Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Oktoba p. 5
  • Yin Ladabi da Biyayya Yakan Rinjayi Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Ladabi da Biyayya Yakan Rinjayi Mutane
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka Daraja Matarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Kada Ku Ci Amanar Juna
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Yadda Za Ku Zauna Lafiya da Danginku
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Oktoba p. 5

RAYUWAR KIRISTA

Yin Ladabi da Biyayya Yakan Rinjayi Mutane

Mata masu bi, sukan rinjayi mazajensu su soma bauta ma Jehobah ta wurin halayensu masu kyau. Amma mace za ta iya yin shekaru da yawa tana jimrewa kafin ta iya yin hakan. (1Bi 2:​21-23; 3:​1, 2) Idan maigidanki yana wulaƙanta ki, ki ci gaba da jimrewa don ki iya rinjayi mugunta da nagarta. (Ro 12:21) Mai yiwuwa maigidanki ba zai saurari wa’azin da kike masa ba, amma idan ya lura da halinki mai kyau, hakan zai iya rinjaye shi ya soma bauta ma Jehobah.

Ki yi iya ƙoƙarinki don ki fahimci maigidanki. (Fib 2:​3, 4) Ki zama mai tausayi kuma ki yi ƙoƙari ki cika duk hakkinki na matan aure. Ki riƙa sauraran sa da kyau. (Yak 1:19) Ki riƙa haƙuri kuma ki tabbatar wa maigidanki cewa kina ƙaunarsa. Ko da maigidanki ba ya daraja ki kamar yadda kike masa, ki tabbata cewa Jehobah yana farin ciki domin amincinki.​—1Bi 2:​19, 20.

KU KALLI BIDIYON NAN JEHOBAH YANA ƘARFAFA MU DON MU JURE WAHALA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Yaya rayuwa ta kasance wa Grace Li jim kaɗan bayan ta yi aure?

  • Me ya sa ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki?

  • Ta yaya ’yar’uwa Li ta jimre da matsaloli bayan ta yi baftisma?

  • Wace addu’a ce ’yar’uwa Li ta yi a madadin maigidanta?

  • Wace albarka ’Yar’uwa Li ta samu domin ta yi ladabi da biyayya?

Wata ’yar’uwa tana nazari da Grace Li; Grace tana kuka a waje; Grace da yaranta sun bar shagonsu na dafa abinci don su je taro; Grace da iyalinta.

Ladabi da biyayya suna da muhimmanci sosai!

Yin ladabi da biyayya zai iya taimaka miki idan mijinki ya yi baftisma, amma ba ya taimaka ma iyalinsa su bauta ma Jehobah. Ku kalli bidiyon nan Ki Ƙarfafa Mijinki Ta “Hali Mai Kyau.”

Wata ’yar’uwa tana kallon mijinta da ya daina zuwa taro da kuma fita wa’azi
    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba