TALIFIN NAZARI NA 29
WAƘA TA 121 Mu Riƙa Kame Kanmu
Ka Yi Tsaro don Kada Ka Faɗi Cikin Jarraba
“Ku yi tsaro, ku kuma yi adduꞌa domin kada ku faɗi cikin jarraba.”—MAT. 26:41.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu guji yin zunubi, da kuma abubuwan da za su iya sa mu yi zunubi.
1-2. (a) Wane gargaɗi ne Yesu ya yi ma almajiransa? (b) Me ya sa almajiran suka gudu suka bar Yesu? (Ka kuma duba hotunan.)
“LALLAI ruhu ya yarda, amma jikin ba ƙarfi.”a (Mat. 26:41b) Yesu ya san cewa mu masu zunubi ne shi ya sa ya furta kalmomin nan. Amma abin da ya faɗa gargaɗi ne a gare mu, cewa kada mu buga ƙirji cewa ba za mu yi zunubi ba. Kafin ya furta kalmomin nan, almajiransa sun buga ƙirji cewa ba za su taɓa barin sa ba. (Mat. 26:35) Sun faɗi hakan ne domin suna da kyakkyawar niyya. Amma sun manta cewa su ajizai ne, kuma ba wuya su yi abin da bai dace ba idan suka shiga yanayi mai wuya. Shi ya sa Yesu ya yi musu gargaɗi cewa: “Ku yi tsaro, ku kuma yi adduꞌa domin kada ku faɗi cikin jarraba.”—Mat. 26:41a.
2 Amma almajiran Yesu ba su yi tsaro kamar yadda Yesu ya gaya musu ba. Shi ya sa da aka zo kama Yesu, abin ya zo musu ba zato, kuma dukansu suka gudu suka bar shi. Abin da a baya sun ce ba za su taɓa yi ba.—Mat. 26:56.
Yesu ya gargaɗi almajiransa cewa su yi tsaro don kada su faɗi cikin jarraba, amma daga baya sun gudu sun bar shi (Ka duba sakin layi na 1-2)
3. (a) Me ya sa bai kamata mu buga ƙirji cewa ba za mu yi zunubi ba? (b) Me za mu tattauna a talifin nan?
3 Mu ma kada mu buga ƙirji cewa ba za mu yi zunubi ba. A gaskiya, ba ma so mu yi abin da zai ɓata ma Jehobah rai. Amma mu ma ajizai ne, kuma zai iya yi mana sauƙi mu faɗi cikin jarraba. (Rom. 5:12; 7:21-23) Ba zato, za mu iya samun kanmu a cikin yanayin da zai sa mu yi shaꞌawar yin abin da bai dace ba. Don haka, abin da zai taimaka mana mu riƙe amincinmu ga Jehobah da kuma Ɗansa, shi ne mu bi gargaɗin Yesu cewa mu yi tsaro don kar mu faɗi cikin jarraba. Abin da za mu tattauna a wannan talifin zai taimaka mana mu yi hakan. Da farko, za mu tattauna abubuwan da ya kamata mu fi yin hankali da su. Saꞌan nan za mu tattauna yadda za mu kiyaye kanmu daga yin zunubi. A ƙarshe, za mu tattauna yadda za mu ci-gaba da yin tsaro.
KA SAN INDA KAKE DA KASAWA
4-5. Ko da yake wasu zunubai ba su kai wasu tsanani ba, me ya sa yin su yake da haɗari sosai?
4 Akwai zunubai da ba su kai wasu tsanani ba, amma su ma za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Kuma za su iya kai mu ga yin zunubi mai tsanani.
5 Dukanmu muna fuskantar jarrabar yin abin da bai dace ba. Amma kowannenmu yana da abin da ke saurin sa shi ya yi zunubi. Alal misali, wani kasawarsa ita ce jarrabar yin lalata. Wani kuma yana fama da jarrabar yin abubuwa masu ƙazanta, kamar yin wasa da alꞌaura ko kuma kallon batsa. Ƙari ga haka, wasu suna fama da tsoron mutum, ko son yin abubuwa yadda suka ga dama, ko saurin fushi, da dai sauran su. Shi ya sa Yakub ya ce, “Kowane mutum dai yakan sami jarraba saꞌad da mugun kwaɗayinsa ya ruɗe shi, ya kuma sha kansa.”—Yak. 1:14.
6. Me ya kamata mu tuna game da kanmu?
6 Ka san inda kake da kasawa? Idan mun san kasawarmu kuma muka yi watsi da ita domin muna ganin ba za mu yi zunubi ba, ruɗin kanmu muke yi. (1 Yoh. 1:8) Ka tuna cewa Bulus ya ce ko waɗanda “Ruhu Mai Tsarki yake tare da” su ma, wato waɗanda suka manyanta, za su iya faɗi cikin jarraba idan ba su yi tsaro ba. (Gal. 6:1) Don haka, dole ne mu gaya wa kanmu gaskiya ta wajen tuna da inda muke da kasawa.—2 Kor. 13:5.
7. A kan me ya kamata mu fi mai da hankali? Ka ba da misali.
7 Idan mun gano wuraren da muke da kasawa, me ya kamata mu yi? Mu yi iya ƙoƙarinmu mu shawo kansu! Alal misali, a zamanin dā, ta ƙofar birni ne maƙiya suke saurin shiga su yi ɓarna. Shi ya sa ake saka masu gadi da yawa a ƙofar. Mu ma ya kamata mu fi mai da hankali ga inda muka san muna da kasawa, don kada mu faɗi cikin jarraba.—1 Kor. 9:27.
YADDA ZA KA KIYAYE KANKA DAGA YIN ZUNUBI
8-9. Waɗanne kurakurai ne matashin da aka ambata a Karin Magana sura 7 ya yi da suka kai shi ga yin zunubi? (Karin Magana 7:8, 9, 13, 14, 21)
8 Ta yaya za mu kiyaye kanmu? Za mu iya yin hakan idan muka yi laꞌakari da abin da ya faru da matashin da aka ambata a Karin Magana sura 7. Matashin ya yi lalata da wata mace mai zina. Aya 22 ta gaya mana cewa “ba labari sai ya bi ta.” Amma idan muka dubi ayoyin da suke kafin aya ta 22, za mu ga cewa akwai kurakurai da ya yi da suka kai shi ga yin wannan zunubi.
9 Waɗanne kurakurai ne ya yi? Na ɗaya, da yamma ne ya bi titin da ke “kusa da inda [mace mai zinan] take zama.” Saꞌan nan ya bi hanyar zuwa gidanta. (Karanta Karin Magana 7:8, 9.) Na biyu, da ya ga matar, bai kauce ba. A maimakon haka, ya amince ta yi masa sumba, kuma ya saurari bayaninta a kan yadda ta miƙa hadayu na gyaran zumunci. Da alama ta faɗi hakan ne don ta sa ya ɗauka cewa ita macen kirki ce. (Karanta Karin Magana 7:13, 14, 21.) Da a ce matashin bai yi abubuwan nan ba, da bai fuskanci jarrabar nan ba, kuma da bai yi zunubin ba.
10. Kamar matashin, waɗanne abubuwa ne za su iya kai mutum ga yin zunubi a yau?
10 Wannan labarin ya nuna abin da zai iya faruwa da kowannenmu. Mutum zai iya yin zunubi mai tsanani kuma ya ɗauka cewa abin ya faru ne “ba labari,” wato bai yi zaton cewa hakan zai faru ba. Amma idan ya yi tunani da kyau, zai ga cewa akwai wasu kurakurai da ya yi da suka kai shi ga yin wannan zunubi. Wataƙila ya soma bin abokan banza, ko yana yin nishaɗi marar kyau, ko ya je inda bai dace Kirista ya je ba, ko ya shiga dandalin intane marar kyau. Wataƙila ma ya daina karanta Littafi Mai Tsarki, da yin adduꞌa, da yin waꞌazi. Kamar matashin nan a littafin Karin Magana, kurakurai da ya yi ne suka kai shi ga yin wannan zunubi.
11. Me za mu guje ma idan ba ma so mu yi zunubi?
11 Mene ne darasin? Muna bukatar mu guji yin zunubi, amma kuma, yana da muhimmanci mu guji abubuwan da za su iya kai mu ga yin zunubi. Bayani da Sulemanu ya yi ke nan bayan da ya ba da labarin saurayin. Game da matar, Sulemanu ya ce: “Kada ku bi hanyoyinta.” (K. Mag. 7:25) Ya kuma ce: “Yi nesa da hanyarta, kada ma ka yi kusa da ƙofar gidanta.” (K. Mag. 5:3, 8) Hakika, idan muna so mu kiyaye kanmu daga yin zunubi, dole mu yi nesa da abubuwa da kuma wurare da za su kai mu ga yin zunubi.b Wannan yana nufin cewa ko da yin wani abu ba laifi ba ne, idan mun san cewa zai sa mu cikin jarraba, kar mu yi shi.—Mat. 5:29, 30.
12. Wane ƙuduri ne Ayuba ya yi, kuma ta yaya hakan ya taimaka masa? (Ayuba 31:1)
12 Idan muna so mu kauce ma yanayoyi da za su iya kai mu ga yin zunubi, dole mu tsaya kafa biyu. Abin da Ayuba ya yi ke nan. Ya ‘yi yarjejeniya da idanunsa’ cewa ba zai kalli budurwa har ya yi shaꞌawar ta ba. (Karanta Ayuba 31:1.) Ayuba ya tsaya kafa biyu a kan wannan ƙudurin nasa, kuma hakan ya sa ya kiyayi kansa daga yin lalata. Mu ma za mu amfana sosai idan muka ƙudura cewa za mu kiyayi duk wani abin da zai sa mu cikin jarraba.
13. Me ya sa muke bukatar mu yi hankali da abubuwan da muke tunanin su? (Ka kuma duba hotunan.)
13 Ƙari ga haka, dole mu yi hankali da abubuwan da muke tunanin su. (Fit. 20:17) Wasu suna ganin ba laifi ba ne idan suna tunani cewa suna yin wani abin da bai dace ba, tun da ba su yi shi a zahiri ba. Amma yin hakan laifi ne. Me ya sa? Domin irin wannan tunani zai ƙara wa mutum shaꞌawar yin zunubi. Kamar dai yana sa kansa cikin jarraba ne, kuma zai ƙara masa wuya ya shawo kan jarrabar. Wani lokaci tunani marar kyau zai zo zuciyarmu. Amma abin da zai taimaka mana shi ne, da zarar irin tunanin nan ya zo zuciyarmu, mu kau da shi kuma mu soma yin tunani a kan abubuwa masu kyau. Hakan zai kiyaye mu daga yin zunubi mai tsanani, domin ba mu bar tunani marar kyau ya tayar mana da muguwar shaꞌawa ba.—Filib. 4:8; Kol. 3:2; Yak. 1:13-15.
Ya kamata mu guji duk wani abin da zai iya sa mu cikin jarraba (Ka duba sakin layi na 13)
14. Mene ne kuma zai taimaka mana mu kauce ma duk wani abin da zai sa mu cikin jarraba?
14 Mene ne kuma zai taimaka mana mu kauce ma duk wani abin da zai sa mu cikin jarraba? Muna bukatar mu tabbatar ma kanmu cewa za mu amfana a duk lokacin da muka bi dokokin Jehobah. Yin tunani da kuma son yin abin da ya dace a kullum bai da sauƙi, amma idan muka yi ƙoƙari muka yi abin da ya dace, mu karan kanmu za mu ji daɗi.
15. Ta yaya zama masu ƙin mugunta da masu son abu mai kyau zai taimaka mana?
15 Yana da muhimmanci mu so yin abin da ya dace. Idan muka horar da kanmu muka zama masu ‘ƙin mugunta’ da masu ‘son abu mai kyau,’ zai yi mana sauƙi mu yi abin da ya dace kuma mu kauce ma abin da zai kai mu ga yin zunubi. (Amos 5:15) Ƙari ga haka, idan muna ƙin mugunta kuma muna son abu mai kyau, za mu samu ƙarfin guje ma jarraba idan ta zo mana ba zato.
16. Ta yaya yin ayyukan ibada zai taimaka mana mu yi tsaro? (Ka kuma duba hotunan.)
16 Ta yaya za mu horar da kanmu mu zama masu son abu mai kyau? Mu shagala wajen yin ayyukan ibada. Idan muna a taro ko muna waꞌazi, da wuya mu yi tunanin yin abu marar kyau. A maimako, ayyukan nan suna sa mu ƙara son yin abin da zai gamshi Jehobah. (Mat. 28:19, 20; Ibran. 10:24, 25) Ƙari ga haka, karanta Littafi Mai Tsarki, da nazarin sa, da kuma yin tunani a kan abin da muka koya, za su sa mu ƙara son yin abu mai kyau kuma mu ƙi abu marar kyau. (Yosh. 1:8; Zab. 1:2, 3; 119:97, 101) Ka tuna abin da Yesu ya gaya wa almajiransa, Ya ce: “Ku kuma yi adduꞌa domin kada ku faɗi cikin jarraba.” (Mat. 26:41) Idan muna yin adduꞌa ga Ubanmu na sama, zai taimaka mana, kuma za mu ƙara samun ƙarfin yin abin da yake so.—Yak. 4:8.
Yin ayyukan ibada babu fashi zai ba mu ƙarfin yin tsayayya da jarrabawa (Ka duba sakin layi na 16)c
KA CI-GABA DA YIN TSARO
17. Wace kasawa ce Bitrus ya yi ta fama da ita?
17 Zai iya yiwu mu shawo kan wasu kasawa da muke da su gabaki-ɗaya. Amma mai yiwuwa mu ci-gaba da yin fama da wasu kasawarmu. Abin da ya faru da manzo Bitrus ke nan. Tsoron mutum ya sa shi ya yi mūsun sanin Yesu sau uku. (Mat. 26:69-75) Saꞌad da Bitrus ya ba da shaida da ƙarfin zuciya a majalisar Yahudawa, mai yiwuwa mutane sun ɗauka cewa ya shawo kan tsoron mutum. (A. M. 5:27-29) Amma bayan wasu shekaru, Bitrus ya daina cin abinci da waɗanda ba Yahudawa ba, domin yana “tsoron waɗanda suke so a yi wa waɗanda ba Yahudawa ba kaciya.” (Gal. 2:11, 12) Tsoron nasa ya sake dawowa. Hakan ya nuna cewa bai shawo kan wannan kasawar gabaki-ɗaya ba.
18. Me ya sa ya kamata mu ci-gaba da yin lura da inda muke da kasawa?
18 Mu ma hakan zai iya faruwa da mu. Ta yaya? Wataƙila mu yi zaton cewa mun shawo kan wata kasawa, amma sai ta sake dawowa. Abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa ke nan, ya ce: “Na daina kallon batsa har na shekaru 10, kuma na ɗauka cewa na gama shawo kan wannan kasawa. Amma bayan haka, na shiga wasu yanayoyi da suka sa na yi shaꞌawar kallon batsa.” Godiya ga Allah, ɗanꞌuwanmu bai karaya ba. Ya ga cewa dole ya ci-gaba da yin iya ƙoƙarinsa kowace rana, don ya ƙi kallon batsa, kuma mai yiwuwa ya yi hakan har iya rayuwarsa. Da taimakon matarsa da kuma dattawa, ya ɗauki wasu ƙwararan matakai don ya ci-gaba da yaƙar wannan kasawar tasa.
19. Me za mu yi don kada wata kasawa da muke fama da ita ta shawo kanmu?
19 Me za mu yi don kada wata kasawa da muke fama da ita ta shawo kanmu? Mu bi shawarar da Yesu ya bayar cewa: “Ku yi tsaro.” Ko da kana ganin kamar ka shawo kan wata kasawa, ka ci-gaba da kiyaye duk wani abin da zai sa ka cikin jarraba. (1 Kor. 10:12) Ka ci-gaba da bin matakan da suka taimaka maka a baya. Karin Magana 28:14 ta ce: “Mai albarka ne shi wanda yake tsoron Yahweh kullum,” wato wanda yake yin tsaro a koyaushe.—2 Bit. 3:14.
AMFANIN YIN TSARO
20-21. (a) Ta yaya za mu amfana idan mun ci-gaba da yin tsaro don kada mu faɗi cikin jarraba? (b) Idan mun yi iya ƙoƙarinmu, mene ne Jehobah zai yi mana? (2 Korintiyawa 4:7)
20 Ba shakka za mu amfana sosai idan muka ci-gaba da yin tsaro. “Daɗin romon zunubi na ɗan lokaci” ba zai sa mu farin ciki kamar bin ƙaꞌidodin Jehobah ba. (Ibran. 11:25; Zab. 19:8) Me ya sa? Domin Jehobah ya halicce mu mu yi nufinsa ne. (Far. 1:27) Shi ya sa idan muka yi nufinsa, zuciyarmu ba za ta dame mu ba, kuma za mu samu damar yin rayuwa har abada.—1 Tim. 6:12; 2 Tim. 1:3; Yahu. 20, 21.
21 Gaskiya ne cewa, “jikin ba ƙarfi.” Amma hakan ba ya nufin cewa ba za mu yi nasara ba. Jehobah zai ba mu ƙarfin da muke bukata. (Karanta 2 Korintiyawa 4:7.) Ka lura cewa ayar ta ce zai ba mu “ikon da ya fi duka,” wato ikon da ya fi namu. Amma dole ne mu fara da yin amfani da namu iko mu yi tsayayya da jarrabawa. Idan muka yi haka kuma muka roƙi Jehobah ya taimaka mana, tabbas zai ji adduꞌarmu kuma zai ba mu ƙarin ƙarfin da muke bukata. (1 Kor. 10:13) Hakika da taimakon Jehobah, za mu iya yin tsaro don kada mu faɗi cikin jarraba.
WAƘA TA 47 Mu Riƙa Adduꞌa ga Jehobah Koyaushe
a MAꞌANAR WASU KALMOMI: “Ruhu” da aka ambata a Matiyu 26:41 yana nufin muraɗin zuciyarmu. “Jikin” kuma yana nufin ajizanci da yake sa mu tunani da yin abin da bai dace ba. Shi ya sa wani lokaci ko da muna so mu yi abin da ya dace, idan ba mu yi hankali ba, ajizancinmu zai sa mu yi abin da bai dace ba.
b Littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! darasi na 57, batu na 1-3, da talifin nan, “Ka Mai da Hankali ga Nan Gaba” da ke Hasumiyar Tsaro ta Nuwamba 2020, shafi na 27-29, sakin layi na 12-17, za su taimaka ma wanda ya yi zunubi mai tsanani.
c BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa yana karanta nassin yini da safe, yana karanta Littafi Mai Tsarki a lokacin hutunsa da rana, saꞌan nan ya je taron tsakiyar mako da yamma.