KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI
Yin Amfani da Misalai
Sa’ad da muka koma ziyara ko muke nazarin Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu taimaka wa masu sauraronmu su fahimci muhimman darussa. Idan muka yi amfani da kwatanci don mu bayyana muhimman darussa, hakan zai ratsa zuciyarsu kuma ya yi musu sauƙi su tuna da darussan.
Sa’ad da muke shirin komawa ziyara ko nazarin Littafi Mai Tsarki, mu zaɓi muhimman darussa da za mu yi kwatanci a kansu, ba kowane bayani ba. Sai mu zaɓi kwatanci mai sauƙi da mutane suka san da shi. (Mt 5:14-16; Mk 2:21; Lu 14:7-11) Ka yi la’akari da al’adar masu sauraronka da kuma abubuwan da suke yi na yau da kullum. (Lu 5:2-11; Yoh 4:7-15) Idan ka ga yadda ɗalibinka yake farin ciki don ya fahimci wani batu, kai ma za ka yi farin ciki sosai.
KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI —KU RIƘA AMFANI DA MISALAI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Me ya sa ɗalibai suke bukatar taimako don su fahimci ayoyin Littafi Mai Tsarki?
Ta yaya Anita ta kwatanta abin da ke Romawa 5:12?
Kwatanci mai kyau yana ratsa zuciya
Ta yaya kwatanci mai kyau zai iya shafan masu sauraronmu?
Me ya sa muke bukatar mu yi amfani da bidiyoyi da kuma abubuwan da ƙungiyar Jehobah ta tanada a wa’azi?