DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 1 BITRUS 3-5
“Ƙarshen Dukan Abu Ya Yi Kusa”
Jim kaɗan, za a soma ƙunci mai girma wanda ba a taɓa fuskanta ba a tarihin ’yan Adam. Ta yaya za mu ci gaba da kasancewa da aminci a yanzu da kuma nan gaba?
Mu yi addu’a ba fasawa tare da yabo da godiya da kuma roƙo
Mu nuna ma ’yan’uwanmu ƙauna sosai kuma mu yi kusa da su
Mu riƙa yin alheri
KA TAMBAYI KANKA, ‘A waɗanne hanyoyi ne zan iya nuna ƙauna ga ’yan’uwa a ikilisiyarmu da kuma waɗanda suke ko’ina a faɗin duniya?’