DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 21-22
Ka Daraja Rai Kamar Yadda Jehobah Yake Yi
21:20, 22, 23, 28, 29
Jehobah yana ɗaukan rai da daraja sosai. Ta yaya za mu nuna cewa mu ma muna ɗaukan rai da daraja?
Ka ƙaunaci mutane sosai kuma ka daraja su.—Mt 22:39; 1Yo 3:15
Ka nuna kana ƙaunar mutane ta wajen yin wa’azi da ƙwazo.—1Ko 9:22, 23; 2Bi 3:9
Ka guji abin da zai sa ranka da na wasu cikin haɗari.—K. Ma 22:3
Ta yaya daraja rai yake sa mu guji ɗaukan alhakin jini?