RAYUWAR KIRISTA
Za A Yi Kamfen na Musamman a Watan Nuwamba don A Yi Shelar Mulkin Allah
Yesu ya yi wa’azin ‘labari mai daɗi na Mulkin Allah.’ (Lu 4:43) Ya kuma gaya wa mutane su yi addu’a game da Mulkin. (Mt 6:9, 10) A watan Nuwamba, za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi shelar Mulkin Allah. (Mt 24:14) Ka tsara ayyukanka da kyau domin kai ma ka sami damar yin wannan kamfen. Masu hidimar majagaba na ɗan lokaci za su iya ba da sa’o’i 30 ko 50 a watan.
Idan zai yiwu, ka bayyana nassin da ya yi magana game da Mulkin Allah ga mutane da yawa a yankinku. Sa’ad da kake zaɓan nassin da za ka karanta, ka yi la’akari da addinin mutumin. Idan wani ya nuna cewa ya ji daɗin saƙonmu, ka ba shi Hasumiyar Tsaro ta 2 2020. Ka yi ƙoƙari ka koma wurinsa kuma ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗaya daga cikin littattafanmu. Jim kaɗan, Mulkin Allah zai hallaka mulkokin ’yan Adam da ke adawa da shi. (Da 2:44; 1Ko 15:24, 25) Bari dukanmu mu yi amfani da wannan damar don mu nuna cewa muna goyon bayan Jehobah da kuma Mulkinsa!
Mulkin Allah zai sa duniya ta zama Aljanna!