DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Kori Dukan Mazaunan Ƙasar”
Jehobah ya umurci bayinsa su kawar da duk wani abin da zai sa su yi zunubi da ke Ƙasar Alkawari (L.Ƙi 33:52; mwbr21.05-HA an ɗauko daga w10 8/1 23)
Jehobah zai albarkace su idan suka yi iya ƙoƙarinsu don su mallaki dukan ƙasar (L.Ƙi 33:53)
Isra’ilawa za su fuskanci matsaloli sosai idan ba su yi nasara a kan maƙiyansu ba (L.Ƙi 33:55, 56; w08 2/15 27 sakin layi na 5-6; mwbr21.05-HA an ɗauko daga it-1 404 sakin layi na 2)
Idan muna so mu faranta ran Jehobah, wajibi ne mu guji duk halayen da za su iya ɓata ibadarmu ko lalata dangantakarmu da Jehobah. (Yak 1:21) Jehobah yana ba mu ƙarfin guje wa abubuwan da za su sa mu yi zunubi da kuma halaye marasa kyau na mutanen duniya.