Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb26 Maris pp. 4-5
  • 16-22 ga Maris

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 16-22 ga Maris
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2026
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2026
mwb26 Maris pp. 4-5

16-22 GA MARIS

ISHAYA 45-47

Waƙa ta 2 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. “Ni Ne Allah, Babu Wani Kamar Ni”

(minti 10)

Israꞌilawa da yawa da suke bauta a Babila suna barin birnin.

Babu wani kamar Jehobah (Ish 46:9; w20.06 5 sakin layi na 14)

Babu abin da zai hana Jehobah yin abin da yake so ya yi (Ish 46:​10, 11; cl 42 sakin layi na 14; it-E “Exiles Return From Babylon” sakin layi na 1)

Waɗanda suka dogara ga allolin ƙarya ko kuɗi ba za su yi farin ciki ba (Ish 46:​6, 7; w99 6/1 12 sakin layi na 18-19)

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Ish 46:10—Shin, Jehobah ya san cewa ‘tun daga farko’ Adamu da Hauwaꞌu za su yi masa rashin biyayya ne? (w11-E 1/1 14 sakin layi na 2-3)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Ish 45:​1-11 (th darasi na 5)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka bayyana wa mutumin da ba Kirista ba abin da Taron Tunawa da Mutuwar Yesu ya ƙunsa. (lmd darasi na 5 batu na 3)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Kwanan baya da ka ziyarci mutumin, ya karɓi gayyata na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kuma ya ce zai zo. (lmd darasi na 9 batu na 5)

6. Almajirtarwa

(minti 5) lff darasi na 19 gabatarwa da kuma batu na 1-3 (lmd darasi na 11 batu na 3)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 38

7. Jehobah Ne Kaɗai Zai Iya Taimaka Mana a Kullum

(minti 7) Tattaunawa.

Idan muna fama da matsaloli, Jehobah ne kaɗai zai iya taimaka mana.—Ibr 13:​5, 6.

Karanta Zabura 55:22. Sai ka tattauna misalan da aka ambata a gaba da masu sauraro.

Hotuna: ꞌYanꞌuwa maza da mata da suke fama da matsaloli. 1. Wani danꞌuwa da ya rasa aikinsa ya zauna yana bakin ciki. 2. Wasu jamiꞌan tsaro suna yi ma wani danꞌuwa da aka saka a kurkuku tambayoyi. 3. Wata ꞌyarꞌuwa tana yi wa maigidanta da aka kwantar a asibi adduꞌa. 4. Mata da miji suna bakin ciki bayan wani balaꞌi da auko musu.

A kowane yanayi, ka rubuta hanya ɗaya da za ka nuna cewa ka dogara ga Jehobah, da kuma wata hanya da yake taimaka mana.

  • Idan mun rasa aikinmu ko kuma yana mana wuya mu kula da iyalinmu

  • Idan gwamnati ta hana mu ayyukan ibada

  • Idan muna fama da ciwo mai tsanani

  • Idan balaꞌi ya auko mana ko kuma wani danginmu ya rasu

8. Ƙarin Bayani na Sashen Zane-Zane da Gine-Gine na 2026

(minti 8) Jawabi.

Ku kalli BIDIYON.

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

(minti 30) lfb darasi na 70-71

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 148 da Adduꞌa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba