DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYYUKAN MANZANNI 25-26
Bulus Ya Ɗaukaka Ƙara Zuwa Gaban Kaisar Kuma Ya Yi ma Sarki Agiriffa Wa’azi
Ko da yake bai kamata mu damu ainun game da abin da za mu faɗa sa’ad da aka kai mu “gaban shugabanni da sarakuna” ba, zai dace mu “zauna a shirye kullum mu bayyana” wa mutane abubuwan da muka yi imani da su. (Mt 10:18-20; 1Bi 3:15) Idan magabta suka kafa “dokokin ƙeta,” ta yaya za mu bi misalin Bulus?—Za 94:20.
Muna amfani da ’yancinmu don mu kāre wa’azin da muke yi.—A. M 25:11
Mukan yi wa mahukunta magana da ladabi.—A. M 26:2, 3
Idan zai yiwu, muna bayyana wa mutane yadda imaninmu yake taimaka mana da kuma wasu.—A. M 26:11-20