Za Ka Iya Yin Tsayayya da Jaraba!
“Ban shiga Intane da nufin kallon batsa ba. Amma sa’ad da na shiga, wani abu kamar saƙo ya ɓullo farat ɗaya, kuma na buɗe.”—In ji CODY.a
“Wata kyakkyawar yarinya a wurin aikinmu ta soma kwarkwasa da ni. Sai wata rana ta ce mu je don mu ‘wala’ a wani hotal. Na san ainihin abin da take nufi.”—In ji DYLAN.
JARABA abu ne mai ban sha’awa ga wasu mutane. Ga wasu kuma, jaraba ta zama musu kamar kashi a wuya da za su yi farin ciki sosai idan suka rabu da shi. Kai fa? Ya kamata ka faɗa wa jaraba ne ko kuwa ka guje mata?
Hakika ba kowace irin jaraba ce ke sa mutum cikin babbar matsala ba. Alal misali, satar kuli-kuli ba zai halaka ranka ba. Amma faɗa wa wasu jarabobi kamar yin fasiƙanci ko zina, wato lalata, zai iya jawo mummunan sakamako. Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu da cewa: “Wanda ya yi zina . . . mara-fahimi ne: Wanda ya aikata wannan ransa yake nema ya hallaka.”—Misalai 6:32, 33.
Idan aka jarabce ka ka yi lalata, wane mataki ne ya kamata ka ɗauka? Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan shawara: “Gama nufin Allah ke nan, tsarkakewarku, ku hanu daga fasikanci; kowanne daga cikinku shi san yadda za shi riƙe santali nasa [jikinsa] cikin tsarkakewa da daraja.” (1 Tasalonikawa 4:3, 4) Mene ne zai taimaka maka ka kasance da irin wannan ƙudurin? Ka yi la’akari da matakai uku da za su iya taimaka maka.
Mataki na 1: Ka Kiyaye Idanunka
Kallon batsa yana rura wutar sha’awar banza. Yesu ya nuna cewa akwai alaƙa tsakanin kallo da yin sha’awar abu, saboda haka ya gargaɗe mu da cewa: ‘Duk wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyarsa. Kuma idan idonka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar.’ (Matta 5:28, 29) Mene ne Yesu yake nufi a nan? Yana nufin cewa idan muna so mu guji faɗa wa jaraba, wajibi ne mu daina kallon abubuwa masu ta da sha’awar jima’i.
A ce idanunka sun yi karo da hasken wutar walda, me za ka yi nan da nan? Za ka ci gaba da kallon wutar ne? Hakika ba za ka yi hakan ba! Amma za ka kawar da idanunka nan da nan don ka kāre su. Hakazalika, idan ka tarar da batsa, ko a cikin littattafai ko a talabijin ko kuma a zahiri, zai dace ka kawar da idanunka nan da nan. Kada ka gurɓata zuciyarka da tunanin banza. Juan, wani mutum da a dā yake da jarabar kallon batsa ya ce: “A duk lokacin da na ga mace kyakkyawa, nakan ji kamar in riƙa kallonta. Saboda haka, ina kawar da idanuna daga wurin kuma in gaya wa kaina: ‘Ka yi addu’a ga Jehobah! Kana bukatar yin hakan yanzu!’ Bayan na yi addu’a, sai sha’awar ta bar ni.”—Matta 6:9, 13; 1 Korintiyawa 10:13.
Na biyu, ka yi la’akari da Ayuba, wannan mutum mai aminci da ya ce: “Na yi wa’adi da idanuna; yaya fa zan yi sha’awar budurwa?” (Ayuba 31:1) Me zai hana ka kasancewa da irin wannan ƙudurin?
Ka Gwada Wannan: Idan ka tarar da duk abin da zai iya tayar maka da sha’awa, ka kawar da idanunka nan da nan. Ka bi misalin wannan marubucin Littafi Mai Tsarki da ya yi addu’a cewa: ‘Ka kawar da idanuna daga duban abin banza.’—Zabura 119:37.
Mataki na 2: Ka Kiyaye Tunaninka
Dukanmu mukan yi fama da sha’awoyi da ba su dace ba domin mu ajizai ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kowane mutum yakan jarabtu, sa’anda sha’awarsa ta janye shi, ta yi masa tarko. Sa’annan, lokacin da sha’awa ta haɓaka, takan haifi zunubi.’ (Yaƙub 1:14, 15) Ta yaya za ka guji jefa kanka cikin irin wannan mummunan yanayi da zai yi maka wuya ka rabu da shi?
Idan ka fara sha’awar yin abin da bai dace ba, ka tuna cewa kana da zaɓi. Kada ka bar waɗannan sha’awoyi su sha kanka. Kada ka bar zuciyarka ta riƙa tunanin yin lalata. Wani mutum mai suna Troy, wanda ya faɗa cikin jarabar kallon batsa a Intane ya ce: “Na yi ƙoƙari sosai in kawar da mummunan tunani daga zuciyata. Bai kasance mini da sauƙi ba. Sau da yawa nakan koma ga yin wannan halin banza. Amma a hankali, na koyi kame kaina.” Wata mata kuma mai suna Elsa, wadda ta yi fama da sha’awar yin lalata a lokacin da take budurwa ta ce: “Yin addu’a ga Jehobah da kuma shagala a ayyukan ibada sun taimaka mini in daina tunanin banza.”
Ka Gwada Wannan: A duk lokacin da ka soma tunanin yin lalata, ka yi addu’a nan da nan. Ka kawar da tunanin banza daga zuciyarka ta wajen bin gargaɗin nan daga Littafi Mai Tsarki: “Iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adalci, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo ƙauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato; idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga waɗannan” abubuwan.—Filibiyawa 4:8.
Mataki na 3: Ka Kiyaye Sawunka
Idan tun dā can mutum yana sha’awar abin da bai dace ba, kuma aka jarabce shi, zai kasance da sauƙi ya faɗa cikin jarabar. (Misalai 7:6-23) Ta yaya za ka guji faɗawa cikin wannan yanayin?
Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan kyakkyawar shawara: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya: Amma wawaye sukan bi ciki, su sha wuya.” (Misalai 22:3) Saboda haka, ka kiyaye sawunka. Ka bincika don ka san irin yanayin da za su iya tayar maka da sha’awa kuma ka guje su. (Misalai 7:25) Wani mutum mai suna Filipe, wanda ya fita sha’anin kallon batsa ya ce: “Na ajiye kwamfuta da iyalina ke amfani da ita a inda kowa zai iya ganin mai amfani da shi, kuma na saka irin na’urar da za ta ba da gargaɗi idan mutum zai shiga dandali marar kyau a ciki. Kuma ba na shiga Intane idan babu mutane kusa.” Hakazalika, Troy, wanda aka ambata shi ɗazu ya ce: “Na daina kallon fina-finai masu ta da sha’awa ko kuma mutanen da suke maganar banza game da jima’i. Ba na so in jefa kaina cikin matsala.”
Ka Gwada Wannan: Ka yi ƙoƙari ka san kasawarka, kuma ka shirya yadda za ka guje wa duk wani yanayi da zai tayar maka da sha’awa.—Matta 6:13.
KADA KA FID DA RAI!
Amma idan ka faɗa cikin wata jaraba duk da ƙoƙarin da kake yi fa? Kada ka yi sanyin gwiwa har ka daina ƙoƙartawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-adalci yakan fāɗi sau bakwai, ya sake tashi kuma.” (Misalai 24:16) Hakika, Ubanmu wanda ke cikin sama yana ƙarfafa mu mu “tashi.” Za ka yarda ya taimake ka? Idan kana so ya taimake ka, to kada ka gaji da yi masa addu’a. Ka ƙarfafa bangaskiyarka ta wajen yin nazarin Kalmarsa. Ka kyautata ƙudurinka ta wajen halartan taron Kirista. Ka bar wannan alkawari da Allah ya yi ya ƙara maka ƙarfin gwiwa: ‘Zan ƙarfafa ka, zan taimake ka.’—Ishaya 41:10.
Cody, wanda aka ambata a farkon wannan talifin ya ce: “Bai kasance mini da sauƙi in wanke hannuna daga jarabar kallon batsa ba. Sau da yawa na riƙa komawa gidan jiya, amma da taimakon Allah, na yi nasara a ƙarshe.” Dylan kuma da aka ambata a farkon wannan talifin ya ce: “Da zai kasance mini da sauƙi in yi jima’i da abokiyar aikina. Amma na yi tsayin daka, kuma na gaya mata ‘Sam, ba zan yi ba!’ Ina jin daɗin kasancewa da lamiri mai kyau. Ban da haka ma, na san cewa Jehobah ya yi alfahari da ni.”
A duk lokacin da ka yi tsayyaya da jaraba, ka tabbata cewa Allah zai yi alfahari da kai!—Misalai 27:11.
a An canja sunayen da ke cikin wannan talifi.