Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Yuni p. 32
  • Yadda Za Mu Riƙa Tuna da Nassosi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Riƙa Tuna da Nassosi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Yin Amfani da JW Library
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Shawara A Kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Yuni p. 32

SHAWARA A KAN YIN NAZARI

Yadda Za Mu Riƙa Tuna da Nassosi

Ya taɓa yi maka wuya ka tuna da wata aya da kake so sosai? Mai yiwuwa, aya ce da ta ƙarfafa ka, ko wadda ta taimaka maka ka shawo kan tunanin da bai dace ba, ko kuma aya ce da kake so ka nuna ma wani. (Zab. 119:​11, 111) Ga wasu shawarwarin da za su taimaka maka ka riƙa tuna da irin nassosin nan.

  • Ka yi amfani da manhajar JW Library®. Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki a manhajar JW Library kuma ka ga wata ayar da kake so ka riƙa tunawa, za ka iya adanawa.a Hakan zai sa ka same ta da sauƙi a wani lokaci.

  • Ka manna ayar inda za ka iya gani. Ka rubuta ayar a wani fallen takarda kuma ka manna inda za ka riƙa gani kullum. Wasu sukan manna a jikin madubinsu, ko kuma a kofar firijinsu. Wasu kuma sukan ɗauka hoton ayar kuma su sa shi ya zama abu na farko da za su gani a wayarsu ko a kwamfutarsu idan suka buɗe shi.

  • Ka yi amfani da ƙaramin fefa da za ka iya yin rubuta gaba da baya. Ka rubuta sunan littafin, da surar, da kuma ayar a gefe ɗaya, sai ka rubuta abin da ayar ta ce a ɗayan gefen. Saꞌan nan, ka kalli inda ka rubuta sunan littafin, da surar, da ayar don ka ga ko za ka tuna da abin da ayar ta ce, ko kuma ka kalli inda ka rubuta abin da ayar ta ce don ka ga ko za ka iya tuna da sunan littafin da surar da kuma ayar.

a Don ƙarin bayani game da yadda za ka yi hakan, ka kalli bidiyon nan, Abubuwan da Ƙungiyarmu ta Cim ma—Abubuwa da Za Su Taimaka Mana Wajen Yin Amfani da JW Library da ke jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba