DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 29-30
Ba da Gudummawa ga Jehobah
30:11-16
Sa’ad da ake gina mazauni, Isra’ilawa masu kuɗi da talakawa sun sami damar yin gudummawa don su tallafa wa hidimar Jehobah. Ta yaya mu ma a yau za mu ba da gudummawa ga Jehobah? Wata hanya da za mu iya yin haka ita ce ta wajen ba da gudummawa don tallafa wa ginin Majami’un Mulki, da Majami’un Babban Taro, da ofisoshin fassara, da Bethel da kuma wasu ginin da ake yi don bautar Jehobah.
Mene ne waɗannan nassosin suka koya mana game da ba da gudummawa don tallafa wa bautar Jehobah?
1Tar 29:5