Shaidu suna marabtar wani da ya zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu
Yadda Za Mu Yi Wa’azi
●○○ HAƊUWA TA FARI
○●○ KOMAWA ZIYARA TA FARKO
Tambaya: Me ya sa Yesu ya mutu?
Nassi: Mt 20:28
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Ta yaya za mu nuna godiya don fansar Yesu Kristi?
○○● KOMAWA ZIYARA TA BIYU
Tambaya: Ta yaya za mu nuna godiya don fansar Yesu Kristi?
Nassi: Yoh 17:3
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Me ake yi a Majami’ar Shaidun Jehobah?
RARRABA TAKARDAR GAYYATA NA TARON TUNAWA DA MUTUWAR YESU (23 ga Maris–19 ga Afrilu):
Muna gayyatar ka zuwa wani taro na musamman. Ga naka takardar gayyatar. Miliyoyin mutane a faɗin duniya za su taru a ranar Jumma’a, 19 ga Afrilu don su Tuna da Mutuwar Yesu. An rubuta lokaci da kuma wurin da za a yi taron a wannan yankin a cikin takardar. Muna kuma gayyatar ka ka zo ka saurari wani jawabi mai jigo “Ku Ƙoƙarta Don Ku Sami Rai Na Har Abada!” Za a ba da jawabin kafin makon da za a yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu.
Tambayar da Za Ka Yi Idan Mutumin Ya So Wa’azin: Me ya sa Yesu ya mutu?