burge mu domin yawancinsu suna jimre tsanantawa daga ꞌyanꞌiyalinsu, da maƙwabtansu, da abokan aikinsu, da kuma abokan makarantansu.

A 2012, mun halarci taron yanki na musamman a Tel Aviv, a ƙasar Israꞌila. Wannan taron yankin shi ne taro na farko da bayin Jehobah suka taru da yawa haka, bayan wanda aka yi a Fentakos na shekara 33 B.H.Y. Ba za mu taɓa manta da wannan taron ba!

A lokacin da muke hidima a Gabas ta Tsakiya, an tura mu mu ziyarci wata ƙasa da aka sa wa aikinmu takunkumi. Mun je da wasu littattafai, mun ɗan yi waꞌazi, kuma mun halarci ƙananan taron daꞌira da aka shirya. Sojoji ɗauke da manyan makamai da kuma wuraren bincika ababan hawa suna koꞌina. Duk da haka, ba mu ji tsoro ba domin akwai ꞌyanꞌuwa da suke raka mu duk inda za mu je.

MUN SAKE DAWOWA AFIRKA

Franco yana shirya jawabi da laptop ɗinsa.

Ina shirya jawabi a ƙasar Kwango a 2014

A 2013, an ce mu soma wata hidima dabam, wato mu je mu yi hidima a reshen ofishin da ke Kinshasa, a ƙasar Kwango. Babbar ƙasa ce da ke da kyau sosai amma suna fama da talauci da yaƙe-yaƙe. Da farko mun ce, “Ai mun san Afirka; don haka a shirye muke.” Amma gaskiyar ita ce, har ila akwai abubuwa da muke bukatar mu koya, kamar yin tafiye-tafiye a wuraren da babu hanyoyi masu kyau. Duk da haka, mun mai da hankalinmu ga abubuwa masu kyau. Kamar yadda ꞌyanꞌuwan suke jimrewa da farin ciki duk da matsalolin tattalin arzikin da suke fama da su, da yadda suke son fita waꞌazi, kuma suke ƙoƙarin halartan taro da manyan taro. Mun ga yadda aikin waꞌazinmu yake samun ci gaba domin Jehobah yana tare da mu kuma yana mana albarka. Hidima ta cikakken lokaci da muka yi a ƙasar Kwango ta koya mana darussa masu muhimmanci kuma ta sa mun sami abokai da suka zama iyalinmu.

Franco yana waꞌazi tare da wasu ꞌyanꞌuwa, suna gangarawa zuwa wani ƙauye.

Muna waꞌazi a Afirka ta Kudu a 2023

A ƙarshen shekara ta 2017, sai aka tura mu hidima a reshen ofishi na Afirka ta Kudu. Reshen ofishi mafi girma da muka taɓa yin hidima a ciki ke nan, kuma ba mu taɓa yin irin aikin da aka ce mu yi a wurin ba. A nan ma, mun ga abubuwa da yawa da za mu koya, kuma hidimomin da muka yi a dā sun taimaka mana mu san yadda za mu yi hakan. Muna ƙaunar ꞌyanꞌuwan da sun daɗe suna hidimarsu da aminci a reshen ofishin. Kuma mun ji daɗin ganin ꞌyanꞌuwa da suka fito daga wurare dabam-dabam suna aiki tare da haɗin kai, duk da cewa alꞌadunsu da launin fatarsu ba ɗaya ba ne. Mun ga yadda Jehobah yake sa mutanensa su zauna lafiya domin suna bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki.

Ni da matata mun yi shekaru muna yin hidima a wurare dabam-dabam, masu alꞌadu da kuma yare dabam-dabam da muke bukatar mu koya. Hakan bai yi mana sauƙi ba, amma mun ga yadda Jehobah ya yi amfani da ƙungiyarsa da kuma ꞌyanꞌuwanmu don ya nuna mana ƙauna marar canjawa. (Zab. 144:2) Abubuwa da yawa da muka koya a hidima ta cikakken lokaci sun taimaka mana mun ci gaba da inganta dangantakarmu da Jehobah.

Ina godiya sosai don renon da iyayena suka yi mini, da yadda matata ta taimaka mini, da misalai masu kyau na ꞌyanꞌuwa a faɗin duniya. A duk saꞌad da muke tunanin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba, mun ƙudiri niyar cewa za mu ci gaba da koyan darussa daga wurin Malaminmu da Babu Kamar Sa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba