Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Satumba p. 7
  • Za Ka Iya Ba da Lokacinka da Kuma Karfinka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Ba da Lokacinka da Kuma Karfinka?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Taimaka a Aikin Gine-ginenmu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Gine-gine da Aka Kammala Kafin Bullowar Koronabairas
    Yadda Ake Amfani da Gudummawarka
  • Aikin Gini da Ke Ɗaukaka Jehobah
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Satumba p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Za Ka Iya Ba da Lokacinka da Kuma Ƙarfinka?

Wani dan’uwa yana murmushi sa’ad da yake yanka karfe a wani aikin gini.

Kamar yadda annabi Ishaya ya annabta, muna ganin yadda ƙungiyar Jehobah take samun ci gaba sosai. (Ish 54:2) Hakan ya sa ana gina sababbin Majami’un Mulki da Majami’un Babban Taro da kuma wasu ofisoshinmu. Bayan an gama ginin, waɗannan wuraren suna bukatar a riƙa kula da su, wasu ma suna bukatar gyara sosai bayan wani lokaci. Ta yaya za mu ba da lokacinmu da kuma ƙarfinmu don mu taimaka a yin waɗannan ayyukan?

  • Za mu iya zuwa mu share Majami’ar Mulki idan rukuninmu ne da shara

  • Za mu iya amincewa a horar da mu a kan yadda za mu riƙa kula da Majami’ar Mulkinmu

  • Za mu iya cika fom ɗin nan Local Design/Construction Volunteer Application (DC-50) don mu taimaka da aikin gine-gine da gyare-gyare a yankinmu

  • Za mu iya cika fom ɗin nan Application for Volunteer Program (A-19) don mu taimaka da aikin gini da ake yi a ofishinmu ko a wata ƙasa na sati ɗaya ko fiye da hakan

KU KALLI BIDIYON NAN ANA SHIRIN WANI GAGARUMIN AIKIN GINI​—TAƘAITAWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Tun daga 2014, ta yaya muke amfani da bidiyoyi fiye da dā?

  • Don a iya ci gaba da wallafa bidiyo, wane shirin gini ne ake yi kuma zai ɗauki tsawon wane lokaci?

  • Ta yaya ’yan’uwa za su taimaka a wannan aikin?

  • Idan muna so mu taimaka a aikin ginin da za a yi a Ramapo, me ya sa zai dace mu cika fom (DC-50) kuma mu taimaka da aikin gine-gine da ake yi a yankinmu?

  • Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana goyan bayan wannan aikin?

  • Ta yaya za mu taimaka idan ba za mu iya zuwa aikin ginin ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba