Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb26 Maris pp. 6-7
  • 23-29 ga Maris

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 23-29 ga Maris
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2026
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2026
mwb26 Maris pp. 6-7

23-29 GA MARIS

ISHAYA 48-49

Waƙa ta 89 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Yadda Za Mu Amfana Daga Koyarwar Jehobah

(minti 10)

Jehobah yana koyar da bayinsa (Ish 48:17; it-E “Teacher, Teaching” sakin layi na 2)

Zai dace mu saurari Jehobah (Ish 48:18a; ijwbq talifi na 44 sakin layi na 2-3)

Hakan zai sa salamarmu ta kasance “kamar ruwan rafi,” adalcinmu kuma za ta yi ta “ɓullowa kamar raƙuman ruwan teku” (Ish 48:18b; lv 199 sakin layi na 8)

Wata ꞌyarꞌuwa tana tafiya a bakin teku saꞌad da rana take faduwa.

MAꞌANA: Kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “salama” tana iya nufin ƙoshin lafiya da kariya da natsuwa da abokantaka da dai sauransu.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Ish 49:8—A waɗanne hanyoyi uku ne annabcin nan ya cika? (it-E “Acceptable Time” sakin layi na 1-3)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Ish 48:​9-20 (th darasi na 11)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci wani danginka da ya daina zuwa taro ko fita waꞌazi zuwa jawabi na musamman da kuma Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 5 batu na 3)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka bayyana ma wani da ya ce zai zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu abin da zai faru a taron. (lmd darasi na 9 batu na 3)

6. Komawa Ziyara

(minti 5) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Bayan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, ka amsa tambayoyin wani da ya halarci taron. (lmd darasi na 8 batu na 3)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 107

7. Yadda Za Ka Amfana Daga Rana Mafi Muhimmanci a Shekara

(minti 15) Tattaunawa.

Idan muka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, hakan yana nuna cewa muna biyayya da umurnin Yesu kuma muna godiya don fansar da Allah ya yi mana tanadin sa. (Lu 22:19) Taron yana tuna mana cewa Jehobah da Ɗansa suna ƙaunar mu sosai. (Ga 2:20; 1Yo 4:​9, 10) Ta yaya za mu amfana daga tanadin nan da Jehobah ya yi mana? Ta yaya za mu taimaka ma waɗanda suke son saƙonmu su ma su amfana?

  • Ka shirya yadda za ka bi karatun Littafi Mai Tsarki na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu kowace rana

  • Ka yi tunani sosai a kan kyautar da aka yi mana na fansa da kuma yadda za mu yi rayuwar da za ta nuna cewa muna godiya

  • Ka sa ƙwazo a waꞌazi na musamman da za a yi, kuma ka gayyaci abokai da dangi da mutanen da ke yankinku su zo su ji jawabi na musamman, kuma su halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu

  • Da faraꞌa ka marabci baƙin da suka zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Mutanen da aka gayyata a lokacin da aka yi waꞌazi na musamman da mutanen da kai da kanka ka gayyata, za ka iya gaya musu su zauna da kai a taron

  • Ka zama a shirye don ka amsa tambayoyinsu

  • Ka zama a shirye don ka marabci waɗanda suka daina zuwa taro. Idan waɗanda a dā su Shaidun Jehobah ne sun zo taron, dattawa su mai da hankali musamman ga marabtar su

Wani hoto daga bidiyon: “Yesu Ya Zo Garin Neman Abin da Ya Bace” Don Ya Cece Shi. ꞌYanꞌuwa a Majamiꞌar Mulki a daren Tunawa da Mutuwar Yesu suna tattaunawa da juna.

Ku kalli BIDIYON “Yesu Ya Zo Garin Neman Abin da Ya Ɓace” Don Ya Cece Shi. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu marabci waɗanda sun daina zuwa taro ko fita waꞌazi idan sun zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

    Wani hoto daga bidiyon: “Yesu Ya Zo Garin Neman Abin da Ya Bace” Don Ya Cece Shi. Wata ꞌyarꞌuwa da ta daina zuwa taro ta halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kuma wata ꞌyarꞌuwa tana rungumarta.

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

(minti 30) lfb darasi na 72-73

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 134 da Adduꞌa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba